← Book details So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 55

Sashe 5

So Da Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . 1/31/22, 18:28 - Buhainat: *_SO DA ZUCIYA_* *_NA_* *_NANA HAFSATU_* *_ZAFAFA 5 (2022)_* *_FREE PG:4_* _ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY _MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_ _KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR NI MA GIRMA_ _WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI _GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN https://youtube.com/c/sudaiskura _Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._ _Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan ?. ?. ?. ***Dadaa dake cikin dakin ta ita da yara, tana jiyo hayaniyar masu kawo amarya tai saurin kashe fitilar shekarau ya gaza din da ta kunna musu dan suga haske. Tayi haka ne dan mutane suyi zaton sunyi bacci dan gudun kar ayi mata habaici da yawa. Gwaggo Lami ce ta shigo gidan da gud r ayyirrrrrrriri tana cewa. marya ta shigo gidan masoyinta, Jimmamman tako kafarki da hannun dama saboda kore asirin kishiyoyi. Gabaki daya mutanan da suka yo rakiya suka kwashe da dariya tare da hada baki wajan furta. hayye!! Nanayeeee casss...! Mama Atuwa na daki sai faman kwafa take, ji take kamar ta harbe daga su har amaryar saboda kishin da yake damunta. Kai tsaye kuwa suka nufi dakin ta zasu kai amarya a hada su tare da yi musu nasiha. Sai da suka fara shiga ta mike a zabure tana wani irin nishi tace dasu tana nuna su da yatsa manuni. radun Allah duk wace ta kuskura ta shigo sai na balla mata kafar baya bakaken munafukai. Daga ku har Ardon a karkashin kafata kuke babu uban da nake tsoro billahillazi. eeee caras-cas! Ardo dai ya yi sabon zubi, kuma dole yadda ya dama haka za'a shanye a gidansa. ? Cewar wata kanwar Jimmamman daga can bayan Gwaggo Lami. ikin banza aikin wofi BZ din? Har bazawara tana da wani daraja da kima a gurin miji? Mune nan aka aure mu a yan mata yan shila ba wai ragowar wani ba. Mama Atuwa tai maganar cikin cusa musu haushi. Sai dai babu wanda yaji din sai ma wata gud da suka sake yi kamar sun zo gidan gala. aba ke kuwa Hafsatuwa, wannan auren fa ba haramun bane. Annabi Muhammad S.A.W ya auri bazawara, dan me zaki dinga aibata makamancinsa? Kiyi istigifari dan kinyi sabo babba. Gwaggo Lami ta fada tana kamo hannun Jimmamman suka juya dan shiga wajan Dadaa, wacce tasa duk suka kwanta tare da yin kamar sunyi bacci. Duhun da suka gani ne yasa su haska fitilun dake hannuwansu, nan suka tarar da Dadaa kwance tayi ai-dai tamkar mai baccin gaske. Gwaggo tace a rabu dasu a kai amarya dakinta. Jimmamman na yafe da mayafi cikin ranta tana ta sak yadda zata zauna a gidan, musamman zama da Atuwa dan taga itama ba wai mutunci gare ta ba. Sai da suka gama habaice-habaicen su kafin su tattara kowa ya kama gabansa, aka bar amarya ita kadai a daki tana jiran shigowar angonta. ?. Sai da kafa ta dauke ya rage daga yan dakin Dadaa sai dakin Mama Atuwa da kuma amarya. Cikin daga murya suka ji malam Ardo ya yi sallama kai daga jin muryarsa kasan cewar yana cikin farin ciki kamar wani saurayin ango. Mama Atuwa tai saurin fitowa daga daki har tana take kafar Farilatu kuma ko a jikinta bare ta bata hakuri saboda tsabar masifa tana cinta. Kicibus suka yi dashi zai shiga dakin jimmamman hannunsa rike da wata karamar kula da leda baka sai murmushi yake yana lasar lebe. Ganin Atuwa gabansa yasa shi hade rai tamkar be taba dariya ba a rayuwarsa dan yasan fitowa tayi dan tai masa tijara. oh malam kasan dai yanzu yara sun dawo gidan uban su ko? ai kuma aka yi me dan sun dawo? Ai ni ban ma san basa gidan ba sai da kika fada dazu Haushi da bakin ciki ya sake cika Atuwa, ta buga cinya tare da sake matsawa kusa dashi dan ta gano meke cikin kular. Kamshin tafarnuwa da kanumfari ne ke ta tashi kadan-kadan saboda an kulleta sosai. Malam Ardo ya kuma rike kular yadda ko kwata tazo yi ba zata iya ba duk masifarta. Atuwa ta kama kugu da yake akwai hasken farin wata ta ciki ana ganin komai, tace dashi. h! Daman ya za ai kasan suna nan ko basu nan? tunda kwan su kawai kake ajiyewa baka san yadda muke kyankyashe su ba bare kasan yadda muke kiwon su. Babu abinda ka sani malam sai aure, da anyi magana kace sunnah kake rayawa. Toh wallahi yanzu bazan dauki rainin hankali ba. Menene wannan kazo dashi bayan mu ka hada mu da kwayoyin awara.? na ruwanki dako ma menene? Hafsatuwa bana son sa ido, ki fita daga cikin sabgogina idan ba haka ba wallahi tallahi zan saba miki. ai tafi can, ni fitowar da nayi shine. Kafin ka shiga gurin waccan BZ din ka fara bani kudin karin kumallon gobe, nasan kana da kudi tunda gashi har aure ka sake jajibowa mutane muna cikin rashin abinci. Wannan dubu goma ta sake jajibo mana bala bayan ko shekara ba rufe ba na shikar Zabba n mai koko da kayi. ani dasu, Ina ruwan ki kuma? matsa ki bani guri." ikuwa baka isa ba sai ka bani abin karin kumallon safe, ai nauyin a kanka yake bani ba. Malam Ardo ya kalleta ya kalli dakin amarya jimmamman, ya kagara ya shiga ciki amman Atuwa ta kasa ta tsare. Ya daddage tare da sa gefen hannunsa ya bangajeta da sauri ya shige dakin jimmamman yana faman baza yar shararsa. aka fito ka same ni wallahi, ba dai a gidan zaka kwana ba? Banyi niyar shigowa dakin ba dan ban sani ba ko sunyi barbade a bakin kofar. Amman Allah ya kaimu safiya duk masifarka sai ka bani abin da zamu ci, banda mugunta ba zaka tsaya ka gina mu ba, sai dai daka samu kudi kace aure sai kace wani jaki. Malam Ardo yana jin ta amman da yake ba ta ita yake yi ba duk maganganunta babu wanda ya d'ad'arasa a kasa, burinsa kawai ya farantawa amarya Jimmamman dake zaune tana ta murmushi cikin mayafi, dadi kawai takeji miji na sonta. Ardo ya ajiye kular a gaban Jimmaman da ledar ya zauna a kusa da ita baki a wangale kamar shine farkon auransa. marya ta. ? Ya fada kamar zai shiga jikinta. a'am na Jimmamman. ? Ta bashi amsa babu ko kunyar nan. an bude min fuskar mana, ai yanzu babu maganar boye wani abu ga junan mu. ? Kamar yana kallanta, ta saki fari da ido ta cikin mayafin tare da cewa. ai ka siya baki. ahahaha amarya ta kenan, yo maganar siyan baki ai ta kare. Maza bude fuskarki farfesu ne nasa aka yi mana na kaza. Yana magana yana bude kular, shi kansa ya kagu ta faraci yawunsa gaba daya a tsinke yake. Jimmamman ta bude mayafi dai-dai lokacin da Ardo ya gama bude kular kamshi ya bud'ad'e cikin dakin. Tai saurin janye kular daga gabansa tana wani yauki kamar wata karuwa tace dashi. dan har ta siyan baki ce ai babu kai zamu ci. Wannan tawa ce ni kadai na Jimmamman. Ardo ya ware ido tare da tunawa da yayi bashi yasa aka bashi kazar guda daya ta hausa, ya kuma sa aka dafo masa gashi ta dan kaciya ce. Amma ya zai yi tunda amarya tace ba zai ci ba. Ya goge hannunsa yana ta sakin fara'a yace mata. n bar miki kiyi yadda kike so da ita, ai ke amarya ce duk yadda kika ce haka za'a yi. Yana magana yana janyo leda mai dauke da lemon kwalba Pepsi guda daya tal. Ya fara laluben mukullinsa mai dauke da keyholder na bude murfin kwalba. Nan ma da sauri Jimmamman ta karbe tare da lakuce masa hanci tana faman murmushi tace. aba na Jimmamman wai duk bani ka kawowa ba ne? u naki ne mana amarya ta. ? Ardo ya fada cikin gigita ganin ta kwace komai zata handame. oh ka bar min kayana ba yanzu zan ci ba sai gobe. Ardo ya jinjina kai tare da shafa hannu kamar me goga man shafawa. Yana ji yana gani ta tura karkashin gadonta daga nan ta kwanta. Ganin tana neman hanashi raya daren yasa shi saurin bin bayanta suka kwanta. Bata hana shi ba domin ita kanta ba ta da juriyar da zata hanashi dan tayi mu'amala da kayan mata daban-daban kafin ta shigo gidan. Dadaa kuwa bata rintsa ba saboda tasan wata gwagwarmayar Ardo ya sake jajibo musu, takan ce shi kuma kaddarasa ta auri saki ce. Duk da yasha gaya musu cewa yana yin aure ne saboda ya mori kuruciyarsa ya kuma samu yalwatar a maza tunda bashi da a mazan sai Modibbo kad i ba sauran maza da zasu gajeshi ko su taimaka masa nan gaba. Yaransa duk mata ne da zasu zame masa wahala aganin sa, ya gama rainan su da kulawa dasu a karshe wani katon yazo ya aure su shikenan bashi zai more su ba. A cewar sa mace wahalace shi kuma ba zai wahalar da kansa ba wajan kiwata su a karshe su tafi gidan wasu babu ko na buhun shinkafa bare kudin cefane. Fitilar da ta kashe shigowar kawo amarya, ita ta kunna. Abin da ya bata mamaki shine ganin Zaraah a zaune ta zabga uban tagumi ga alama kuma tunani ta fada dan ko motsawa ba ta yi daga inda take. araah! Zaraah!! Ke Zaraah...!!! ikin firgita da zabura Zaraah ta dago tare da cewa. a'am Dadaa aba tunanin me kike yi haka?
Chapter 5 · 0% Book details