← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 50

Sashe 50

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ashe ni Nana nafi Sardaun gata? Sardauna dai ba shi da ala™a da wannan gidan? Ya zaiyi idan ya ji wannan magana? Kai innullahi abubuwa sun caSewa Sardauna, sun juye masa gaba Waya.

Ji na yi an buWe ™ofa an fito, Turaki idonsa sun yi jawur. Kana ganinsa kasan ya sha kuka, ya Waga kai ya kalle ni.

Nana, kinji?

Na gyaWa kai sama, ya girgiza min kai ya ce.

Nana sirri dan Allah, ya zama da gani sai ke.

Ban iya ce mai komai ba na mi™e na shiga ciki, ina zuwa na ajiye mata abincin na fito, a lokacin yana zaune a falon.

Habibty.

Na Wago na kalleshi, ya ce.

Ki yi ha™uri da abinda na yi miki, raina ne ya sosu.

Bakomai Habiby, nima ina ™ara baka ha™uri akan abinda na yi.

Daidai lokacin kuma Hajiya Falmata da iyalanta suka shigo, na matsa musu hanya suka shige, har sun yi gaba Alisha ta dawo ta kallemu sannn ta ce.

Wai me kuke nufi? Kulluk aganku ku biyu ina Islahan? Ko dubiyar ma ka hanata ne, sabida ka Sata ta a cikin yan uwa?

Hajiya Falmata da ta dawo ita ma ta ce.

Na yi al™warin bazan ™ara zuwa gidanka ba, amma tabbaa kaje ka kawo min yata yanzu.

Yar taku tana wajena ne? Ku tambayeta man&

Na yi sauri na rufe masa baki, jin yana shirin Sallo ruwa, wanu kallo na yi masa wamda zai sa shi ya tuna Islaha bata nan, tana zaune a gidan Sisiter Seemah a sirrance, amma ina Alisha ta ce.

Bangane ba, kana nufin Islaha ba ta gidanka? To tana ina? Lallaima.

Ke cika mishi baki, shashasha marar tarbiya, zai yi magana kin wami rufe masa baki, wallahi idan wani abu ya sami Wiyata sai na kai ki prison.

Turaki ya ™wace bakinsa, a fusace ya ce.

Ki kaita prison? Ashe kuwa za aje prison da yawa, yar ki tana nan da tarin abun kunyar da ta aikata, kuje ku tambayi Sister Seemah, yarinyar ku tana wajensa, kuma ku sani abinda ke jikinta, bazan taSa amsa ba.

Bangane ba, tana wajen Seemah, kan babbar uba.

Kuje ku nemeta a wajenta, kar wanda ya ™ara haWani da ita, nasake ta tuntuni.

Yana gama faWin haka ya ja hannu muka fice, muna fita na ce.

Me ya sa ka yi haka? Ba ance za a rufa asirin komai ba, me ya sa ka watsa?

Sai da muka shiga mota ya ce.

Habibty, Sardauna fa ba Wan familynmu ba ne, amma yazo sai ™o™arin raba mana kai yake, duk wata fitina shi yake tado da ita, kanmu gaba Waya ya rabu duk a sanadin mutum Waya, yanzu wannan dole aiki na ne na haWa kanmu waje, nine fa jika babba namiji, wannan nauyi na ne, ha™™ine a kaina, bazan bari wani daga waje yazo ya tarwatsa mu ba.

Na kalli Turaki kallo na tsanaki, yanda idonsa ya yi ja, yana fitar da ™walla ya yi matu™ar bani tausayi, tabbas a yanzu aikine akn Turaki ya haWa kan yan uwansu waje guda, amma ba sai ya biyo ta haka ba, na ja numfashi sannan na ce.

Habiby, tabbas wannan aikin ka ne, kuma sai ka dage akai, ka yi duk wani ™o™ari da zaka iya akan hakan, amma kuma komai ta masalaha ake bi, kowanne abu kafin a aikata shi, sai anyi masa dogon zama, dogon nazari. An nazarce mai zai je ya dawo, sharri ne ko alheri, idan duka ne wanne yafi sharri yafi yawa ko alheri? Duk yakamata ayi masa wannan nazarin, ni Nana na yi al™warin zan tsaya da kai, zan kasance mai taimakonka ta kowanne fanni, komai tsanani komai wuya.

Ya sakar min wani murmushi, ya kama hannu ya ce.

Na gode Habibty, na gode da shawarwarinki, ma gode da. Kasancewa a tare da ni.

Babu godiya a tsakanin mu habiby, ha™™i ne akan kowacce mace ta gari ta kasance a tare da mijinta komai tsanani komai wuya, yin haka shine zai baki riba a duniya da kuma lahira.

Ya sake wani murmushin ya jawo ni jikinsa, daidai lokacin wayarsa ta fara ringing, ya Wauka yana faWin.

Sister Seemha.

Na gyaWa masa kai, ya Waga kiran tare da sa wayar a buWaWWiyar speaker.

Turaki kana ina? Me ka cewa waWan can mutanen?

Ina asibiti, yanzu zamu tafi gida.

To ka jirani yanzu zan zo nan, ayi komai ya ™are.

A a kar ayi asibiti, gwanda a nemi wani wajen da bazaiyu akan wani daban ba muje muna Waga hankalin kakarmu a asibiti, har wani abu yasake samunta.

To kazo gidanmu, nima zamu wuce can, suma zance su je can, har da shi Sardaunan.

Tom.

Ya faWa tare da kashe wayar, yaja motar muka nufi hanyar, ni dai Allah Ya ganu banso ayi komai a haka ba, abi ta masalaha, yanzu me Sardauna zai ji da shi, cikin shege ko kuma rashin asali, ko da yake ba rashin asali ba, ya zai ji idan yagane shi ba Wan asalin gidan da yake ta™ama da arzi™insu ba ne, ya zaiji idan yaji bashi da ko sile a ciki?

Too jama a, munzo iyakar littafi na biyu, ga dai Sardauna ba Wan familyn Ta ambo ba ne, ga cikin da ya yi wa Islaha, shine familyn Ta ambo zasu ci gaba da ri™e Sardauna? Ko zasu sallameshi ni? Wai Nana zata samu haihuwa kuwa?

Mu haWu a littafi na Uku da zai fara zuwa ranar 20 ga wata june a arewapen, 22 a whatsapp.

Legendspen

08129553971
Chapter 50 · 0% Book details