← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 55

Sashe 34

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda Zaraah ta futa wucewa gida tayi kai tsaye kamar yadda Daada ta umarceta. Jikinta gaba daya yayi sanyi. Jinta take tamkar mara lapia. Saboda tsananin yadda gabanta suka Yi lakwas. Bugun zuciyarta ya tsananta. Hailala tashiga Yi ahankali har takarasa shiga gidah . Kai tsaye ta wuce sashen da yake matsayin nasu. Ta duba dakin Yan biyu ta dakko musu kaya kala 'dad'dai. Sam bata 'bata lokaci ba ta kullo sashen nasu ta tafi titi kai tsaye. Motar da take amatsayin ta sudies ce ta yanko kwanar titin da zai sadaka da gidan Capt muhd. Wanda Zaraah ke a tsaye a bakinsa tana jiran wucewar dan sahu. Sai da gabanta ya fadi lokacin da motar ta tsaya a daidai saitinta. Maheer ne ya tsaida motar hango ta da yayi. Daga makabarta yake ta airport road. An rigada an hade mamatan waje daya an sallace su an kuma binne su. Sakamakon babbakewa da sukayi. Ba ta yadda zaa gane wannan shine wa ne. Kifa kansa yayi akan sitiyarin motar, sautin muryar sudeis na masa gezo a kwakwalwar kansa . Ya matse hawayen dake sharara a idanun sa. Ya sake daga kansa ya sauke a fuskar Zaraah dake tsaye a gaban motar tana danna yar wayarta Nokia mai fitila. Sake gaba yayi da motar daidai saitin ta ya tsaya yana mai zuge glass dinta. Ta daga kai ta dora akan motar. Caraf idanun su suka hadu. Sunyi wani kallo na yan wasu dak'ik'ai kafin zaraahn tayi azamar dauke nata tana jan siririn tsaki. Maheer ya samu kansa da jin haushin tsakin data yi masa. Wani 'kasan na zuciyar sa ya saisaita masa ita. Kafin ya dan mayar da kansa gefe. Ya zaro gilashin sa dake cikin aljihu ya zura a fuskar sa. Saboda wani kuka dayaso kufce masa. A duk sanda ya daga idanu ya dora akanta. Sudies kawai yake hangowa da kalaman sa na karshe akan amanar Zaraah . Fucewa yayi bayan ya bude murfin motar. Ya zagaya ya bude mata kofar baya. "Shiga na kai ki inda zaki je." Ya fada muryarsa na rawa. Saboda ya baro Dadaa da Capt a asibiti Kuma Dadaan ce ta sheda masa yadda sukayi da zaraahn. "Bazan shiga ba.." Ransa matuka gaya ya sosu amman saboda amanar ta da Sudeis ya bashi hakan yasa ya sake daurewa ya rike murfin motar, "Dan Allah kiyi hakuri ki shiga... Zaraah" Ya karasa hadi da jan sunan nata cikin wani salo mai taken rarrashi. Girman Allah daya ambata. Hakan yasa Zaraah shigewa cikin motar bayan ta aika masa da sak'on murguda baki. Ya shige motar ya tada ita. Sai da yahau kan titi tukun sannan ya dan rage sautin karatun dake tashi acikin motar . "Ina zan Kai ki?" "Makarantar su yan biyu " Bai ce komai ba ya wuce kansa tsaye. Dakyar yake ta kokarin danne damuwar dake cikin zuciyar sa na rashin dan uwan sa sudeis . Yana karasa tsayawa a kofar makarantar Zaraah ta bude ta fita. Shiga ciki tayi tadan jima saboda sai data tsaya suka sauya kayan su zuwa na gidah. Suna fitowa taga Yana nan inda ya faka bai tafi ba. "Sanabe" Ta furta tana yamutsa fuska. "Adda manga ba motar zamu shiga ba?" Suka hada baki wajen tambayar ta. Sanin motar ta sudeis ce. Bata amsa su ba. Illa rike hannun su da tayi. Raheelah a hagu Na'eelah a dama. Ita Kuma tana tsakiyar su. Suka cigaba da tafiya zuwa titi. Yayi reverse da motar ya shiga binsu a baya. Ya Sha gaban su ya tsaya. "Ku shigo na ajiye ku" Zatayi magana kenan yai saurin katseta, "Dan Allah ku shiga." Sarai ya gano lagwanta. Don haka bata sake musu ba. Suka shiga cikin motar. Su a baya, Na'eelah a gaba. "Ina zamu je?" "Rimin kebe." Danna map yayi dake jikin screen din motar ya rubuta address din. Take map tashiga nuna masa hanya har suka karasa rimin keben. "Karfe nawa Zan dawo daukar ku?" Ya tanbayeta a hankali Yana sauke zuciya. "Dare." Ya juya kan motar ya dauki hanyar asibitin da Dadaa take. Ya dako su Dadaan suka koma gidah. Nan gidah ya shiga tunbatsa da mutane yan zaman makokin sudeis da kuma barkar baby sudeis da aka haifa. ********. Suna karasa shjga layin su da yayi gaje gaje da kwata. Suka fara jiyo ihun sautin Ardoo. Yanata magiya. "Wayyo Allah na. Dan girman Allah Rumalle kiyi hakuri. Ki yafemun. Qur'anin ubangiji mak'oshi na zai dagargaje. Da kwankwaso na. Na tuba Rumalle." Wannan Ife ifen Ardoo ketayi tundaga farkon layin ake jiyo shi. Suka karasa shiga ciki yayinda jimmamman ke kofar dakinta tanawa Asabebiya kktso. Atuwa kuwa na tsaye tanata dadarawa bakinta jambakin gyatuma radau. Sai kallon fuskarta take a mudubin dake hannunta na fashashshiyar hoda . Ashe Ardo lefi yayiwa Rumalle. Dan kwua ya kirb'a Usmanu da duka akan ya siyar masa rediyon sa. Ashe Rumalle na rike da abun a zuciyarta .shine ta zaune Ardo akan gado tahau ruwan jikinsa. Hadi da shake masa wuyan sa. "Ah wargajalle mutanen gayu. Yau June agarin?" Cewar Atuwa dake kokarin yafa mayafinta. Gayshe su duka suka yi. Yayinda Atuwa ta sake 'daga katuwar muryarta ta saki gud'a tare da cewa, " A hayye landantsan. Allah mai alheri. Ku samu waje ku zauna. Bana bappan naku ya dakko ruwan dafa kansa. Iya karbar fanushiman (purnishment) wajen Rumallen sa." Ta karasa hade da yaye labulan dakin Rumalle. Sai ga Ardo ya hada gumi sharkaf Yana kakarin mutuwa. Ganin su ne yasa Rumalle sauka daga Kansa. "Tashi ka tafi. Sun fanshe Ka. Gobe ka 'kara maimaitawa. " Atuwa tasheke da dariya tana duban Ardo daya di'iba aguje yayi waje. Dariya ta shiga yi sai datayi mai isarta kafin tace, "Jammu wannan karon bata baku'dan kayan dadin nan ba?" "Nama manta, Dadaa ta haihu dazu ba jimawa. An samu namiji." Jimmamman ta saki kifiya tana mikewa tsaye. Suka hada baki wajen tambayar su, "Namiji?" Ai atuwa bata samu bakin magana ba, Sai guda data sake saki tayi waje tana nanata, "Dole ne Ardo yaji Wannan dadd'adan zance. "Dan qundun uba, Kai Kai a hayye landantsan, shagali budiri wan dinner. Wabillahil lazi har gada zanje na sanar masa. " I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p *WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* ABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . ___________ 2/4/22, 07:42 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *SO DA ZUCIYA* *NANA HAFSATU* *29* ***Atuwa na ta zambad'a sauri a hanya tana kalle kallen lungu da sak'o wajen nemo Ardo. Don shelanta masa haihuwar Jammu . Can gefen gada ta hango shi. Ya tsayar da zabbau me awara suna tad'i. Ta sauke bokitin awarar a tsakiyar su. Shi kuma Ardoo ya choge daga gefe yana zuba mata zance. Yayin da zabbau ke rike da gammon dora awarar a hannu tana jujjuya shi. Sun lula sosai a fagen zancen da suke. Sai ga Atuwa ta isa wajen su. Ta duk'a ta dau awara guda da daya ta cusa a baka. "Ina kudin awarar da kikaci?" Cewar zabbau. Hade da mikawa Atuwa hannunta alamar ta chanke mata kudinta. "Zabbau kenan. Ko Adaman shehulle (mahaifiyar zabbaun) na goya ta a baya bake ba." "To ni meye ruwana aciki? Kawai kiban goma ta. Gaskia." "Uban iyali. Malam Ardoo saurayin kawayen 'yayan sa. An gayda Ardo uban iyali. Nazo maka da daddadan labari. Amman kafin sannan biya mun goman awara dana ci ." Harara Ardo ya dankara mata kafin ya zaro nera goma daga cikin nera 80 din dake aljihun sa ya mikawa Zabbau me awara. Atuwa taja guda tasaki hade da shewa. " 'karuwa muka samu Ardodo." "Ta mai fa? " Ardo ya tambayi Atuwa cikin kade kunnuwansa don jin daddadan labarin karuwar da suka samu. "Jammu ce ta haihu." "Jammu kuma? To meye garin gami na da ita?" "Kayya bakacin ribar zance Ardo. Sai gani nayi abun atayaka murna ne tunda anyi zaman mutinci da kuma yalwar arzikin 'ya'ya a tsakanin ku. Gashi kuma garin ku 'daya" "Ina sauraron ki. Wannan rawar kan da kike. Ko sunan ki aka sawa jaririyar ne?" "Ka ji ka da wata magana. Na gayan ka abunda ta haife ne?" "Yo ai nasan ba zai wuce hakan ba " "Toh sanin ka bai fadi daidai ba " "Toh uwar yan kanzagi. Ya akai?" "Kai dai bari Ardodo. Sa goshinka bisa kasa ka fara yiwa Allah godia." Ardo ya washe baki. Take zuciar sa ta hasaso masa kilan auren Dadaa ne ya mutu takeson jimmamman din ta roka mata shi. Ya mayar da ita dakinta. Take ya goho ya duka yayi sujjada bayan ya dubi gabas. Wandonsa har sab'ulewa yayi. Ya janyo shi ya mayar come da jin dadi . Ya girgiza kai cike da jin dadi yace da Atuwa. "Ai shika da nayi ba uku na shika ba. Idan ma ukun nayi ai tayi auren kisan wuta ko?Yo dama su Usmanu ne a dakin, Sai su futa daga ciki. Kice mata tadawo dakinta da zarar tagama id.." Bai karasa fada ba. Jimmamman tasaki katuwar dariya tana jujjuya kai. "Angon Rumalle mijin jimmamman. Na Atuwa bada kanka asare. Kaga uban iyali baban su
Chapter 34 · 0% Book details