Sashe 18
So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ciwon kai da zai dan yi na kwanaki. Tinda Alhamdulillah tunanin sa da komai ya dawo dai dai yadda akeso, Rik wannan takardar, Irin abincin daya kamata ya dinga ci kenan. Sannan kuma kada adinga bata masa rai. Abu na karshe shine mun baku takardar sallama, Nanda wata 8 Idan Allah ya kai mu sai ku dawo, Allah ya kai mu. ayi kwarai matuk , Mungode i zan fita ziyartar sauran wards, Idan kun tafi Allah ya kiyaye hanya ya tsare. ohm Insha Allah, Mungode Dr. Allah ya saka muku da alkhairi Kai da sauran yan uwa ma ikatan lapia, Hakika kun kula da mu, Kun kuma bamu kulawa ga duk abunda ya danganci rashin lapiar sa, Mungode sosai. Sake yiwa juna bankwana sukayi. Capt. Muhd ya rike hannunsa suna musabaha lokacin da likitan mai suna Dr. Hamoodi ya rike hannunsa suna sallamar bankwana. agode k arai Dr. Allah ya saka da alkhairi. llahumaa Aamin Capt. Allah ya baka lapia mai dorewa yasa karshen wahalar kenan. Aamin. Sake gaysawa sukayi, Sannan Dr. Hamoodi ya kara bawa Alhaji Harith hannu sukayi bankwana. Bayan fitar sa Alhaji Harith ya dubi Capt. Muhd, omai normal ko? alau ma kuwa! Alhamdulillah. Ai inaga Bappah idan akace muyi yar tsere da kai sai na wuce ka. A gafarce ni. ? Capt. Muhd ya karasa fada yana sakin tattausan murmushi. oh Alhamdulillah Capt. Ai haka muke so. uba nake Bappah. Suka saki dariya baki d ya. Tukun sannan alhaji Harith ya taya Capt. Muhd shirya kansa. Cikin sababbin kaya kirar riga da wando na kananun kaya, Ya dora babbar coat akansa. Kana kallon sa zakasan tabbas sun hada jini da Alhaji Harith saboda tsananin yadda suke kama. Lokacin da suka fita masaukin da alhaji Harith ya kama musu suka wuce, Sukayi sallah. Capt muhd ya jima a sujjada yana addu i. Yasha kuka kwarai matu a lokacin da ya daga hannuwa yana mai yiwa Allah godia a bisa lapia daya bashi. Bayan tsawon lokaci daya dauka acikin rashin ta. **WASHE-GARI** A jirgi bayan sun tashi daga kasar Qatar zuwa Nigeria. Cikin hirar da suke yi ne. Alhaji Harith ya sako zancen gidan na Capt. Muhd. Capt muhd ya girgiza kai kawai bayan ya karasa sauraron baffan nasa, Cikin faffadan murmushi yace, i Bappah... Banajin zan arasa zama da matan nan, Domin bayana suke son gani tinda basason gudan jini na. Zanma fad wa Addayo dana koma zan sauwake musu. ar kai haka Capt. Yadda kake da hakuri ka dubi girman Allah kabar komai ya wuce. Tunda abunda suke fatan bai farun ba. Kuma kai gaka nan Alhamdulillah! Allah ya yaye maka lalurar da sanadin shirin su ya jefa ka ciki. Sai dai mucigaba da yiwa Allah godia kawai.. appah! Ni da so nake kasa baki acikin maganar nan. Nagaji da TAKUN SAAKA da ake da matan nan. Ta temaka ta lamunce mun na sawwake musu. Bappah! Zama da irin shedanun matar nan hatsari ne. Gaba d ya ZUCIYAr su sun isissima mata mugayen alkaba ayi hak ri dai, Mu kuma cigaba da adduar Allah ya zaba abunda yafu alkhairi kaji ko? aji Bappah! Toh Aamin Yaa Rabbi. asan an kusan kammala komai na islamiyar nan, Masha Allah ba abunda ya rage sai arashen abun rubutu da za sassaka da signboard din da za sa ka akan layi. Shima ? muke jira suyi approving sunan makarantar kawai. asha Allah Bappah! Sannu da ko ari, Nagode kwarai, Allah yabar zumunci ya kuma kara maka lapia da nisan kwana mai amfani.. Allahumaa Aamin. amin Yaa Rabbi Capt. Komai da nake ai da dukiyar ka ne, Sai fatan Allah ya kara maka yalwar arzuka. amin Bappah! Kai kuma kanayi da jikin ka da jinin ka ba, Ai kaine mai yi gaba d ya Bappah! Yanzu kenan Bappah Addayo ba zamu sanar mata ba sai dai tagan mu? h mana sai tafi farin ciki, Allah dai ya kai mu lapia. llahumaa Aamin. Sun dau tsawon lokuta kafin su sauka a birnin kano dake k sar ta Nigeria, Sudeis ne ya dakko su a airport ?, Yayi matuk r Farin cikin ganin su. Musanman Capt da yaga ya warke kalau dashi. Rungume shi sukayi a tare. Dan dadi sai da kowannen su yayi kukan farin ciki. Kai tsaye sudeis ya kai su gidan na Capt. Muhd. Babu kowa sai Addayo, matan gaba d ya kowacce tatafi aiki. Mazan gidan ma sun tafi ofishin su, yammatan kuma wasu na makaranta. Sashen Addayo kawai suka zarce. Fadawa mai karatu adadin farin cikin da addayo ta shiga yayi kadan kalamai su zayyano muku. An Sha kukan farin ciki, Anyi raha hade da wasa da dariya. Addayon kuwa murna uku ce ta hade mata. Madaukakiyar murnar da tafi yi itace samuwar lapiar anta Capt. Muhd. Da jikanta Sudeis. Da kuma gani guda d ya da Allah ya albarkace ta dashi wato alhaji Harith. Dukkanin su ta dau tsawon lokaci kafin ta sasu a idanun ta. Sai yau da Allah yayi. ***GIDAN MALAM ARDO(AURE-AURE)*** **Safiya ta zama rana, Rama ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha , Watan bikin Ardo ya shigo, Tuni ya azalzali Jimmamman ta kwashe kayanta daga akin mai sarari ta komar da kayanta ? dakin girkin da ada shi ke amadadin parlorn ta. Kujerunta uku da wardrobe dik ta sayar dasu, Saboda bazeyiwu ta sanya suba sunyiwa akin girma. Kullum sai Ardo yace ya shikata, Ita kuma tace wallahi saki d ya ne. Tana da igiya biyu awajen sa, Yakan jera tsaki ba adadi aduk lokacin da ta isheshi kan bazata ko na ba, Takance ita taga gidan zama babu inda zataje, Ai kuwa kullum Sai tasha shika shikan rashin mutincin Ardo. Itama tabi layin su Atuwa sam bata gaban sa. Dadaa kuwa kullum cikin adduoi take, Da neman zabin Allah abisa abunda yafi alkhairi a rayuwarta, Tarasa wanda zata nema ta gayawa damuwar ta. Gashin kusan kullum Sai sunyi waya da Hajia amina ta wayar Modibbo. Sam bata taba gaya mata halin da take ciki ba, Bare dan uwanta dake k uye guda d ya ne dama yayi ragowa kuma shidin makaho ne. Wasu zafafan hawaye ne suka shiga mata reto a fuskarta, Hango mata na shige da fice a dakin amaryar Ardo da za kawo. Tabbas yayansu basuyi sa r uba ba. Domin Ardon duk wacce zai aura sai ya kashe mata kudade a dan banzan bashin dayake ciwa kansa, Kowacce kuma data shigo zai rabu da ita. Tarasa meyasa matan ke amincewa auren sa, Sarai bayan sunsan adadin yawan sake saken auren da yake. Sai dai zucia kowa da irin tasa, Wasu matan akan kudi idanunsu rufewa yake. oh Allah ya kyauta, Ta mu qaddarar kenan... Allah ka musanya mana da mafificin alkhairi. ? Ta mike ta tada sallar da zatayi istikhara na kwanaki 3 chas. Aranar ta kammala. Ta karkade yar katifar Zaraah tayi kwanciyar ta bayan ta rufe yan biyunta da adduoi. Ta saya kofar dakin nata. Lokacin data jiyo ife ifen gudar amaryar Ardo ta 9!!! Tuni zuciar ta ta yanke mata barin gidan shine mafi alkhairi..!! Ango Malam Ardo ya gwangwaje da amaryar sa Rumallen Nababa mai ice, Bazawara ce yar kauyen su Dadaa (unguwar kuka fanda)!! Dadan sam batada masaniyar wacece, Cikin dare dai ihun Ardo ya karade cikin gidan da unguwar baki d ayyo Allah na! Kai garin dadi na nesa, Rumalle Allah ya miki albarka, Qur nin Ubangiji na baki gidan nan halak malak, Takardun na cikin dakin Modibbo a jakar kayana. Wayyo Rumallen Nababa, Na baki kai na gabaki d ya sai yadda kikayi.. ? Sambatun da Ardo keta sakarwa amaryarsa kenan yayinda suke nunawa juna farin ciki Cikin kirsa ta rad masa a kunne; ankwali yaja hula kenan? aja mana Rumalle tah, Billahil lazi dankwali yaja hulunan Ardo da gangar jikin sa hade da zuciar sa baki d ya. Atuwa dake kwanciyar bakin ciki ta jiyo su, Cikin jan tsaki hade da nanawa cinyarta da sauro yaciza duka tace, ankadaddu! Yan gaba da iska, Allah ya kwashe muku albarka. *AL-MADRASATUL SHUHADA'I LI TAHFEEZIL QUR'AN* ***Tunda driver ya sauke ta, Sanye take cikin uniform din islmiyar, Mai dauke da kalar amber orange da white jilbab sai niqab bak , Da socks baka. Yana tsaye daga barandar ajikin sa dake sama, Sanye cikin jallabiya, Baisa hula ba , Gashin kansa ya kwanta luf gwanin sha wa. Manyan idanun sa ya sake zuba mata ya kasa dauke su daga gareta. Zuciar sa ramkar Zata faso kirjin sa ta fado. So yake ya tabbatar wa ZUCIYAR sa, Itace ba gizo bane. Yanayin bakon lamarin daya shige sa ne ya sashi sauke idanunsa ahankali daga kanta. Yana fatan shigowar ta cikin makarantar, Don tabbatarwa idanun sa itace. Domin bai manta da manyan idanunta Dake dauke da kwayar idanun coffee color. Tabbas sudeis ya kamu da SO DA ZUCIYAr Zaarah Ardo Borkindo... Saura kadan ya ci tuntub ya fado lokacin dayaga tashigo ciki ta nufi ajin da zai koyar. Wata katuwar bahaguwar zucia ya sauke mai nuna hamdala ga samun abun bege. #unedited #ALHAMDULILLAH MUN KAMMALA SHIMFIDA, YANZU ZAMU SHIGA GUNDARIN LABARIN, TAWAN TA UNCLE ABDULL (BILLY TAHH) TAKANCE YANZU WASAN ZAI FARA I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI