← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 55

Sashe 39

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bani nake zartarwa. ? Ya karasa hade da jan kasan leben sa ahankali . Lock din ya cire, Ta fice da sauri har tana tuntube. Ya sauke zuciya kawai hade da girgiza kai. Ya ja motar zuwa bangaren sa. Ya sha mamaki kwarai matuka wajen ganin masu aikin gidah nata rushe rushen bangaren nasa ana sake kawata shi. Zai yi magana kenan sai ga fitowar Addayo daga ciki. Fuskar ta kumshe da murmushi. Gayar da ita Maheer yayi ya na mata kallon karin bayani game da gyaren bangaren nasa. ddayo m na ikko dan albarka. Kaga bangaren ka ya fara sauyawa ko? Ya daga kai alamar eh hade da susar keyar sa. oh me zaa jira, Aure an rigada an daura, Sai tariya kadai ta rage. Ina ita kishiyar tawa ne. a shiga sashen su. auwa inason ganin ku an jima da yardar Allah. ohm Addayo! Saukar yaushe? un dazu fa nazo. Dan na tsaya gidan Harisu ne. kay Masha Allahu. llah ya maka albarka, Allah ya jikan mahaifan ku da dan uwanka. Ta karasa fada tana mai goge hawayen dake tsiyaya a idanunta aamen Addayo ? Ya bata amsa yana runtse idanun sa. uje bangare na nan aka mayar maka da kayan ka kafin a kammala nan din. oh Addayo. Tana gaba da yar sandar da take dogarawa, Shi kuma Maheer yana biye da ita a baya yana tunanin yadda zasu kwashe da Zaraah idan suka tare. Dubada ganin su duka biyun ba kaunar junan su suke ba. Gwara gwara ma shi yakan aga mata kafa awasu abubuwan saboda amanar ta da Sudeis ya bashi. ?. ?. Tana shigewa parlorn nasu bakinta dauke da sallama ta ajiye ledar hannunta akan kujera. Hadi da kwaye hijabin dake jikin ta, Ta ajiye a kusa da ita. Dadaa dake daki tafito tana jijjiga baby sudeis daya tashi a bacci. adaa barka da yammaci. arkan mu.. ove of my life ? Zo nan. ? Ta karbu baby sudeis a hannun ta tana kallon sa. Har cikin bargon jikinta take kaunar baby Sudeis. Idan ta dauke shi ji take nutsuwa da kwanciyar hankali ta dabaibayeta. Dadaa na hankalce da ita, Ta zauna akan kujera hade da janyo ledar da Zaraah ta ajiye. annan kayan fa? aya Maheer ne ya sayo a waye? ? Dadaa ta tanbayeta tana dudduba hijaban da su safa hadi da sabuwar wayar. ai nawa ne ? ta karasa cikin kasa da murya. auwa zo ki zauna anan Zaraah. Ki bani hankalin ki da nutsuwar ki. Abunda zan gaya miki abune mai muhimmanci a rayuwar ki. Kinga saura kwanaki kalilan ku fara jarabawar kare makaranta ko? Dan haka inaso kafin lokacin ki samu nutsuwa ki kuma sa aranki hukuncin da aka zartar akan ki shine mafificin alkhairi agare ki. ohm Dadaa. ? Ta fada, Hadi da zama a gefen kujera . Tuni hawaye suka shiga reto a idanun ta. llah yasa ba laifi nayi ba Dadaa da aka yankemun hukunci a wallahi ko d ya! Hasalima nina bada hadin kai wajen yanke hukuncin. Illa dai kiyi hak ri na rashin neman yarjewar ki da bamu yi ba. Kina sauraro ko? oh Dadaa. Ina ji a wani abu bane fyace daurin auren ku da akayi da Maheer. Maheer dai yayan Sudeis marigayi Dadaa na karasa fada, Maheer ya doka sallama ya shiga parlorn. Don sanarwa Zaraahn nema su da Addayo take Zaraah ta daga idanunta da suke zama tamkar garwashi saboda tsananin yadda suka rine sukayi ja. Ta sauke akan Maheer. Hawaye d ya na bin d ya suka shiga kwarara a fuskar ta. Unedited Sorry for the late post Thank you *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar XOXOWRITES 2/9/22, 20:31 - Buhainat: SO DA ZUCIYA A LOVE SOO.BEAUTIFUL NANA HAFSATU ZAFAFA5 PAID NOVELS Gabanta ya tsananta bugawa. Kallon idanu cikin idanu tayi masa. Wanda shi kansa sai dayaji rashin jin dadin kallon da take masa. Kallo ne na kaci amanata da sauran su. "Dadaa barka da yammaci." Ya tsugunna yana kwasar gaisuwa wajen Dadaa. Idanunsa na kallon gefe. Jikin sa na nuna masa alamun har yanzu idanun Zaraah na kansa . Ita kuwa Zaraah bude shafin sabon kuka tayi. Sudeis kawai take tunanowa da ire iren kalaman sa da suka zama tamkar wasiyyar sa ta karshe... Ta fashe da wani matsanancin kuka mai karya zuciya. Hade da rungume baby sudeis ta kankame shi tamau. "Wayyo Allah na Dadaa. Shikenan sudies ya tafi kenan har abada. Dadaaa meyasa za'a bani Maheer. Wallahi zan iya zaman aure da kowa kuka hadani dashi. Matsayar ba Maheer bane. wallahil azim bana kaunar Maheer Dadaa. Na tsane s.." Kafin ta karasa Dadaa ta wanke fuskar ta da zazzafan mari me tartsatsi. Saura kadan baby sudies ya fadi. Dadaan ta karbe shi ta ajiye shi cikin dan gadon sa dake gefenta . Maheer kuwa ya lula duniyar kalaman Zaraah. Yau bama kwaskwarimar Yayan sai Maheer gatsal.? Ga kuma furucin madaukakiyar kiyayyar tsanar da take masa . Duk kuwa da shima baya son ta da aure. Ya tabbata baya 'kinta amatsayin ta na kanwa agare shi. Tana daga cikin masoyan dan uwan sa marigayi. Kuma tabbas shidin bazai iya dubar mahaifin sa ba Kai ko Dadaan ce ma ya kallesu yace baya kaunar Zaraah ya tsaneta. Gaba daya tunani ya shigaa zagaye kwakwalwar sa. Ya furzar da iskar bakin sa dai dai lokacin daya kammala tunanin ya jiyo kalamai masu dauke da umarni daga bakin Dadaa zuwa zaraah. Don dik maganganun ta bai ji ko daya ba. Domin zama yayi tamkar mutum mutumi ne. Shi dai kawai a zaune yake. Amman jin sa da ganin sa sun dauke na wasu yan dak'ikai. "Ki Kuma kwashe kayan ki ki bar gidan nan tunda haka Kika zaba. Zai sawwake miki. Kuma karki kuskura kije gidan wani nawa. Ki wuce can rimin kebe. Mahaifin ku ya sama miki wani mijin. Na tabbata cikin su Haruna mai gurasa ko Nata'ala me kwasar kashi zai aurar dake. Kuma wallahi karki soma zuwa waje na ko wani nawa kinji na gaya miki Ashe dama mutum na sauya hali rana daya? Maheer sauwakewa yarinyar nan." Dadaa ta karasa cikin fushi. Muryarta har rawa take. Tacigaba da cewa "Badan an temaka an tsamo mu daga halin rashin da muke ciki ba. Ke kin isa kallo ma wani a zuri'ar gidan nan ya miki? Shashasha kawai" "Wayyo dan Allah Dadaa kiyi hakuri ki yafemun. Wallahi bansauya hali ba Dadaa" "Dadaa dan Allah kiyi hakuri. Kar kiga lefinta. Baa sanar mata da wuri ba. Kiyi hakuri ki yafe mata.". Dadaa ta girgiza kai kawai. Hadi da Zama akan kujera tana sauke numfasbi. Zaraah ta rarrafa ta rike kafafun Dadaa tana bata hakuri. Hawaye nata ambaliya a fuskar ta . Maheer da Zaraah dai hakuri sukayi ta bawa Dadaa. Dadaa mamakin Zaraah ne kawai ke mamayeta. Ta samu miji mai tarin kamala dan gidan masu dattako da sanin ya kamata. Amma ta dinga furucin nuna kiyayyarta a fili? Ta ja tsaki yafi sau ba adadi. "Maza kafin na hamb'are ki. Maheer akwai abunda kake bukata ne? Yi hakuri baka fadi abunda zaka fada ba muka sako wani zancen." Dadaa na rufe baki, captain na shiga parlorn bakin sa dauke da sallama. Addayo na biye dashi a baya. Gaisuwa ce ta biyo baya. Kafin su tambayi abunda ya faru, Tuni Dadaa ta fetsa musu komai ba abunda ta rage. Addayo ta murmusa kawai tana duban su baki daya. Kaunar Dadaa da zuri'arta suka sake maimaye kambun zuciyarta . Domin ko captain ka kalla zakasan ya samu nutsuwa da warakar zuciya. Yayi kiba ya mayar da jikin sa. Fatarsa har canzawa tayi saboda sheki da santsi . "Duk naji komai Jammu. Kuma batayi lefi ba yarinyar nan. Karma kiga lefinta wallahi . Ni banmasan batada masaniya ba sai dazu da wannan yaron ke gayamun. Nace zahiri an tafla babban kuskure. Kuma yakamata a nemi yafiyarta. A Kuma tausasa mata zuciar ta. KO kadan banga lefin taba. Ace rana tsaka kwatsam a sanar da kai wai dama an daura maka aure a baya? Aina ake haka? Uhm? Yanzu kota kula wasu da ba muharramanta ba a baya Sam batada lefi. Lefi na kan ku ku uku. Danme ba za'a sanar mata ba? Sai kawai rana tsaka a shigaa zuba mata doka? A sayo hijabai da komai akuma mata dole kan amfani dasu? "Zancen gaskia ba'a kyautawa Zaraah ba. Kuma dukkanin ku sai kun nemi afuwarta. Ku kuma nemi afuwar ubangiji abisa Keevin da kukayi. Allah ya yafe muku. Shysa ina zuwa na tambaya Zaraah ta tare ko kuwa? Wayaga garmaho. Ashe ma ko masaniyar auren bata da shi. Saboda haka na Ikko da ke kishiya ta Zaraah. Ku bude kunnuwan ku dika ku saurare ni, "Aure na da alakaa ce ta haliccin zaman tare tsakanin namiji da kuma mace. Ana yinsa ne saboda abinda aka haifa ya samu asali, da mutunci da kiwon iyaye. Kuma shine maganin zina da a marasa iyaye ?. Aure muhimmin abu ne ga al mma. Sabili da haka akwai hanyoyi ayyanannu na tabbatar dashi.[2]ko kuma ace ,Aure alaka ce ta halascin zaman tare tsakanin namiji da mace, Ana yin aure domin abubuwa da dama, daga ciki akwai kariya daga zina, samun nutsuwa da kwanciyar hankali, samawa abin haihuwa (abin da aka haifa wato 'da ko
Chapter 39 · 0% Book details