Sashe 28
So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
furnitures da komai. Kamar sabuwar amarya Zai 'bare a leda. Jikin su Haj Iklima yayi sanyi kwarai matuka. Kuma Addayo Kai tsaye ta sanar dasu auren da mijin nasu Zai Kara. Sun tashi hankulansu kwarai matuka. Wanda hakan da sukayi ya jefa zukatan su ga dimuwa. Domin 'barau 'barau capt muhd ya futo musu a mutum ya nuna musu ya san abunda suka aikata a bayan . Yana Gama fada ya fice kai tsaye ya wuce gidan ALHAJI Dangoje cikin shigar sa ta alfarma. Sai kamshi ke tashi ajikin sa Bayan sun gaysa dasu Haj Amina da kuma Alhaji Dangoje dake tsokanar sa. Hajian tayi masa iso zuwa ga parlorn baki. Nan ba jimawa Haj Amina ta raka Dadaa parlorn inda Capt muhd yake . Tun da tashiga parlorn yake binta da kallo. Kallon ta ya shiga yi tamkar saurayi yaga budurwar sa. Wanda hakan da yake yi ya jefa Dadaa fadawa kogin kunyar sa. A 'darare ta zauna nesa dashi. Ta zuba kyau cikin dogon jilbab din dake jikin ta. Maroon color wanda ya karawa kyakkywar fuskarta kyau. Shi Kuma capt. din yayi shiga cikin manyan kaya shudaye. Ya dora hular zanna bukar. Kamshin turaren sa ya gauraye parlorn baki daya. Gaisawa suka fara Yi Da Dadaan. Cikin nutsuwa da kalama. Gwanin sha'awa Capt muhd ya fara yiwa Dadaa bayanin kansa ya 'karkare da, "Sai abu na karshe Kuma muhimmi shine a yanzu Ina da mata biyu da yara 9. Matata ta uku Wanda a yanzu itace ta kasance ta farko tanada yara 4. Sai mai biye Mata tanada yara 3, Sai maza biyu Wanda iyayen su duk sun rasu. Jamila da Jamila kenan. Ya da kanwa ne. Yayar na Fara aura muka samu albarkacin 'da namiji. Sai tarasu. Aka bani kanwar ta mai suna Jamila itama. Duk suna daya ne dasu. Kowanne cikin su ya ci sunan kakannin su ta uwa da uba. Jamila ta farko ana ce da ita ('Bingel) kanwar ta Kuma jamilann ake CE Mata, Toh dai itama kanwar sai Allah ya mata rasuwa bisaga wani hatsari shiryayye da aka Mana cinne dashi. Wanda Nan gaba Zan sanar miki komai. Itama kafin rasuwar ta, Alah ya azurrta mu da albarkacin 'da namini. "MAHEER shine 'da na na farko a duniya, Wanda ya kasance 'dan Jamila data rasu wajen haihuwa ko!? Ina fatan kina ganewa?" Dadaa ta 'daga Kai. Capt muhd yayi murmushi kafin ya cigaba da cewa, "Toh anan bayan wani lokaci sai aka auramun kanwar ta tacigaba da shayar da yaron Bingel dayaci suna MAHEER. Bayan wani dan lokaci sai na Karo aure. Wani oga na daya samamin aiki a lokacin sai bayani 'yar sa na ayra bayan shekaru budu da yin auren matata ta uku kenan. Toh dai bayan na auro Maijidda sai Jamila ta haihu. Muka samu albarkacin 'da namiji muna ce dashi SUDEIS. "Wanda insha Allah nan gaba Zan sanar miki komai. Amma kafin sannan Maheer yana kasar Egypt acan yayi karatn sa da komai. Ya kanzo Nigeria. Amma iya Ikko (Lagos) yake sauka gidan kawu na kanin mahaifya.tah. Wanda Matar sa Haj. Laila ke rikon dukkanin su a baya. Kafin a mayar da sudies zuwa kasar saudiyyah. "Shi Kuma Maheer Yana kasar Cairo Egypt. Gaba daya dangi musanman mahafiya ta ma muna Kiran sa da na Ikko........" Ya karasa fada hade da daukar ruwan robar gaban sa ya kurba.... 2/1/22, 10:21 - Buhainat: SO DA ZUCIYA!! I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ Dadaa dai tayi shiru tana sauraron sa, Hadi da jujjuya kalaman da yake fada a kwakwalwar ta. Sai daya sha ruwan sosai, Tukun sannan ya zare robar ruwar daga bakin sa. Ya saki katuwar ajiyar zuciya mai dauke da hamdala. Yanayin yadda ya sauke zuciyar tasa zaka gano tabbas ya sauke wani boyayyen nauyi dake addabar zuciyar sa. "Jameelah! Baki ce komai ba" Ya karasa hadi da zuba mata manyan idanun sa akanta dake nuna tsantsar kaunarta a zuciyar sa. "Allah ya jikan su da rahama." Ta samu kanta da fadin haka. "Amin Aamin! So duka dai. Kamar yadda na gaya miki,' Yaya na 9. Maza bakwai mata 2. Sai matan da igiyar aure na ke akan su. Maijidda ita likita ce dake aiki a asibitin kwararru na murtala muhammad, Sai ikhiima ita kuma babbar ma'aikaciyar banki ce. Yara kuma wasu na aiki wasu na karatu , Ban aurar da kowa cikin su ba. Amman ina fatan aurar dasu da zarar lokaci yayi. Tamkar dai yadda neman kowane aure yake, Zaki ga kowa da sanadin dayaa sa yayi 'karin, Ni dai a nawa bangaren zan kara aure ne saboda zucia ta ta aminta da wadda zan auro, Mahafiya ta ta amince fiye da kalmomi, Sannan dalili na biyu zan kara aure ne saboda gazawar da ke cinye zucia ta ta farfado. A yanzu ba abunda nafi bukata fiye da akula da ni. Wannan shine dalilin dayasa zan aure ki Jameelah. Ina kuma fatan zaki tallafe ni ki amince ki aure ni. Insha Allahu zaki same Ni mai rike amana da kuma kyauta tawa.. Ko?" Yadda ya karasa maganar yana langabar da kansa tamkar wani matashin saurayi ne hakan ba karamun dariya ya bawa Dadaa ba. Ta danyi murmushi kawai 'kasan zuciyar ta kuwa cike yake da fargabar irin ilimin matan sa. Taya ma ya yanke hukuncin auren ta. Bayan ita din batada ilimin boko sai na arabi. Sam ba zata iya gogayya da su ba. Tunda su din gogaggu ne da suka shak'i ilimin boko suka 'koshi. "Ba ki ce komai ba" Ba tare da masaniyar labarin zuciyar ta yafito ba Dadaa tace, "Bani da ilimin da zan iya gogayya da matan ka." Yadda ya zuba Mata idanu ba ko kyaftawa yasan ya Dadaa gano baranbaramar da tayi. Kafin tace wani abu tuni ya rigata. "Haba Jameelah Kar ma ki sake dakko maganar nan. Ke kuwa ki me da ishasshen ililin da zaki tafiyar da gidana da ni kai na baki daya. Banason auren mu ya dau lokaci Jameelah . Ni da son samu na ma a daura gobe da yardar Allah...." Dadaa ta sauke ajiyar zuciya tana lankwasar da yatsun ta dake dauke da maroon color lalle "Kinji? Idan har ban takura ki ba. Don inaga babu wani abu da zai dau lokaci. Mu ba yara bane,So ba wani hidindimu da zamuyi Wanda zai ja lokaci. Yanzu dai ga wannan ba yawa idan da akwai abunda kike bukata sai a saya." Ya karasa maganar hade da ajiye wata leda bak'a mai dauke da bandir din kudi. Dadaa dai tayi shiru tamkar ruwa ya cinyeta. Zuciar tace ta shiga tsananta bugu. Gaba daya jj take tamkar mafarki take Wai yau itace babban mutum Mai cike da Kamala da dattako yazo Yana neman aurenta? Babban mutum gogagge wanda ake damawa dashi a yankin masu farcinan susa. Ga matan sa masu dimbin ilimine. Da gayu . Wai yau ita Dadaa matar Ardo a baya, Yar kauyen kayau. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha'u .Ta 'daga idanunta ta sauke akan bakar ledar daya ajiye a gabanta. Da sauri jiki da bakinta na rawa na tsoron ganin himilin kudin dake cikin ledar gaban ta tace. "Ba abunda nake bukata yallabai. Mungode kwarai." Ta karasa hade da 'dan janye ledar daga gabanta. "Yallabai?" Ya tambaye ta yana sakin tattausan murmushi. Itama murmushin ta danyi tana maida kanta kan 'kofa. Ya kalli agogon hannunsa kafin ya mike tsaye Yana mai gyara zaman hular kansa "yalla...." "Karki karasa don Allah. Wai yallabai kamar wani alhajin kauye, Dole acanzamun suna da zarar an daura." Tamkar wata yar budurwa haka Dadaa ta samu kanta da rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta. Murmushi ya sake yi. Kyakkyawar fuskar sa mai 'dauke da annurin kamala ta fad'ad'a da farin cikin Jammu dake gaban sa. "idan har ba renawa ki Kayi ba. Dan Allah kada ki sake cewa na dauk a. Zan koma gida, Kinji ko?" Dadaa ta samu kanta da daga masa kai alamar eh. "Ina yan biyun mu da Zaraah?" "Suna ciki " "A kirawo su mu gaysa sai na wuce " Mikewa Dadaan tayi ta hau saman. Gaba daya kunya duk ta kamata. Ai kuwa tana ganin Na'eelah tace da ita. "Kira su Zaraah kuje ku gaysar da bakon su Abba (Alhaji Dangoje) a parlorn baki." Da sauri Na'eelah ta juya ta shige dakin Zaraah inda suke baki daya. Gaya musu tayi umarnin Dadaa suka wuce parlorn kai tsaye. Cikin faraa da nuna kaunar sa gare su Capt muhd ya shigaa amsa gaisuwar su Yana wa yan biyu Wasa . Lokaci daya yaji kaunar yaran sun shiga can cikin zuciar sa. Sarai ya gano Dadaa ba zata dawo ba. Don haka ya dau ledar da damun kudin yake ciki ya bawa Zaraah yace takai wa Dadaa Ya kirawo alhaji Dangoje a waya. Ashe har ya dawo Yana parlorn sa . Can yaje suka shigaa hira. Nan Capt din ke shedawa alhaji Dangoje auren Dadaa da yake son yi nan kusa ba sai an debi lokaci ba Dakyar dai Alhaji Dangoje ya sha kan Capt Kan ya bari Nan da sati biyu sai ayi daurin auren. Domin ya kamata ya bawa Dadaan lokaci da itama zata shisshirya komai