← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 50

Sashe 19

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni da Ra is ne muka yi gida a mashin Win Yaya Ridwan, sai mota Waya me Wauke da kayan kicin da kayan sawa na, da wasu abubuwan. Šayar kuma su Yaya Radiya da Yaya Rumaisa da Ya Ridwan suka nufi kasuwar katakwaye, sabida Yaya Rumaisa ta rantse ta kuma rantsewa ba za a shiga da kayan Sardauna cikin gidanmu ba. Tun da muka shiga unguwarmu idon mutane ya yo kanmu, gaba Waya na tsargu ganin irin kallo da ake bin mu da shi, da motar da muka kwaso kayan aciki. Har muka tsaya a ™ofar gida ina jin idanun mutane akaina.

Da gudu gudu na shiga cikin gidan, ina shiga na fashe da wani irin kuka, idanun mutane da nagani ya kiWima ni, yanzu nasan babu wata ake maganarta kaf yelwawa sai ni.

Nana me ya faru kuma?

Hajiya ta faWa, ban kai ga bata amsa ba Ra is ya shigo.

Hajiya ba abinda ya faru, kawai rigima ce irinta ta.

Hajiya baki ga yadda mutane suke kallonmu ba, ba kiji yadda ake zunWen mu ba Hajiya.

To Nana kan ki farau ko ™arau? Mene a ciki dan mutane sunyi zancen ki?

Nima shine abinda nagani Hajiya.

Ra is ya faWa, yana ™o™arin fara shigowa da kayan da mu ka tawo dasu.

Ina sauran suke?

Wai sun tafi kasuwar katakwaye.

Na faWa, bayan na zauna akan dakalin ™ofar Wakin Hajiya.

Me za su yi acan?

Kayan zasu siyar.

Sabida me?

Ban bata amsa ba Ra is da ya sake shigowa ya ce.

Hajiya duk ya siyar mata da asalin kayan da aka kaita da su, sai waWan nan aka Weba shine Yaya Rumaisa ta ce ba za akawo su nan ba siyarwa zaayi, ba ta son duk wani abu nasa a gidan.

Eyh to, hakan ma ya yi.

Ni dai na zauna jigun ban iya cewa ko ™ala ba, da ido nake bin Ra is da kayan da yake shigowa da su, har ya gama sannan ya zauna yana faWin.

Hajiya a zuba min abinci.

Karka zauna, zuba da kanka ni bayi zan shiga.

Hajiya ta faWa, ba musu ya mi™e ya shiga kicin ya zubu.

Zaki ce?

A a.

Na ce da shi, na zauna na co gaba da tagumi na. Ina nan zaune shi yana gefe yana cin abinci Hajiya ta fito, ta shiga Waki ta shirya ta sake dawowa tsakar gidan.

Hajiya kinsan me?

Ra is ya faWa.

Daman zama na yi ka faWa min abinda ya faru.

Hajiya kinga rashin arzi™i kuwa? Wai amaryarsa har da wani Webu ™awayenta su yi mana rashin mutunci.

Dan Allah fa? Kai amma waWan nan ya ya ba su yi ba.

Hajiya ta faWa tana ta fa hannaye, ni kuwa kallonsu nake ina mamakin yadda suke zama kamar ™awaye, suna hira.

Kinsan kuma ™azama ce, gidan har wani wari yake.

Can su ™arata Ra is, mu dai ga tamu anan, babu wani abu da ya shafemu da gida, dan haka su yi abinda suka ga dama.

Ki faWa masa dai Hajiya, sai gulma da ™ananan magana kamar wata mace.

Ke kuma sai nun™ufurci.

Tashi na yi, na shige Waki na barsu suna ta mai da yadda aka yi, Hajiya kamar a gabanta akayi komai haka yake ba ta labari. Ina cikin Waki a zaune na ji sallamar ™awata Malaika, duk daWewar da akayi ba zan iya manta muryar Malaika ba, nasan dai jaje ta zo yi min amma kuma bana son wannan abun nawa ya yaWu. Suna gama gaisawa da Hajiya ta ce da ita.

Ki shiga tana ciki.

Da sauri na rufe idona, na yi baje baje kamar me dogon bacci, amma dake Malaika uwar naci ce sai da ta tasheni, a hankali na buWe idona na sauke su akanta, na sakar mata murmushi tare da faWin.

Malaika.

Nana.

Ta faWa tana zama, na sake wani mumushin sannan na ce.

Yaushe a gari?

Šazu na faWa miki, ake sanar da ni abinda ya faru na ce wallahi bazan zauna ba, sai nazo na ga ™awatah, Nana ashe abinda Sardauna ya yi miki kenan, Allah Ubangiji ya gamashi da daidai shi mitsiyaci.

Na yi murmushi, sannan na ce.

Wallahi fa.

Ai tun yadda naga hotonansu suna yawo a kafafen sada zumunta na ce wannan tsohuwar soyayya ce, tun lokacin naso fargar dake amma naga kamar idonki a toshe yake.

Wallahi Malaika ba iya idona ba, gaba Waya ma a toshe nake, na yi rayuwa a cikin duhun rayuwa, sai yanzu nake ganin haske.

Allah Sarki ™awatah, mun yi magana da Fauziyya da Amina tuntuni, amma ganin kamar ba kya bu™atarmu ya sa muka ™yale ki, ace Nana a gidan miji ko waya ba kya Wagawa, wane irin aure ne wannan?

Ba zaki gane ba ne Malaika, sai dai kawai na ce Allah kar ya Worawa wani irin ™addarar soyayyar Sardauna da ya Woramin, amma kinsan wani abu?

Ta girgiza kai, na ce.

Wallahi Malaika ko Wigon son Sardauna yanzu babu a raina, ina jin kamar ada ma ba son Sardauma na yi ba, wani abu ne kawai da Allah Ya ™aga, a Wazu da naga Sardauna sai na ji matu™ar haushin kaina, da na so sardauna, Malaika a gidan Sardauna ban sami wani abu na mussaman ba, wanda babu a wani wajen, kullum rayuwata daga kicin sai zaman falo, kinsan a gidan Sardauna ko firjin ban isa na kunna ba, tabbas Allah ne Ya ™addara min rayuwa a gidan Sardauna, kuma nasan na so Sardauna son dan bantaSa yi wa wata hallita ba, a lokacin da son Sardauna ya tashi barin zuciyata, sai ya busar da zuciyar ta ™ame ™am, babu wani abu da nake so ko marari, wallahi Malaika na ha™ura da rayuwar gaba Waya, na ha™ura da komai na sallama.

Nana, kar ki ce zaki cire tsammani daga rahamar ubangiji, Nana akwai tarin alheri da suke a gaba, Nana rayuwar yanzu aka fara ta, akwai saura a gaba in sha Allah, kuma zaayi nasara, dole a yanzu kina cikin halin da zuciyarki ke bu™atar lallashi, kulawa da dogon ha™uri, amma tabbas Nana komai zai wuce, Wallahi zaki ga kamar ba ayi komai ba.

Bana jin rayuwata da ta gutsire fatsa fatsa, zata sake haWuwa waje Waya, akwai mutanen da basu da wata sa a a rayuwa, ni dai ina fatan bana cikinsu.

In sha Allahu Nana, ba kya ciki.

Sallamar su Yaya Rumaisa ce ta katse mana maganar da muke yi, muka tashi muka fito gaba Wayanmu, mu ka tarar Hajiya na yi musu sannu da dawowa. Sai da suka zauna Yaya Radiya ta ce.

Hajiya kayan gado fa sun yi kasuwa, har miliyan Waya da dari huWu.

A raina na ce. Aikuwa ba su yi daraja ba, domin sardauna ya kashe sama da miliyan uku akan waWan nan kayan, kuma ba wani amfani aka yi da su ba.

Ni Yaya bai dame ni ba, ai Wan fariya ne zai yi abinda yafi wannan.

Yaya Rumaisa ta faWa, Hajiya ta ce.

Me za ku yi da kuWin ne yanzu, ni dai a mayar masa kar yazo ya yi wa mutane tashin hankali, yaron nan ba Wan arzi™i ba ne.

Ya daWe bai yi ba Hajiya.

Yaya Rumaisa ta faWa tana mi™ewa ta nufi cikin kicin.

Hajiya ina abincin?

Yana cikin seat room.

Ni yanzu Hajiya da cewa na yi asiya wasu kayan katakon a ajiye mata, ko sabida gaba.

Ni a a, bana son kayan katako, ni bana son na ji anyi wata magana ta aure, bazan yi ba, bazan sake aure ba.

Ke dallah rufe min baki, kar ki yi auren ke kika sani, Wazu wani shegen kallo wancan mitsiyacin ya yi miki duk jikinki ya yi sanyi.

Yaya Rumaisa ta faWa tana fitowa daga seat room Win, hannunta ri™e da plast Win abincin.

Rumaisa ce miki aka yi yarinyar nan tana bu™atar tsawa ne? Ko hayaniya, ki zo ki tarkata ki bar min gida.

Hajiya ai Nana bata bu™atar wani rarrashi, maganin da Turaki ya kawo mata masu ™arfine, kuma sun yi mata aiki da wuri, yanzu zallan iskanci ne.

Tashi na yi na shige Waki, jin surutun nasu zai sanya min wani ciwon kai na daban, ina shiga Malaika ta biyo ni, sai dai bamu kai ga magana ba Turaki ya yi sallama.

Waye ya zo?

Malaika ta faWa, ban jiyo ba na bata amsa

Turaki ne, cousin Win Sardauna.

Shi kuma lafiya?

Eyh lafiya ™alau.

Nana bari na wuce to, gobe dai zan tafi amma zan sake shigowa.

Shikenan Malaika, ki gaida su Mama na gode.

Fitar ya yi daidai da shigowar Turaki, wani irin abu na ji ya fara yawo a cikin zuciyata, na kasa jiyo na kalleshi ko na yi masa magana.

Legendspen

08129553971

Sorry for the short page.

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na sha shida.

Nana, ya jikin?

Na ji ya faWa, ni kuma gaba Waya na rasa me ya sa bana son na waigo na kalleshi.

Me kike a tsaye ne? Ko jikin ne?

Na girgiza kai, sannan na zauna.

Da sau™i Alhamdulillah.

Gashinann kam na gani.

Na yi murmushi ba tare da na bari mun haWa ido ba, haka kawai na ji yau ina jin nauyinsa fiye da ko yaushe.

Nana.

Ya kira sunana, na amsa ciki ciki.

Šago ki kalle ni mana.

Na Wago amma ban kalleshi ba.

Yanzu mene tsarinki na gaba?
Chapter 19 · 0% Book details