Sashe 38
So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ardo dake leken su Capt daga waje ganin suna shirin futowa hakan yasa shi saurin yafito su garzali abokan sa. "Ku zo ku gaggaysa da surikin nawa." Ya janyo hannun Maheer da fitowar sa kenan daga cikin masallacin. "Zo ku gaysa da abokai na." Ya fada yana mai nunnunawa Maheer su da yatsa. "Wannan garzali ne uban Adama kawar Zaraah, Wannan shine Mati jatau me kayan gwari, Wannan kuma akilu ne uban su Hannafi abokin Modibbo. Wannan kuma sabitu ne me gidan wamka da bahaya. Wannan kuma inusa ne dan uwawwu me kosai. Can wa'incan dake tsaye ajikin bishiya kana ganin su?" Maheer ya kada kai alamun eh "Toh ubale ne me gurasa, Sai liman, da kuma 'Dan tani me ice." "Masha Allah" cewar Maheer da ke kakaro murmushi. "Yauwa shine mijin zaraahn yar awaje na. Sunan sa Masheer " "Maheer ne bappah " "Yauwa Masher. Mahaifin sa matukin jirgin sama ne a baya. Gashi nan shima. Sai aminin mahaifin nasa gashi can shi Kuma attajirine . Usulin sa dan kauyen Dangoje ne dake fandar mu. Yo duka ma dai yan fandan ne. Yauwa." Abokanan Ardo suka shigaa leka kayuwa suna ganin Maheer da Capt . Alhaji Dangoje yana daga can gefe yana murmishi. Domin gaba daya zubin Ardo da yanayin maganar sa dik dariya take bashi. Wani me balangu dake tsallaken titin masallaci Capt yasa ya yankowa kowa a takarda. Gefe daya kuma ga lemuka da suka furfito dashi daga cikin mota. Mutanen wajen suka shigaa wanke bakin su da nama suna kurkurawa da lemo. Lamarin sai sam barka. . . . Ta cikin barandar parlorn ta suka hango wucewar Dadaa. Dauke da wata yar jaka a hannunta. Haj Jidda taja tsaki ta saki labulen da suka dage. "Wannan mata ko bak'ar munasira." "Ai bantaba ganin makirar mace ba irinta wallahi." Cewar Haj Iklima. "Allah kuwa yadda kikasan mijin nata ne ita daya. Nacacciya." "Ai ko kadam jinina bai hadu da ita ba. Rannan ina hango dosowarta na sawa kofar lock taita bugawa naki budewa. Shine ta koma." "Mun biyu kenan. Don ina jiyo sallamar me aikinta na rufe cikin dakin. Ta karaci shawaginta ta tafi ." "Kingan shi. Gotogoto jeme jeme zakiga ya sab'a yaron a kafada yana zagaye gidan nan dashi." Haj Iklima ta rike throwpillow tana gwadawa dashi. "ke kuwa yana rawar takashi yayi amaria. Ko nace bz mai tarin agola. Yadda kikasan akan sa aka fara haihuwa. Kamar du namu yaran ajiya aka bashi ba mallakin sa ba ne." "Hmm! Allah dai ya kyauta." "Aamin" "Ga shegun agolan yaran nan nata sai kace shi ya haife su . Dan gaba da renin hankali." "Ke kuwa an jika an bashi ya sha." Suka shigaa yi da Dadaa da captain tamkar zasu yayyanki naman jikin su suji dadi. Dadaa ta karasa yar barandar dake sashen Capt. Jikinta sai tashin kamshi yake yi. Yana ganinta ya mike ya taro abarsa yana murmishi. Dadaa ta gayar dashi cikin girmamawa. Ya amsa da faraa. "Sai kamshi kike Jammu naa! Yau ma dai turaren kayan kika yi?" Ya karasa fada yana sinsinar kasan mayafinta daya kai kofar hancin sa. "Eh mana turaren yerwaincenseandmore dinnan dai dana gaya maka na saya." "Habawa wani irin kamshi kike so heavenly exotic. " Ya fada yana mai jinginar da kan dada a kafadar sa. "Kaga bansan mekace a karshe ba. Anya bazan koma boko ba na faro daga farko. Ka amince mun kaji?" Ya girgiza kai yana murmishi . "Ke nakeso na ke kuma kauna ba karatun boko ba. Nama fi kaunar ki a haka, Ga ki a hakan kika zarta wasu matan da suka kurbi romon boko suka koshi. Ina kaunar ki sosai Jammu nah. Shi yasa banason ko yaya kiyi nesa da ni. Ni kuwa ya maganar business din da nace me zaki fara na baki kudin?" "Godia nake bappan sudies . Ai ni gani nake da kabar zancen kasuwancin nan. Ni da yara ba abunda muka nema muka rasa. Komai ka dauke mana shi bappan sudies. " "Karki kara fadar haka. Ni dai kiyiwa wa kikace ma magana? Cikin sati mai kamawa nakeson jin sunan kasuwancin da zaki kinji ko?" "Na ji bappan su. Kawo hannu a yanke qumba naga tafito da yawa." Dadaa ta karasa tana mai zaro yar jakar hannun ta dake dauke da kayan yanke farce. "Godia nake uwar alkhairi. Baki na ba zai iya nuna tsantsar farin cikin da ke nunkuwa ta sanadiyyar ki ba. Allah ya saka miki da alkhairi. Kece gugar kafata. Gyara mun farata na. Yimin tausa da sauran su. Jammu nah kin gama sace zuciyar captain baki daya." Daria suka saki baki daya. Dadaa ta rike hannunsa cikin hankali da nutsuwa tashiga yanke masa faratan da gyare masa su tas... HAKA kawai ya tsinci kansa da tsara sabuwar doka ga dalibai mata. Na sanya safar hannu data 'kafa. Duk dalibar datazo babu su to zata karbu hukunci na kawo tsintsiya ko tabarma da doriyar bulala 3 zazzafa. Yana daga zaune tun dazu yake jiran fitowar ta daga cikin gidah . Yan biyu ne suka fara fitowa daga cikin gidah suka bude bayan motar suka shigaa bayan sun gaishe shi. Sai data mula tasha iska tareda doriyar adduar Allah yasa yayi zuciya yatafi. Don sam bata kaunar sabuwar tsurfar daya dauka ta shi zai dinga kai su inda zasuje ya kuma dakko su. Ciki harda makarantar boko da islamiyya. Ranta a matukar turnike tafito. Saboda tsananin yadda take jin takaicin yadda Maheer yake neman mulkar dukkaninta batare da saura ba. Ta bude murfin motar da karfin gaske tana yatsina fuska. Nan duniya bawanda ta tsana sama da Maheer . "Zaraah" Ya fada ahankali yana tada motar. "Na'am" Ta amsa cikeda takaici. "Barka da rana" Tayi biris bata amsa ba. Ya saki tattausan murmushi. Saboda Yana son ya zolayeta. Sam taki sakin jiki dashi. Gashi batasan 'baranbaramar da akai da ita ba. Kai tsaye ya wuce islamiyyr . Ya karasa parking Yan biyu na Shirin fita ya hango hannunta ba safar hannu. Gashi tayu lalle. Yatsunta da kafafun sun dau lallen takara haskawa. "Zaraah! Meyasa baki saka safa ba? Uhmm? Zaraah?" Ya karasa Yana kwantar da kujerar dayake kai ya maida dubansa gaba daya kanta. "Bani da su." "Ni inada su" Ya fada ahankali hade da zaro murfin gaban motar ya ciro sabuwar safar hannu data kafa, "Gashi sa" Wafcewa tayi tafice daga cikin motar. Maheer ya girgiza kai yana murmishi. Ya haye ofishin sa. Minti kadan sai ya leka ajin su Zaraah ya tabbatar babu namijin dake magana da ita cikin dalibai. Haka kawai Maheer ya samu kansa cikin kishin zaraahn. Wani irin kishi da bai taba kawowa ba kuwa. Ko da aka tashi daga makarantar', Shopping mall ya wuce dasu kai tsaye. Ya shige ciki wajen kayan mata. Ya shigaa lafto hijabai kala kala. Masu mugun tsawo da kauri. Da sabuwar waya fil a kwali. Ya wuce mota bayan ya biya kudin Zaraah nata latsa baby nokia dinta. Sai da suka isa gidah zata fita ya dakatar da ita, "Dauki naki ne....?" "Wait... What? Why? " "Cuz you are my property!" Ya Bata amsa kasan makoshi. "Banji ba" "Saboda ke mallaki na ce!!!!" I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ 2/8/22, 08:22 - Buhainat: Zafafa biyar na ku i ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna ha aki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika sa a mana al awari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._* *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb _________________________ Ya fada a can 'kasan zuciya yana yamutsa fuskar sa. Yanayin yadda ya yamutsa fuskar tasa ne hakan yasa Zaraah sake matse tata fuskar. Ta wulkita idanu ta dankara masa harara. Hade da kokarin bude murfin motar cikin fushi da takaicin sa. Ledar ya dora mata akan cinya. Tare da sake rufe murfin motar . "Budemun. "Ta fada a hankali. Hade da kaudar da fuskar ta zuwa kan murfin motar. Don sam batason kallon fuskar Maheer. Domin tamkar sudeis yayi kaki ya tofar. Saboda tsananin kamar da suke. "Tsiwar ki ta bude miki" Ya fada cikin muryar umarni . Ya kuma bata rai don karta dauka da wasa yake. unkuni ta fara yi ahankali . Maheer ya saki siririn tsaki, auka ledan ki fita. Kuma this should be the very last time da zaki tsallake dokata kinji na gaya miki. Ya karasa ransa a matukar bace . Cikin zuciyar sa na masa zugi. oh ina ruwanka da rayuwata. i kike gayawa haka? ? Yana kokarin jefa mata wani kallo mai dauke da kalamai. i dai ka budemun na fita Ta karasa fada tamkar zatayi kuka. . Hade da sake kiciniyar bude murfin motar. Hannun sa d ya ya dora akan nata da zummar hanata kokarin fitar da take. Wani Irin electric shock ne ya ziyarce ilahirin jikin su da kwakwalen su. Da sauri ya janye itama ta dauke nata hannun. auki kayan ki fita . Kuma su zaki dinga amfani dasu wajen fita unguwa da sauran su. Kar ki kuskura ki kawo wani abun a zuciar ki. Amanar da dan uwana ya