← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 50

Sashe 39

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doguwar riga na Wauka nasa, bayan na fito daga wankan na Wauki mayafinta nasa, bayan na yi wa fuskata light care, daga powder sai man baki, na Wau jakada takalmi na, nasa wayata a jaka na fito falo, zama na yi akan kujera dan bazanje Wakinsa ba ya ™ara ja mana wani abun, ina zaune naga Islaha ta fito daga Wakinta, wayata ce ta fara ™ara na yi saurin ciro ta daga jakar na duba.

Hello Ra is.

Na faWa bayan na Waga wayar, daga can Sarin ya amsa da.

Yaya Nana ya gida?

Tun da na auri Turaki Ra is ya koma ce min Yaya Nana.

Lafiya ™alau, ya su Hajiya.

Kowa lafiya, wai daman su Hajja ne suka ce a tambayeki yaushe zasu zo?

Too Ra is yaushe kake gani, yanzu dai fita zamu yi dashi dan ma na shirya, amma idan naga yanayin gidan gobe sai na ce su zo.

To Allah Yakaimu, komai da lafiya a gidan?

Lafiya ™alau Ra is.

To ma sha Allah, sai anjima.

Ya faWa yana kashe wayar, ina Waga kaina na ga Turaki a tsaye.

Ra is ne kenan?

Eyh shine.

Taso mu tafi.

Ni sai dai ka goyani.

Yanda kika ce ai haka za ayi ranki ya daWe, hau.

Ya faWa yana tsugunnawa, na yi dariya sannan na ce.

Bazaka karye ba?

Habibty ko irinki goma bazasu karya ni ba.

Ya faWa yana cacumata ya Worani a bayansa, ai kuwa ya Wauke ni cas muka fice, ina dariya, shima yana dariya.

To ka sauke ni anan?

Ai har mota, ko munje ma a baya zan shiga dake, duk wacca ta ganni tasan mijin Hajiya ne.

Ko mijin ta ce ba.

Na faWa ina dariya, shima ya yi dariyar sannan ya ce.

A a kan ta ce ne ni.

Na sake wata dariyar, daidai lokacin muka fito Waga part Winmu, a lokacin kuma Sardauna yake fitowa daga cikin motarsa, wani irin bugu na ji ™irjina ya bada. Fat& fafat. Shi kuwa Turaki ko ajikinsa ya taka zuwa wajen motar.

Ai baki da nauyi Habibty.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na talatin da biyu.

Wata uwar ™arar hon ce ta cika harabar gidan, wadda ta firgita mu har Turaki ya yi ™o™arin watsar dani ™asa, sai da ya yi zafin nama ya tare ni na faWa jikinsa.

Sannu.

Na faWa ina ™o™arin mi™ewa, ya ri™e ni tare da kashe min ido Waya.

Baki da nauyi Habibty.

Na ji, amma tashi kana ™asa fa, kayanka zasu Saci.

Sai na canja wasu.

Mu kuma mu Sata lokaci.

Na ji ni dai.

Duk yadda naso Turaki ya cika ni mutashi ya™i, sai da muka kusa minti goma a zube a ™asa, sannan muka tashi.

Juya naga bayanka.

Na faWa ina ko™arin juyashi, ya juya naga duk ™asa ta Sata wajen.

Gaskiyya sai ka canja su.

Tom ranki ya daWe.

Ya faWa tare da nufar cikin, ni kuma na koma jikin motar na tsaya, har ga Allah ni nama manta an hallici wani Sardauna a wajen, sai da na Waga kaina, kawai na ganshi ya zuba min idanu kamar zai cinye ni, na kau da kaina gefe tare da Wauko waya ta na fara dannawa, ina tsaye Turaki ya dawo cikin wasu kayan, na buWe mota na shiga shima ya buWe ya shiga muka bar gidan. Kwata kwata Turaki bai min maganar Sardauna ba, haka nima bance mai komai, tun rana da muka fita bamu muka dawo ba sai bayan biyar, duk wani babban wajen sha™atawa dake dutse sai da muka zaga shi, mu ka dawo a gidan gajiya ligib, kasancewar yamma ce kuma a ™oshe muke ya sa bamu nemi abinci ba, ba mu yi girki ba.

Wajen ™arfe takwas na dare Turaki ya shigo, ina zaune inda dannawa waya, dan kwana biyu ma fahimci danna waya, akwai dadi ga Webe kewa.

Habibty ta shi.

Na mi™e ina faWin.

Lafiya?

Gidan Big Daddy zamu.

Toopa.

Na faWa, sannan na nufi sif na Wauko mayafi na yafa na fito, Islaha na tsaye a falo shima yana tsaye, ina zuwa suka yi waje duka. Har da sauri na naje na buWe gidan baya na zauna, na barta a gaban ta ci uban da zata ci. Tafiyar ta kasance shiru, babu wanda ke ce da Wan uwansa komai, har muka ™arasa gidan.

Bansan zaman Babba ba ne, sai da na ga yan gidansu Turaki dukkansu, da kuma yan gidansu Islaha, a raina na ce.

Oh su mu saniyar ware.

Da sallama muka shiga duka, nuna shiga islaha ta yi Sarin da yan gidansu k zaune, ni kuma na yi kusa da ™annen Turaki na zauna, babu wanda ya ce komai sai da Big Daddy ya zo, Big Daddyn dai ban taSa sanin shine Big Daddy ba sai a yanzu, daman a wajen family meeting nake ganinsu, to kuma ni banda tabbacin waye wani Big Daddu sai yau.

Bayan ya zauna ne, ya fara magana.

Abubakar! Abubakar! Abubakar.

Ya kira sunan Turaki sau uku, ba iya Turaki ba, ni kaina sai da na ji gabana ya faWi sabida irin kiran da ya yi masa.

Na am.

Turaki ya faWa kansa a ™asa.

Kan ka aka fara auren dangi?

Ya girgiza kai.

Kan ka aka fara haWa mata biyu?

Ya sake girgiza kai.

Kan ka aka fara haWa mata a dangi da wata a waje?

Nan ma ya girgiza kai.

To me ya sa naka zai zo daban? A kan mata ka sa hannu kamari Alisha, ka mari Nusaiba, ka mari Islaha, ka mari Rufaida, dukka akan mace. Bayan zalunci da kake yi wa Islaha a cikin gidan.

Big Daddy wallahi ba haka ba ne, abinda suka faWa duka ba haka ba ne.

To idan ba haka ba ne yane? ˜aryata ni zaka yi? Idan ka ™aryata Alisha da take babba kaf cikin ku nima ™aryata ni zaka yi?

Mamansu Islaha ta faWa, sannan ta ™ara da cewa.

Ban da jaraba irin ta Islaha, ina so a wannan? Ina son a wannan da ya gama bin matar aure?

Haba Hajiya Falmata, wannan wace irin magana ce ai kya jira manya su sasanta tun da a gabansu ake.

Momy ta faWa, Hajiya Falmata ta tare ta cikin matu™ar fusata.

Ni rufe min baki, ai daman ko mene bazaki goyi bayan gaskiyya ba, zaki Wauki Wanki ne.

Ku bari mana, mene amfanin zuwa nan da kuka yi? Dan a fahimci juna ne fa.

Matar Big Daddy, Mama Amina ta faWa. Big Daddy ya ja numfashi sannan ya ce.

Islaha mene ™orafin ki?

˜orafi kuma?

Falmata ki yi min shiru.

Big Daddy katse ta sannan ya sake cewa.

Islaha mene ™ofarinki?

Cikin muryar kuka ta fara magana.

Baya zama ya yi hira dani, Baya cin abincina, baya kwana a tare dani sai dai a wani Waki daban, ranar kwanana ma na kama shi a Wakinta.

Shine ™orafin?

Ta gyaWa kai, sannan ya juya ga Turaki ya ce.

Abubakar, matarka Islaha ta kawo ™ararka bisa waWan nan abubuwan da ta lissafi, ko mene dalilinka na yin haka?

Sai da ya yi kusan minti biyar, sannan ya ce.

Big Daddy, Mom, Mama da sauran mutane ina neman afuwarku bisa abinda baki na zai furta, amma kamawa ta yi, bana so ku Wauki kalamai na a matsayin rashin tarbiya ko wani abu na daban, maganar zama hira da Islaha, ta™i bani haWin kai kwata kwata, ko ds muka yi aure ba ta taSa zama mun yi magana da ita ba, ban taSa zuwa na tarar ta yi min girki ba, tun auren mu har rana mai kamar ta yau, Islaha bata taSa sauke ha™™in aure guda Waya nawa akanta ba, hannu Islaha ba ta taSa bari na kama mata ba, bansan irin auren da take yi dani ba, bansan matsayin aurena da ita a yanzu ba, ko magana na ke yi mata bata tsayawa, haka zan ta binta ina magana amma ko kallo ban ishe ta ba.

Toopah!

Mama Amina ta faWa, Big Daddy ya ce.

Islaha haka ne?

A a, nice nake binsa yana hula™antani, idan namasa girki ba ya ci, idan ina masa magana baya kulani.

Me ya sa baki taSa kawo ™ara ba? Kuma a yanzu ma da kila lissafa ™orafinki baki faWe su ba?

Haba, a dinga adalci mana. Shi an yarda da zancensa ita na ta an ™aryata.

Hajiya Falmata ta faWa, Big Daddy ya ce.

Aina kika ji na ce ™arya take, shi gaskiyya yake?

To idan ma haka ne, marin da ya yi wa ya yana duka fa?

Zaki iya yin shiru, wallahi idan kika kaini bango zan cire hannuna alamarin na barshi da ita, ko sakinta ne ya yi.

To ya sake ta mana, idan ya sake ta sai me? Mene a ciki? Kanta zawarci farau? Matar da yake rawar ™afa a kai ma bazawara ce.

Ni A a, Mommy kar ya sakeni dan Allah, kar ya sake ni.

Islaha ta faWa tana kuka, ni dai ina zaune ina binsu da na mujiya, Wakin ya kacame baki Waya, Big Daddy ya yi shiru, sai dai Mama Amina ta bashi ha™uri sannan ya sake magana.

Kar na sake jin bakin wani, idan ba magana aka yi da shi ba, Islaha mene gaskiyyar abinda ya faWa, alamu sun nuna shike da gaskiyya.

Ni ban iya girki ba, kuma bai kirani Wakinsa ba.

Zaki rantse da Allah? Sau nawa ina zuwa Wakin ki?

Turaki ya katse ta, kawai ta saki kuka, Big Daddy ya ce.

Abubakar me ya sa ka daki Alisha, da Nusaiba, da Islaha, Hajara.

Daddy, Nusaiba kawai na mara, itama sabida ta mari mata ta ba tare da ta yi mata komai ba, daga ta tashi tana musu sannu da zuwa, tasa hannu ta Wauke ta da mari.

Nusaiba.

Big Daddy ya kira ta.

Me ya kai ki marin matarsa?

Rashin kunya ta yi min.

Ba ta girmeki ba? Gidan ta fa kika je.

Ni dai wannan zaman ba shi da wani amfani, zaman zalunci ne, ku tashi mu tafi.

Hajiya Falmata ta faWa tana mi™ewa, sauran ya yan nata suka mi™e, Big Daddy ya ce.

Abubakar, ya za ayi da Islaha?

Tabi su kawai.

Mommy ta ce.
Chapter 39 · 0% Book details