← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 50

Sashe 31

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ™an™anin lokaci muka fara sabawa da Dr Aliyu, har gida ma suka san shi, duk da bai sami karSuwa a wajen yan gida ba, amma ni dai ya yi min, ya kan Webemin kewa sosai. Mussaman a yanzu da idan na kira Turaki bama samun dogon lokaci muna waya, sai kawai na kira Dr Aliyu, sai mu shafe awa guda ko fin haka muna waya dashi, haka a asibiti duk lokacin break muna tare.

Yawan zuwan da yake yi ne ya sa Hajiya ta yi min magana a kansa, na ce mata a asibitinmu yake, sai kuma ta tambayeni Turaki na ce mata yana nan.

Nana, idan wani abu ne ya faru ya kamata ki sanar da mu.

Na ce.

Hajiya ba komai fa, shi wannan a asibiti yake, kuma yanzu muna samun lokaci tare da shi sosai, saSanin Turaki da yanzu al amuran kamar ansa hannu, sai mu daWe ba mu yi doguwar magana ba.

To Nana ki yi masa uziri mana, kinfa san abinda yake faruwa, da kanki kika ce akan ki yana fama da yan uwansa.

Hajiya, nifa ba wai son sa na daina ba ko auren sa na fasa, kawai na duba mana mafita a tsakanin ni dashi, bazan so ya ci gaba da kasancewa cikin matsala ba akaina, kuma wannan ai Hajiya ba cewa ya yi yana sona ba ko.

Nana kenan, yanzu ke kina nufin baki fahimci soyayya ce a tsakanin ku ba ko me?

Ni ban fahimta ba.

Shikenan Nana, amma dai karki zama mace mai sonkai, da rashin uzuri. Kinsan dai abubuwan dayawa da yaron nan Abubakar ya sadaukar akan ki, ke da kan ki kinsan har yanzu yana fama da abubuwa duk sabida ke, amma kina son ki nuna bazaki iya yi masa ha™uri ba.

Nifa Hajiya duk baku gane komai ba ne, amma ba haka nake nufi ba.

Ni dai tunatarwa na yi miki.

Tashi na yi na shige Waki, gaba Waya maganganun Hajiya sun tsaya min a rai, kuma gaskiyya ta faWamin sai dai ni ina cikin nau in mata masu son soyayya da kulawa, a yanzu Turaki duk ya janye daga gaisuwa shikenan, idan kuma ya ha™ura zai yi wa iyayensa biyayyane fa, nima ai gwanda na ha™ura dashi kaman zaifi. Daidai lokacin kuma kiranshi ya shigo, na Waga tare da faWin.

Salamu alaikum.

Amin wa alaiki salam, Habibty ya kike?

Ina lafiya ya kake?

Nima lafiya, ya su Hajiya.

Duka suna lafiya.

To Ma sha Allah, Habibty ina ™ara baki ha™uri akan yanda abubuwa suka canja, nima ba a so na ba ne, na Wan ja baya ne sabida wasu dalilai, kuma in sha Allahu a gaba zaki fuskance su.

Ba matsala, amma dan Allah Turaki idan ka fasa aure na ne ka faWamin.

Habibty mene haka wai? Na fasa aurenki kuma? Kina tunanin zan fasa aurenki akan wani abu? Dan Allah ki daina wannan zancen.

Shikenan na daina, yanzu yaushe zaka shigo?

In sha Allah zanzo.

Ai kullum haka kake cewa.

Nasani, amma zan zo.

Tom.

Kawai na faWa tare da kashe wayar, ni gaba Waya yanzu babu wani shau™i a tattare da shi, anya ba daina sona mutumin nan ya yi ba. Ban kai ga amsa tambayar da na yi wa kaina ba kira ya shigo wayata, ina dubawa naga Dr Aliyu. Shima raina ba daWi na Wauka da faWin.

Hello Dakta.

Nana, ya gida?

Lafiya ™alau.

Me yake damunki ne?

Babu komai mai ka ji?

Haba Nana, gashinan muryarki ta nuna damuwa.

Tashi na yi zaune daga kwanciyar da nake, na ce.

Kawai raina ne ba daWi.

Ayyah! Ki yi ha™uri kin ji ko, Gobe zaki shigo ko?

Eyh, in sha Allah.

To ko zan iya ganinki kafin ki shiga dan Allah, magana ce nake so mu yi mai muhimmanci.

Tom shikenan, babu damuwa Allah Yakaimu.

Amin Nana.

Daga nan muka Wan taSa hira, amma da yake raima duk ba daWi ban wani jin daWin hirara ba. Washe gari, ina zuwa asibiti na wuce ofis Winsa na same shi, duk na matsu na ji me zai cemin. Bayan na zauna ya kalli ni ya ce.

Nana.

Na ce.

Na am.

Nana, tun a zamana dake baki taSa tambayar wani abu game da ni ba, rayuwata, iyayena da yan uwana, ina da aure ko babu?

Na yi shiru, nasan tabbas ban taSa amma ganina ai tun da zama ne na lokaci kamar babu bu™atar wannan.

Kinyi shiru?

Eyh gaskiyya ban taSa ba.

To me ya sa? Nana kinsan yanda na Wauke ki kuwa?

Ji na yi gabana ya yi wani irin bugu dum, na Wago na kalleshi, ya gyaWa min kai, sannan ya ce.

Nana na Wauke ki da wani irin muhimmanci tun ranar da na fara ganinki, Nana tun bayan rasuwar matata Amina, bansake kallon wata mace da irin kallon da nake miki ba.

Na Wago na sake kallonshi da wani irin tausayi. Matarshi mutuwa ta yi kenan?. Na faWa a raina, sai dai ya ban amsa da cewa.

Eyh Nana, Amina ita ce macen da na fara so tun muna makaranta, munyi soyayya mai daWi, kuma munyi aure duk da mun fuskanci ™alubale da dama, amma Nana hakan baisa mun janye soyayyar da muke wa junanmu ba, har Allah Ya nufe mu ga aure, mun fara rayuwa cikin soyayya Nana har Allah ya albarka ce mu da samun juna biyu, da gani har ita munyi murna, munyi farin ciki. Sai dai bamu san wannan juna biyun shine zai zama ™arshen farin ciki a tsakanina da ita, lokacin da Allah Ya nufe da haihuwa lokacin ne kuma Allah Ya amshe ta a lokacin haihuwar, ta mutu ta barni da jarariya, wacca na mayarwa da sunanata. Nana tun a lokacin ban sake jin wata mace ba, bansake ganin wata mace ba, sai a yanzu da na ganki, Nana na kamu da soyayyarki me zafi, ki taimakamin Nana, wallahi ina sonki, Nana ko yanzu kike so zan aureki, Nana ba wasa nake miki ba.

Na yi shiru, jikina duk ya mutu, wani irin tausayinsa ya ratsa zuciyata, mutuwar mata a lokacin haihuwa tabbas abube mai tsayawa a rai.

Nana.

Ya kira sunana, na Waga kai na kalleshi, ya ce.

Nana ko kina da wanda kike so ne? Nana ko banyi miki ba?

Na girgiza kai, sannan na ce.

Ba haka ba ne, nima na taSa aure, amma Allah bai nufi auren da kasancewa na har abada ba, duk da ba haka na so ba, amma Allah bai nufa ba, na yi shekara uku da watanni.

Nana, ni ke nake so, nasan gidanku, nasan tarbiyar gidanku, Nana duk wani abu da ya faru a rayuwarki ta baya, ya riga da ya faru, sanin shi a gareni ba zai canja komai ba, Nana dagaske nake sonki, Nana ko a satinan ne a Waura mana aure.

Na girgiza kai alamar a a, kafin na yi magana ya ce.

Nana, ba aiki ba ne, ni zan dage wajen sama miki aiki, Nana ina da ilimin addini, ina da na zamani,ina da wayewa, nasan abinda yake mai kyau nasan mara kyau Nana.

Ba haka ba ne, akwai wanda a yanzu yake nuna yana sona, kuma shina aurena zai yi, sai dai yana da matsala ta ahalinsa.

Ya yi shiru na kusan mintina goma, sannan ya ce.

Nana, bazan tursasaki ba, ba kuma zanm raba miki soyayyarki ba, amma Nana ina sonki da gaske da zuciyata, Nana ki tausayamin, ki yi tunani a kaina, Nana ko ba ni ba ki duba yarinya ta ™arama dake cikin halin maraicin rashi uwa, Nana nasan zaki kula da ita, zaki so ta tamkar yadda mahaifiyarta za ta yi Nana.

Wani ™arin tausayin naji ya lulluSe ni, tabbas ina son Turaki, amma ni kaina zan so masa zaman lafiya da iyayensa, na duba Dr Aliyu, da yarinyarsa, suna matu™ar bu™ata ta a rayuwarsu.

Nana, dan Allah ki duba, bana son na takura miki, amma bana son na yi sanyi na rasa ki Nana, dan Allah.

Shikenan, zanyi shawara.

Na faWa, sabida zuciyata gaba Waya a cakuWe take.

Shikenan Nana, na gode.

Na tashi na fito, kai tsaye gida ma na nufa dan bazan iya zama cikin asibitin ba, sabida wani irin nauyi nake ji a zuciyata, dole na yi tunani na yi shawarar. Sai dai ko da naje gida kasa maganar na yi da Hajiya, ga Ra is bayanan, ga Yaya Ridwan babu fuskar ma da zamuyi wannan maganar da shi, Yaya Rumaisa kuma ba a maganar arzi™i da ita, gwanda Yaya Radiya ma.

Haka na yini raina ba daWi gaba Waya, sai dai a wannan yinin Dr Aliyu ya kirani sama da sau biyar ya ce wai ina lafiya, kar na takura kaina, kar na damu, na yi tunani a nutse, Turaki kam ko da na kira shi na ce yaushe zai zo sai ya ce idan zai zo zai yi min magana, har dare ina faman tunanin da narasa mafita, haka na kudirci niyar tashi cikin dare na yi sallah, dab da zan kwanta na saita alam ya tashi ne ™arfe uku da rabi na dare, sannan na kwanta.

˜arfe uku da rabi alam Win ya fara ™ara, na kusa minyi sha biyar a kwance kafin na tashi da ™yar, gaba Waya ban iya tashi cikin dare ba, shi ya sa yau Win ma nakasa, ba ™aramin mamaki na yi ba ganin Hajiya a tskar gida tana sallah.

Allah Ka bani ikon tashin daren nan nima.

Na faWa ina nufar bayi, sai da na Waura alwala na fito, na le™a Wakin Yaya Ridwan ta taga na ganshi shima zaune kan abun sallah, na ce.

Ikon Allah, ana ta ibada ina ta bacci, dole ma abubuwa sun caSemin.

Šakina na dawo na Wauki abun sallah na shimfiWa na tayar da sallah, sai da na yi raka shida, sannan na ta fara addu a, sai da na yi addu a sosai da sosai, sannan na koma bacci na, sai dai ban daWe da kwanciya ba aka yi sallar asuba. Gari na wayewa na sake samun kiran Dr Aliyu, na Waga tare da faWin.

Ina kwana.

Lafiya ™alau Nana, kintashi lafiya?

Lafiya ™alau Alhamdulillah, Ya gida, Ya little? Sunan da na ji yana cewa da yar sa.

Kinganta yanzu nake son tashinta, yau zaki shigo?
Chapter 31 · 0% Book details