← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 50

Sashe 29

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa ta shuWa abubuwa da dama sunja, a yanzu mun shiga shekara ™arshe a makaranta, kuma zango na ™arshe gaba Waya bai fi sati bitu ya rage mana, mu fara jarabawar ™arshe, a yanzu na saba da makaranta, makaranta ta sabani, yan Wakinmu mun fara gaisawa da su, mun saba dan wani lokacin mu kan zauna a falo mu taSa hira, Turaki dai duk wannan sati biyun sai ya zo, bai tama gajiyawa ba, matarsa kam ya ce yau da gobe ta sa ta fara yi masa magana, amma sama sama, ko girki mai aiki ce ke yi. Haka zan ta lallaSa shi da nuna masa ya ci gaba da ha™uri da ita, ya matsa na yi nagama karatu, duk da bai ce min yana so na gama karatu ya aureni ba, amma yana cemin ya matso na kammala karatun nan. Yaya Ridwan ma ya sami matar aure, an sa mai rana. Ra is ma yan watanni kaWan da suka wuce ya kammala na shi karatun, a yanzu haka ma service yake anan kanon, Yaya Radiya ta haihu a sabon auren nan da ta yi, ta haifi namiji.

Sardauna dai duk tsahon lokaci nan ban sake sa shi a ido ba, gaba Waya ma cire shi a rayuwata na sake mantawa da shi kamar yadda na yi a baya. Har mantawa ma nake da shi a rayuwata. A yanzu an san fuskaata a makarantar mu daga Walibai har malamai sabida yanda nake dagewa a ajinmu, ina cikin Walibai guda goma masu haza™a a cikin ajin. Sabida yanda na cire komai a raina na durfafi karatu abuna. Mussaman yanzu da jarrabawarmu ta ™arato, Turaki ma ya ce ba zai sake zuwa ba sai gradution Wina, su Yaya Radiya sa kowa ma sun ce sai lokacin graduation Wina, dake a wannan hutun na samu na kwana biyu a gida.

Cikin ikon Allah, mu ka fara jarabawarmu ta ™arshe, a cikin sati biyu muka kammala ta gaba Waya, ranar kammalawarmu yan gidanmu duk sun zo har da Hajiya ma, na yi farin ciki na yi kuka sosai da sosai, a lokacin da aka bani certificate Wina, cikin muryar kuka nake magana.

Alhaji& Alhaji dama ace kana raye yau, kaga yar autarka ta kammala abinda kake so, Alhaji na yi karatun boko da kake so, Alhaji a yau na zama mai ri™e ta kwalin degree.

Babu wanda bai yi kuka ba, mussaman waWan da suka san wannan shine babban burin mahaifina a kaina, tabbas Turaki ya yi min abinda ba zan taSa mantawa dashi ba, ya ri™e hannu ya kai ni ga matakin nasara tabbas ya cancani kowace irin sadaukarwa daga gareni. Haka aka ga ma taro a makaranta, daga nan duka muka wucw gidansu Anty Adiza, su Hajiya ba suzo da shirin Kwana ba, amma irin karamci na yan gidansu Anty Adiza sai da suka sa su kwana, Yaya Ridwan da Ra is hotel suka kama, daman shi Ra is yana nan yana service Winsa.

Washe gari muka shirya muka kama hanyar dutse, a raina na yi ban kwana da kano, nasan babu lallai na sake dawowa, ko da zan dawo bazan sake irin wannan zaman ba kusan shekara uku. Amma tabbas na ji daWin zaman kano fiye da yanda duk zan kwatanta.

A haka muka ™araso dutse, har gida Turaki ya kawo mu, ana cikin shiga da kaya ya ce da ni.

Nana, ina so mu yi magana.

To ka shigo ciki mana.

Ya girgiza kai, sannan ya ce.

Daga wajen nan ma, zan wuce gidane.

Dawowa na yi na jingina da jigin motar, ya kalleni ido cikin ido sannan ya ce.

Nana, a rayuwata na kasance mutun mai wani irin tsari, Allah da ya halliceni ya sanya min soyayyar yarinyar da bansan da ita ba, kowa da yake tare dani yasan da wannan soyayyar, Nana.

Na Wago na kalleshi.

A lokacin da naganki a tare da sardauna a matsayin miji da mata, a kullum addu a ta ita ce, Allah Ya bani mace mai irin yanayi, Wabi a, kamanni, da halaiyarki, hakan shi ya sani nazo gidanku ko Allah zai sa na yi sa a na sami ™anwarki, sai naga ashe kece auta. Nana duk yadda zanyi na Wauke ido na daga kanki, amma Nana na kasa, sabida haka na yi nesa da gidan. A lokacin da nasami labari a wajensu Yaya Radiya kince Sardauna yana nan, a lokacin ban kawo komai a raina ba, sai da na ga halin da kike ciki, Nana na sha wahala, na yi fatan Allah Ya cire miki ciwon nan, a surutan ki na fuskancin komai da Sardauna ya yi miki, Nana na yi al™wari da burika akanki, kuma Nana na fara cikawa, Nana dan Allah ina son ki aure ni Nana, ina sonki, ina yi miki so mai girma, so na gaskiyya da babu algus a ciki, Nana so guda Waya da ba shi da sirki.

Na yi shiru ina sauraren Turaki, tabbas nima nasan ina son Turaki, son da ya goge Sardauna a rayuwata, sai dai ina tsoron sharrin Sardauna, ina tsoron makircin Sardauna.

Nana ki je gida, ki yi tunani.

Tom.

Na faWa tare da shiga gida, duka yan gidanmu suna Waki banda Hajiya da take tsakar gida.

Nana lafiya?

Ra is ya tambaya, sai da na zauna na ce.

Ra is Turaki ne ya ce yana son aure na.

Kai Alhamdulillah Nana na yi miki murna.

Yaya Rumaisa ta faWa, Yaya Radiya ma ta ce.

Daman nasani, Nana Allah Ya sanya alheri.

Na yi shiru, kamar kar na faWa musu komai sai sai kuma suna bu™atar sani domin bani shawara.

Sardauna ya sake zuwa hostel Winmu. Suka juyo su kalleni, na fara basu labari tun daga farko har ™arshe.

lon ya yi shiru, kowa yana saurarena har na kai aya, ina direwa Yaya Rumaisa ta cafe da cewa.

Nifa shi ya sa bana son shiga al amuran Nana wallahi, yarinyar nan gaba Waya bata da lissafi ko kaWan, idan ba ki sake aure ba dauwama zaki yi a haka, da ba™in ciki da wancan mistiyacin ta dasa miki?

Ni bama wannan ba, Sardauna da kansa ya ce ba ke yake so ba, ™uruciyarki yake so kuma ya samu, ya ce yana matu™ar kishinki fiye da kowace halitta a duniya, kuma wannan gaskiyya ne domin ko da mukaje Wauko ki a gida, ina ganin kallon da yake yi wa Ridwan akan ya taSaki, kallo ne me cike da kishi, haka ranar da mukaje kwashe kayanki, kinsan dalilin da yasa ya daki wancan mai motar?

Na girgiza kai alamar bansaniba, Yaya Radiya ta gyara zama sannan ta ce.

Sabida da muka zo shiga jikinki ya gogi nasa, ku duka baku sani ba, a lokacin ina ganin yadda Sardauna ya runtse ido, hakan ya nuna Sardauna yaba matu™ar kishinki fiye da yadda kike tunani, to kina tunanin idan ya ji kinyi aure ya zaiyi?

Ba™in ciki ne zai kashe mitsiyaci. Ra is dake tsaye ya faWa, sannan ya ce.

Ta wani Sangaren ma, kinsan Sardauna ya tsani Yaya Turaki, a yanda kika faWa mana ya ce ya tsani ya ga ya mallaki abu Yaya Turaki ya mallaki mai kama da shi, ki tuna gida Waya suke da Yaya Turaki, ki hango tashin hankali da rayuwarshi zata shiga idan ya buWe ido ya ganki a matsayin matar Yaya Turaki Nana.

Duk wata tsoratarwarsa ta banza ce Nana, idan kina son Turaki to ki so shi, idan zaki iya aurensa ki aure shi Nana.

Yaya Ridwan ya faWa, na kalleshi sannan na ce.

Yaya kai ya ka gani, a lokacin Sardauna kaga abinda bangani ba.

Nana a ta Turaki mutumin arzi™i ne, amma Sardauna sheWani ne, sheWan Win da zai iya wargaza muku zaman lafiya da soyayyarku.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na ashirin da huWu.

To kawai dai ta amince ma sa kenan?

Ra is ya faWa, Yaya Rumaisa ta ce.

Bawai dan abun hannu ba, ko yana kyautatawa gidan nan ba, kawai duba da halaiyya da kamalarsa,ni dai ina ganin Nana ki amince ma sa.

Ra is ma ya ce.

Nima dai.

Kai ai ko kowa ce bai amince ba, kai kam zaka amince, kai da uban Wakin ka.

Yaya Radiya ta faWa tana dariya, sannan ta ™ara cewa.

Nima dai haka Nana, ga Ridwan ma, saura kuma Hajiya.

Tom, Allah Ya tabbatar da alheri.

Kowa ya amsa da amin, haka muka yini a gida, sai dare sannan suka fara tafiya, ina son sanarwar da Hajiya kuma ina jin nauyi, ashe Wan iya ya fesa ma ta, sai da kowa ya tafi sannan ta shigo Wakin.

Nana ta shi mu yi magana.

Ba musu na tashi zaune, na zuba mata idanu.

Ra is ya faWan komai da kuma shawarar da suka baki, tabbas Nana Abubakar ya cika yaron ™warai, bani da wani abu na daban da zan faWa miki sabida yan uwanki sun ruga ni, sai dai na ce Allah Ya sanya muku alheri, ku kuma Allah ya haWa kawunanku.

Na amsa da amin, sannan na koma na kwanta, washe gari da safe na dinga saka ran kiran Turaki amma na ji shiru, har zuwa yamma shiru. Daman Turaki akwai lafiyar bawa mutun space, zai baka ishashen lokacin da zaka yi tunani ba tare da ya takure ka ba. Har zuwa dare bai kira ba kuma bai zo ba, hakan yasa na yanke shawarar kiran da kai na kawai.

Bayan na yi shirin bacci na, na hau kan gado na kira shi a waya, bugu Waya kuwa ya Wauka, ya yi shiru nima na yi shiru, kusan mintuna biyar sannan ya ce.

Ba zaki iya magana ba ne?

Aikuwa kamar jira nake na fara kuka, kukan da ya Waga masa hankali ya fara faWin.

Nana lafiya? Me ya faru ne?

Cikin kukan na ce.

Daga cewa zaka kira ni shine shiru, kwana da kwanaki.

Ki yi hakuri Nana, na baki ishashen lokacine ki yi tunani, bana son na raba miki hankali Nana.

Ina nake da nutsuwar da har zanyi tunani, bayan baka nan.

Ki yi hakuri to, bazan sake ba.

Yaushe zaka zo?

Nana akwai labari ne? Kin gama shawarar.

Na ce.

Uhm.

To Alhamdulillah, me kika yanke?

Na yi shiru, wata kunyarsa ta lulluSe ni.

Eyh, Nana.

Na amince.
Chapter 29 · 0% Book details