← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 55

Sashe 40

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a) mutunci, da sauransu. "Don baka ku dauki auren da aka muku a matsayin taku kaddarar wadda muke fatan kasancewar sa mafificin alkhairi agare ku da mu baki daya. Dukkanin ku had'a ku aure akayi. Ba ganin juna kukayi ba kukace kunaso. Marigayi sudeis Allah ya masa rahama shine usuli mai neman auren Zaraah . Amman dake Allah yafi mu kaunar sa ya kuma san dalilin haka yasa daurin auren ya koma kan na Ikko . Astagfirullah. Allah ya karawa annabi daraja. Sudeis ya zama tamkar shine wanda yayi me zance ne? "Kamar foundation na gini." Capt ya bata amsa Yana mai matse hawayen dake gangara a fuskar sa. "Yauwa ya zama tamkar shine tsani wajen bayar da na Ikko sama. Sudeis ya zama tamkar shine tsani wanda Ms Ikko zai taka a gaba. Sudeis tamkar shimfida yayi . Na Ikko kuma zai maye kan gurbin shimfidar. Tun ran gini tun ran zane. Abunda Allah ya rubuta da alkalamin qudra ba makawa sai ya afku. Haka zalika nj dinnan shaida ce. Sudeis ya fadamin yafi sau ba adadi. Tjn ina ganin tamkar shirme. Har abun ya fara tsayamun arai "Ranar da zan koma gidah. Na shigaa mota. Dan albarka yace da ni. Addayo Allah ya kaiki lapia ya dawo mana da ke lapia. Nace aamin. Yace saura yan watanni na tafi halartar muhawaran nan. Dan Allah Addayo ki dinga tsausarar zuciyar Babban Yaya akan tsanar da yayiwa Zaraah na. Tayi yawa. Gashi kuma shi kadai na fi yadda na baiwa amanar Zaraah na. Addayo ko bayan rai na ni dai idan har bansamu auren Zaraah ba. Dan Allah Addayo ku aurawa Zaraah Babban yaya. Matsalar Zaraah daya tanada ZUCIYA. Abu daya babban Yaya zai rike ya ssamu kaunar Zaraah da mallakin Zaraah bakj daya. Nace menene sudeis wane abu ne ? Baka gajiya da shiririta Kai dai. Yi sauri karka batamana lokaci.. Ya dube ni kafin ya saki murmushi mai taushi. Yace SO kadai ya isa. Idan ya rike SO to tabbas ya gama da ZUCIYAr Zaraah na. Domin SO DA ZUCIYA abune guda daya Addayo. Daga ZUCIYA aka samo SO. Daga SO ake mallakar ZUCIYA baki daya. Da yardar Allah Addayo SO DA ZUCIYAr Zaraah da Maheer zai bada kala. A turance zan iya kiransa da... Bazan iya fadan kalamen da yake yawan fada ba don da turanci ne. Amman har agaban Na Ikko ma ya ambata da yawan gaske." "A LOVE SOO BEAUTIFUL!!! " Maheer ya fada ahankali yana goge hawayen dake zuba a fuskar. Wanda gaba daya Yan parlorn shi suke yi "Zahiri haka yake cewa. Daga karshe yace Addayo inaji ajiki na Zaraah kamar mallakin babban Yaya zata zama. Nace masa ni rabu da ni ba wanda yasan gaibu. Yace nima ba wai na sani bane. Kawai dai sunfi dacewa da juna Allah kuwa. Ni zan samu wata kyakkyawa awani wurin. Ina fatan aljanna ce ma da yardar Allah. Na Zama daya daga cikin samarin aljannah. Yana kai karshe nasa yatsa na dungure masa kai. Hade da rufe murfin motar mukayi gaba. Sai bayan rasuwar sa kalaman sa suka shigaa zagayemun kwakwalwata. Shysa ko da wannan yaron yayi mun magana ya nemi shawarata nace na amince. Domin wasiyyar sudeis ce. Ya kamata acika masa ita "Amman babu dole Zaraah. Bazamu sbiga hakkin ki ba. A yau dinnan. Kai a yanzu ma da yardar Allah Zan sa na Ikko ya rubuta miki takarda ya sawwake miki.. Allah Kuma ya dubi maraicin sudeis da mukayi baki daya ya baki wanj mijin Wanda zai kaunace ki har karshen rayuwar sa. Kai na Ikko dakko takarda da biro. " "Wayyo Allah na. Dadaa, Addayo, Bappah ku gafarce ni. Wallahi na amince. Na yadda na Kuma hakura zan zauna da igiyar auren Ya Maheer. Saboda na cikawa Yaya sudeis burin sa. Na kuma bi umarnin da kuka Yi akai na. Allah ya yafe mana baki daya Amman na yadda na kuma amince zan cika burin Yaya sudies na SO DA ZUCIYAr da yake muradin son haduwar wajen zama abu daya. Dan Allah ku gafarce ni. Allah na yarda zan zauna da Ya Maheer din......." Albarka! Albagka! Godia! Nasiha! Kyauta! Addu'oi babu wanda Zaraah da Maheer basu shaba a ranar daga bakunan Dadaa, Addayo da captain Muhammad Muhammad .. Duk kuwa da zuciyoyin su Zaraah da Maheer basu aminta da juna ba. Haka aka karashe zaman ranar cikin farin ciki da zuba ruwan addu'oi ga marigayi sudeis ibn Harith . 'Da na biyu ga captain Muhammad muhammad . Kuma 'kani ga Doctor Maheer Muhammad Muhammad. A watan da aka saka tariyar Zaraah da Maheer a watanne Maheer tafiyar gaggawa ta same shi zuwa ga kasar saudiyyah. Sai halacci wani taro amadadin marigayi sudeis. Zaraah amarya an kare makarantar sakanni in dire tayi jamb taci postutme. Kai har ta samu gurbin karatu a jami'ar bayero university dake Kano. Inda zata karanci fannin common and Islamic law,, Duk wani gyara da akewa amarya Kama daga magungunan sanyi zuwa na jiki da sauran su anyiwa Zaraah shi. Kai harda Maheer dinma Addayo ta kasa ta tsare Yana shan maganin sanyin shima . sauketa a islamiyya da dakkota ..Kai harda zuwa unguwa. Duk Maheer ya daukewa Zaraah . Baya gajia da yi. Zasu gaysa a mutince. Idan zata unguwa dole saita tambaye shi. Wata rana ya amince. Wataran ya dage gira wajen cewa: Ba inda zaki je Toh a haka dai. Har Allah ya kawo ranar dasu Zaraah suka fara lectures. Mudikalle shi ne direban dake kai Zaraah makaranta ya dakkota. Domin Maheer yayi tafiya. Gyaran gidan da zasu tare ma yanata tafiya. FACULTY OF LAW (BAYERO UNIVERSITY KANO) Sati uku kenan da fara lectures din su Zaraah. Malam M2 (M sqaure) Da yan facultyn ke dokin ganin sa tun day 1. Ba shi ba alamar sa .Har anci sati 3. Zaraah suna class itada su Najwa suna jiran gawon Shanu. Saboda har yau ba alamar zuwan sabon malamin Mai suna M sqaure (M2) har a time table ga sunan sa nan. Bai taba attending lectures Kwatsam Yan ajin na zaune wasu na tsaye anata hira. Malamin ya shigaa sanye cikin blazer baka. Da pcap. So enticing "Settle down pls . Head of the class close the doors pls. Silence. Everyone Tear a sheet of paper. Write your reg number and today's date. Then pass the paperz accordingly to the person sitting next to you ... " XOXOWRITES 2/12/22, 11:37 - Buhainat: SDZ NANA HAFSATU Cikin daddad r muryar sa mai kwantar da hankula da nutsuwa . Wanda ya shaki ilimin arabi ya surka da boko. Gwanin ban sha'awa a duk sanda ya bude baki yayi magana. A hankali kuma a nutse cikin lankwasar da muryar sa. Ya sake maimata musu cikin harshen hausa. u zazzauna dan Allah, Shugaban aji tashi ka rufe kofofin ajin nan. Ayi shiru dan Allah. Kowa ya yago paper ya rubuta lambar rijistarsa da kwanan watan yau. Sai Kowanne bayan ya rubuta a jere ka mikawa wanda yake kusa da kai.. ... ? ya fada Cikin harshen larabc". Rassurez-vous svp. Chef de classe fermez les portes svp. Silence. Tout le monde D chirez une feuille de papier. crivez votre num ro d'enregistrement et la date d'aujourd'hui. Passez ensuite le papier en cons quence la personne assise de vous.. Ya sake fada cikin harshen faransan ci. Zaraah dake zaune kan kujera. Gefenta kuma Adamancy ce course mate dinta. Dukkanin yan ajin sunyi tsit suna sauraron sa. Yan matan ajin gaba daya hankulan su kacokam sun daura akan malam M2. Ya yinda Zaraah ke mamakin yanayin muryar sa data ke da tabbacin tayi kama daya data Maheer. Bataji ko taga labarin zai koyar a jami'a . Dan zahiri datace Maheer dinne. Sai kalle shi take daga kafa zuwa wajen fuskar sa. "Kawata ba dai kin fola ba?" Zaraah tajiyo muryar Adamancy na tsokanar kawar su Zubee. "Yo ba dole na fola ba. Dan gayu mai zazzakar murya mai kwantar da hankali. " Zubee ta fada. Zaraah ta girgiza musu kai kawai tana dariya. Sai da Maheer ya kammala karbar attendance din da class captain ya bashi. Tukun sannan ya daga kansa sama hade da gyara mic din dake maqale a aljihun sa. Ya fara basu hakuri abisa rashin zuwan sa lectures . Sai Kuma ya shiga bayyana musu sunan sa . Da course din da zai koyar da su. "Suna na Dr. Maheer Muhammad Muhammad. Wanda a makaranta kuma nan dama sauran wajajen karatu da nayi. Amfi mun laqabin kira da. M2 wato M square . Square din na nufin surname dina Muhammad, other name kuma Muhammad. Sai first M din ta name na nufin Maheer. So zaku iya ko cigaba da kirana M square din, "Ina da rules and regulations. Doka da ka'idodi. Idan na shigo class ba wanda zai shigo. Bawanda zai fita sai da uzuri. Attendance is compulsory. Kuma individual attendance ne ba general ba. Attendance dinmu 30 marks ne. Open test 10 marks . Sai exams. Oh yes. Presentations zai zama in groups . 5 marks. Then sauran marks din sune na exams. Banda intention din fadar da kowa a exams. Fyace wanda ya karya wannan dokokin. "Maza zasu koma zama a left row, Mata a right. Banda surutu. Abide my rules . Khalas mafi mushkila. Duk wanda yabi dokokin dana fada. In shaa Allah da A zai fita a exams. As for weeks din da banzo ba. Na bawa kowa 10 marks. Insha Allah briefly yanzu zan fara muku bayanun course outlines din. Zamuyi discussing 3 topics yanzu..duk wanda bai gane ba. Zai iya tambayar inda yake son karin haske. Ni kai na zan iya nuna mutum ince ya tashi ya ban amsan kasa. An gane?" "Yes sir! " Yan ajin su ka kurma murya wajen amsa shi. Banda Zaraah da ke mamakin ganin sa. Ashe dai shidinne? Kuma a matsayin malamin su na boko? Bayan shugabantar da su da yake a islamiyya. ? Wani hawayen takaici ya zuraro mata. Don tasan ba makawa sai ya sake takura mata. Don ta lura da gayya yake abubuwan sa yanzu. Wayar tace tayi 'karar shigowar sak'o. Number kuma bakuwar number ce. "Dago ki kalle ni. KO na shelanta musu ke matata ce. Wanda aka hadamu aure bama son juna. Idan
Chapter 40 · 0% Book details