← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 55

Sashe 47

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

choge. "Menace miki acikin mutane uhm? Zaraah. Kiyi magana ," Yana magana yana jagaba kusa da ita. Zaraah ta kasa cewa komai saboda yadda kwarjinin sa ya dabaibaye ta baki daya. "Matsoraciya" ya fada Yana lakuce mata hanci. Shigewa mota yayi . Yayinda Zaraah ta koma ciki wajen dije. Data bararraje tana dama kwalba a kofi. "Har kin dawo?" "Eh... Ranki ya.." "Amin amma karki karasa dan Allah. Naface ki dauke ni amatsayin yayarki. Kuma aminiya tunda mazanmu ma aminai ne. Kinganni nan ni bakina baya shiru, kiyi hakuri " "Haba sis ki dena cewa haka" cewar Zaraah a kunyace. "Wallahi kuwa. Ci abincin dan Allah. Ni kwalba zan sha. Ku yan gayu bakwa sha." "Nima ba yar gayu bace sis." "Ah yar gayu ce . Ni kuwa cikakkiyar yar kauye nake. Kauyen durbun . Haihuwa da tashin kauye. " "Nima haka." "Aa wallahi. Kede CI abincin dan Allah. Alhamdulillah yara basanan bare su hanaki ci da hira. " "Inason yara wallahi. Suna ina?" "Sunje gidan kawu na. Gaba daya na tattara na kai su . Dama babansu bayanan . So nake na wargaje na huta ni daya" Zaraah me zatayi ba daria ba. Tashiga dariya sosai "Yauwa ko kefa? Saki jikin ki sosai agida kike. " Haka dai Zaraah da Dije sukayi ta yar hirarsu. Bayan Zaraah tagama cin abincin. Dije ta rakata dakinta tayi alwala sukayi sallah. Sannan suka haye kan kujerun dakin suna cigaba da hira. "Maheer yace kina bashi tough time. Yar kanwata meyasa? KO har yanzu marigayi sudeis yana cikin ranki. Nasan yana nan. Hakuri zakiyi Zaraah ki cigaba da masa addua. Kisa aranki taki kaddarar kenan. Kuma kin karba da hannu biyu. "Meye laifin Maheer? Hes nice, attentive , and most caring. What more could you want in a man than Maheer ? Allah ne ya kaddara Maheer shine mijin ki ba sudeis ba. Sudeis dai yayi sharar fagene kawai. Allah yayi ba mai zama bane a duniyar . Da Maheer da Sudeis duk abu daya ne Zaraah. Shin Zaraah gaba daya meye ma auren uhm? Barin gaya miki ko ni maimartaba bashi nakeso yake so na ba. Ke nida saurayi na na baya har yaran da zamu haife mun samu suna Zaraah ahaukanmu. Nan duniya a lokacin bakiga yadda muke kaunar juna ba. Bantaba kawo wa a duniya bashi zan aura ba.." "Shima rasuwa yayi?" "A'ah! Ai da rasuwar yayi ma da dan sassauci. Yana raye ingaya Miki. Tawa kaddarar kenan daga zuwa taron sauka kinsan ni yar jarida ce abaya. To anan dai Allah ya kaddara mai martaba zai ganni. Haka banda masaniya aka daura mun aure dashi Ashe wai shine. Ke ko fuskar sa bantaba gani ba. Nasha gwagwarmaya acikin gidan nan na sarauta Zaraah. Idan nace zan fayyace miki komi sai kinyi kuka Zaraah. Nasha wahala ba kadan ba. Allah ya rubuta ni ce zan zamo tamkar KIBIYAR AJALI (littafina na baya) da zata tarwatsa duk wani tuggu na masarautar basannabas Zaraah . "Gaskia sis kinsha wahala Ashe?" "Tab Zaraah ai wasu abun ba zasu fadu ba. Da sannu Zan sanar miki komi iNsha Allah . Amman yanzh dai Zaraah inason ki rungumi kaddarar auren ki da Maheer. Tabbas auren ku da shi alkhairi ne Zaraah . Barikiji zaraah, Aure yana daga cikin manya-manyar huldodi wadanda Musulunci ya qarfafa tare da kwadaitarwa a kan yin su. Ya kuma gaya wa duniya cewa, sunna ce ta Manzanninsa., " Zaraah! Musulunci ya kula matuqa tare da mayar da hankali a kan wannan ibada ta aure. Inda ya fitar tare da shimfida hukunce-hukunce da ladubbanta. A hannu daya kuma ya tsara haqqoqk kowane dya daga cikin ma ura a kan dan wansa, domin hakan ta ba wa wannan alaqa damar ci gaba da tabbata da dorewa. A haka har yanayin tsarin zaman gida ya zama mai nagarta, ta yadda zai iya samar da a masu natsuwa da kwanciyar hankali, da rayuwa a kan addini. A hannu daya kuma su zama zarata a gaba dayan fannonan rayuwar al mma na yau da kullum. Zaraah . Kina ji kuwa ?" "Ina ji sis ..." "To ki temaka ki ajiye marigayi sudeis a gefe addua ce mafi kusanci yanzu tsakanin ki da shi. Sai Kuma ki juyo ki fuskanci mijin ki da Allah ya qaddara aurenku atsakani Zaraah .wallahi insha Allah zakiji dadin Zama dashi. Maheer Yana kaunar ki Zaraah ni na sani ki yadda.. Nasan kinada ilimi kin Kuma mallaki hankalin kanki kinsan hakkokin aure ai. Da azarbabi na dai bari na sake jaddada miki hakkokin miji akan matarsa. Domin rokonki nake ki tallafa ki Kuma agaza ki dauki Maheer ki ajiye a bargon zuciyar ki Kuma bashi kulawar data zamo doliya agareki Zaraah . Kinaji?" "Ehh" "Auratayya ta taba shiga tsakanin ku?" "A'ah" "Saurari abunda malamin nan take cewa,. "HAKKOKIN MIJI AKAN MATAR SA. An karbo daga Abu Hurairah (RTA) yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: |dan mutum ya kira matarsa zuwa ga shimfidarsa amma bata je masa ba, sai ya kwana (a wannan daren) yana fushi da ita, Mala'"iku za suyi ta la'antarta har (zuwa) wayewar gari [Bukhariy da Muslimne suka rawaito shi] "A wata ruwayar ta su kuma: dan mace ta kwana tana mai kauracewa shimfidar mijinta, Mala'iku za suyi ta la'antarta har (zuwa) wayewar gari A cikin wata ruwayar kuma: Manzon ALLAH (SAW) Yace: rantse da wanda rai Na yake hannunSa, babu wani mutum da zai kira matarsa zuwa ga shimfidarsa kuma sai taki zuwa gareshi, face wanda Ke cikin sama Ya yi fushi da ita har sai (mijinta) ya yarda da ita "A cikin wannan Hadisi: "akwai dalili mai karfi akan haramcin bijirewar mace idan mijinta ya bukace ta zuwa ga mu'amalar aure, domin cewa lallai fushin ALLAH zai tabbata a gareta, a tare da haka kuma akwai la'antar Mala'iku". "Wajibi ne mace ta zamo mai kokari wajen sauke hakkokin mijin ta akanta daidai gwargwado ba tare da jinkirtawa ba, ko ta sanya sharuda ko sharadin sai ya mata wani abu ko ya bata wani abu wannan haramun ne, matukar dai tana halin lafiya, wajibi ne akanta ta sauke hakkin mijin ta musamman hakkin mu'amalar aure duba da in taki amincewa hakan zai cutar da shi ya iya jefa shi cikin hali na damuwa ko sabon ALLAH. "Manzon ALLAH (S.A.W) Yace; Idan namiji ya kira matar shi ga bukatar sa to taje masa ko da tana kan tanda ne [Tirmidhi] Wannan hadisin; Dalili ne akan wajibcin da'a ga miji musamman da'a mu'amalar aure, kuma yana nun mace ta gabatar da da'an akan shagalgalun ta. Shima kuma miji wajibi ne gare shi, matukar yana ha'lin lafiya ya amsa kiran ta in ta bukace sa, domin dukkan su masu hakki ne akan junan su, rashin bata hakkin ta itama zai cutar da ita ya iya Kaita ga sabon ALLAH, " Suka karasa saurara atare. Dije ta katse waazin tana duban Zaraah. Dake kife da Kai. "Meyasa kikaki bashi hakkin sa..?" "Bece... Ba" "Sai yace? Lalle Zaraah . Ai shikenan ba zan zurmama cikin tambaya ba. Amman dai a duba kinji ko?" "Insha ALLAH" "Yauwa tawajena! Kina Whatsapp ko?" "Inayi" "Yauwa zan karba number ki nasa ki acikin group dinmu. Iya mukadaine matan abokan su Maheer . Manya ne. Kowacce gogaggiya ce. Dan munee kanana acikin su. Sai ke da zan saka yanzu . Akwai Aliya matar shamsuddeen ( KAI MIN HALACCI) akwai kuma Batoul matar mubeen . (IGIYAR ZATO) Sai ni dije matar Salman Aliyu. (KIBIYAR AJALI) Sai Kuma DALAAL matar hafezullah . Sai ke Zaraah matar Maheer (SO DA ZUCIYA) ... Akwai karuwa sosai agrp din namu. Duk karshen wata muke haduwa ayi meet and greet ko a hadu a kano ko muje Abuja ko kaduna gidan Batoul. " "Masha Allah! Ai kuwa nagode sis. " "Babu godia a tsakanin mu kanwata . Ban number taki" Karbar number juna sukayi. Suka cigaba da hira . Wanda dije keta Dora Zaraah akan network din aure da zamantakewar cikin sa. Sun wuni suna hira sai yamma Lis Maheer yazo daukan Zaraah . "An daiji kunya wallahi. Ba zaa barta ta kwanaba. Toh shikenan ni zanzo na kwana. " Cewar dije.. "Afuwan gimbiya. Zatazo kwana idan kika haife na 6 " "Kaga masu wanka agidan ka Maheer. Da yardar Allah bi biyu zaku tara. " Ita dai Zaraah daria suketa bata. Ta shige gaban mota tana jiran shigowar sa su tafi. Dije kuwa na tsaye ta rike kofar murfin da Zaraah ke ciki. Bayan motar kuwa manyan paper bags ne dauke da abubuwa kala kala da dijen tabawa Zaraah. "Toh gimbiya mun tafi. Allah ya saka da khairan". "Amin badan halin ka ba. Kawata Kuma Yar kanwata nagode kwarai sai nazo ko?" "Sai kinzo sis. Agayda mun da yaran dan Allah. " "Zasuji zaraah. " Ta rufe musu motar. Yayinda Maheer yaja motar da bisimilla suka dau hanyar komawa gidah... I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ 2/17/22, 11:27 - Buhainat: I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ynog1zhfit0q&utm_content=6k8ur6p PLS FOLLOW US ON IG JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO SO DA ZUCIYA!! ZAFAFA 5 PAID BOOKS PG: 39 A tare suka karasa shiga cikin farfajiyar motocin gidan dasu Haj
Chapter 47 · 0% Book details