← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 50

Sashe 2

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana faWin haka ya fice, mi™ewa na yi na bi bayanshi, sai kuma na dawo na shiga ban Waki na wanke fuskata sannan na yi part Win na su. Dukkansu suna cikin Waki, wajen shiru ga ledoji nan duk an barsu a ™asa, kan dinning Win na kalla wata farar jallop idona ya sauka akai, ga ta nan cikin faranti, da alama loma Waya ya yi ya ajiye, kuma ba a kwashe kayan ba. Kai tsaye cikin kicin Win na shiga, shima kayan da aka yi aikin da su duk ba a wanke ba, ga tukunyar ma ta yi wani ba™i.

Ikon Allah.

Na faWa ina nufar gas Win, wata tukunyar na Wauko na yi amfani da ita, da sauri da sauri nake komai kamar Sarawon da yake sata yana tsoron akama shi, bana son na yi wani abu da zai sanar da masu gidan cewar ina nan.

Jollop Win taliya na shiga haWa musu, dan ma dai komai na bu™ata akwai shi a kicin Win, motsu motsu na ji a falon sai da gabana ya faWi, duk tsoro ya kamani. Bilkisu ta shigo kicin Win tana sanye da wata yar iskar riga dukkan jikinta a bayyane, kanta babu Wan kwali bare hula.

Me kike dafa mana.

Banza na yi da ita kamar ban ji me ta ce ba.

Ba dake nake ba.

Nasake yi mata banza na ci gaba da abinda nake, domin wata muguwar tsanar Bilkisu ke ci min rai, gaba Waya ta Wauke min hankalin mijina, ni duk wanda ya ce zai shiga tsakanina da Sardauna ya raba ni da shi, to ko waye natsaneshi kuma bazan iya Soye mai ba.

Dan uwarki ba dake nake ba, shegiya ballagaza jaka marar kishin kai.

Bilkisu ki fita a hurimina kafin na nuna miki zallan hauka.

Na faWa ina ci gaba da aikin da nake yi, ta yi wata shu umar dariya, sannan ta ce.

Nana bazan yi kishi dake ba, sabida nafi ™arfin hakan, amma wallahi sai na gasa miki tsakuwa a hannu.

Tana faWin haka ta fice, na sake goge ™wallar da ta fito min a idona, wani motsi motsin na ji a falon, da kuma wani irin haukatacen nishi. Gabana ya faWi ya bada wani Dum.

Legengdpen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na biyu.

Sautin nishin yana bugun kunnuwana, kamar ana ™wan™wasa guduma, haka cikin ™wa™walwata kamar ana buga kwano, ™irjina ya shiga wani irin bugu da sauri da sauri, kaina ya fara juya da sauri na dafe bango.

Ah! Sardauna da sonka zan mutu.

Bilkisu ta faWa cikin wata iriyar murya mai cike da kissa, da sauri na dafe kaina da faWin.

Innullahi wa inna illahir raji un.

Gaba Waya na ™asa ™arasa girkin, sai da na ji ya fara ™auri na yi saurin kashe wutar gas Win, gaba Waya so nake na fice daga cikin Sangaren ko zanji sau™in abinda nake ji a cikin zuciyata, domin wani irin tu™u™in azaba nake ji kamar ana soke min zuciyar da wu™a. Kamar me lamSo haka na ke bin hanyar da za ta sadani da ™ofar ficewa, bana ko kallon gabana na ™urawa ™asa ido ina tafiya.

Ba ta gyara wajen ba Baby.

Bilkisu ta yi maganar da ta tilastamin tsayawa.

Keeee.

Ya faWa cikin wata iriyar murya, na tsaya ba tare da Waga kai ba.

Zo.

A hankali na tako ina kallon ™asa, na zagayo daga bayan kujerar, yana zaune tana kansa.

Baby Waga ni.

Ya faWa ni dai tun da na kallesu sau Waya ban sake kallonsu ba.

Nana bance dake zaki gyara mata gida ba.

Na girgiza kai sannan na ce.

Ba zan ba.

Ni kike faWawa haka?

Baby kawai ta tafi gidan ubanta mana.

Bilkisu da zan iya da tuni na sallamata ta tafi, bazan iya jurar gani tana mu amala da wani Wa namijin ba ne Bilkisu, bazan iya ba.

Hannu tasa ta fara shafa masa fuska, sannan ta ce.

To ka tursasata mana.

Nana! Nana! Sau nawa na kira sunanki.

Bakina na rawa na ce.

Bib.. bib.. biyu.

Kar ki bari na kira na ukun, domin bazan kira shi da alheri ba.

Yana gama faWin haka ya jawota jikinsa ya ci gaba sa sumbatarta, wani zafi na ji ya mamaye rayuwata gaba Waya, take na fara zufa, cikina ya bada wani sauti. ˜ululululuwww. Da sauri na ta shi harda tuntuSe na fice daga part Win na yi nawa, ina zuwa na faWa kan kujera na fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, yinsa nake kamar raina zai fita, har ji nake gara na mutu da wannan ba™ar ranar, wai mijina da nake so na yi imanin zan rayu da shi, na bashi yarda da dukkan amanata, shi nake yake mu amalal aure da wata a gaban idona, wani irin cin mutunci ne wannan?

Kuka na nake yi marar iyaka, sai da na yi mai isata sannan na tashi na yi alwala na yi sallah, ina kan daddumar da na yi sallah na ji motsin su a harabar gidan, da alamim fita za su yi. Suna fita na tashi na shiga Sangaren nasu, kicin Win na shiga abincin da na dafa gashinan an Wiba an bar ragowar a tukunya, ba a gyara komai ba na kicin Win ba. Kwashe su na yi na haWe sannam na shiga gyara inda zan gyara, wanke wanke ne dai ban yi ba dan ko a nawa Sangaren ba yi nake ba, sawa nake ayi min bare kuma a Sangaren kishiya. Ina gamawa da kicin Win na dawo falon, shima na gyara duk abinda ya kamata na tattara idan zan tattara na fice zuwa nawa Sangaren.

Kicin Wina na shiga na ganshi fes da shi, na Waura farar shinkafa akan gas, haka kawai na ji nima akan gas Win zanyi girkin. Ina gamawa na buWe freeza na Wauko miya na Wumama, daga nan na dawo falo na zauna a ™asa ina ci, bugu na ji a ™ofa na yi banza dan a tunani sune, sai da na ji ana cewa.

Nana buWe Turaki ne.

Wani dogon tsaki na ja, a raina na ce.

Wannan uban me zai yi min? Duk wata matsala tsakanina da Sardauna shine ya asassata.

Sa™o ne Hajiya ta bada a kawo miki, gashinan a bakin ™ofa.

Yana faWin haka ya wuce ni kuma na tashi, buWe ™ofar na yi naga leda ce na Wauka na shigo ciki, bushashen kifi ne da yawa a ciki.

Allah Sarki Hajiya, Allah Ya ™ara miki lafiya da nisan kwana.

Na faWa a raina, Hajiya tasan yadda nake matu™ar ™aunar bushashen kifi shine ta bada akawo min, rabona da shi tun kafin na auri Sardauna, shekara uku kenan. Ina nan zaune har bayan magariba shiru basu dawo ba, anan na yi i sha ma amma basu dawo ba, ganin ™arfe tara ta wuce na tashi na shige Wakina na kwanta.

******

˜arar bugun ™ofar Wakin bacci na ce ta tayar da ni, a hankali na buWe ido tare da faWin.

Waye?

Nana zo ki buWe ™ofar nan.

A zabure na tashi zaune daga kwanciyar, na sau™o.

Shige muje.

Ya faWa bayan na buWe ™ofar, yana nuna min hannu, ba musu na bi hanyar na fice kamar munafuka, tun kafin na ™arasa na jiyo sautin muryarta tana faWin.

Bazan iya ba wallahi, haba Baby ka ce wannan ka ce wannan, ni ban iya kayan fulawa ba wallahi. Tun 8 nake kicin ina fama ™waSa abu, na gama kuma ka ce wai ya yi ba™i, ba jaka ba ce ni da zan dinga yi ma girke girke.

Baby it s okay, gatanan ai.

Ya faWa bayan mun ™araso Wakin, kallona ta yi sannan ta Wauke kai.

Ka yi yadda za ka yi da ita, gashinan goma saura, kuma sha biyu nake da class dan haka ni zan fice, ta yi min girkin rana.

Tana faWin haka ta fice ta barmu ni da shi a falon, ni kuwa zallan mamaki ya cikani. Ina Bilkisu ce min ta yi aiki take, to yanzu kuma ta ce lectures, ji shigar jikinta a haka za ta tafi makarantar? Ni da nake sanya hijabi ance ana kishina?.

Dole ya yi kishinki mana Nana, ita fa a yanzu amarya ce kome take so yi mata zaayi, kin san Sardauna yana sonki kuma zai dawo gareki.

Wani Sari daga zuciyata ya katsemin tunanin da nake ta wannan amsar.

Nana!

Ya kira sunana, na Waga kai na kalleshi ba tare da na amsa ba, a raina ina addu ar Allah ya sa Sardauna ya faWa min abu mai daWi.

Nana kin zaSi na dinga zama da yunwa?

Da sauri na girgiza kaina, wani tausayinsa ya ratsamin zuciya.

Nana! Daga yau kin daina girki a Sangarenki, sai dai ki dinga yi anan kema kina ci.

Tom.

Sannan Nana zaki dawo da rayuwa anan Sangaren gaba Waya, sabida Bilkisu tana makaranta ba ko yaushe zata dinga zama ba, idan ta dawo daga makaranta ke kuma sai ki tafi Sangarenki ki zauna! Sabida kayan da suke nan sunfi naki daraja da tsada, can iya kayanki ne tun da na kwashe nawa, amma nan akwai nata akwai nawa, akwai gwala-gwalanta da sar™o™i.

Tom.

Yawwa Nana, yanzu asama min abinda zanci ina jiranki.

Ta shi na yi na nufi kicin Win, kwaSin samosar da ta yi na Wauka na ci gaba da shafawa, cikin ™an™anin lokaci na kammala na haWa na kawo masa, bayan ya amsa na kalleshi, wani irin tausayinsa ya ratsa min zuciya, Allah Ya sani ina son Sardauna da dukkan rayuwata, ina tausayinsa da dukkan numfashina.

Allah Ya ™ara maka arzi™i da wadata.

Na faWa a raina sannan na fice, gaba Waya tunanin irin yadda Sardauna da Bilkisu suka dinga yaudarata ya shiga zarya a kaina, har nake hasaso abubuwan da bansan da su ba, amma da yake zuciyata ta mutu akan Sardauna ta shiga bani uzurruka masu ™arfi akan Sardauna har na kasa gani ko da laifi Waya.
Chapter 2 · 0% Book details