← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 50

Sashe 24

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kuma kanawa ba a rabasu da ™yale ™yale.

Fito mana.

Ya faWa yana buWe min ™ofa, nasa ™afa na fito muka nufi cikin wajen, sai da muka shiga naga ashe banga komai daga waje ba, wajen shan ice cream ne mai rai da lafiya, shima wajen mutane sai hada hada suke, lallai na yarda kano ta ninka jigawa a wayan jama a, ko ina ko gota mutane kaca kaca. Ina tsaye ya siya mana muka samu waje muka zauna, muna sha muna hira. A wannan zaman na fuskancin Turaki yana son gulma kamar Hajiyar mu ce ta haifeshi, da ya waiga ya ga mutane sunyi abu zai yi ™asa da kansa ya ce.

Nana& kalli na bayan mu, karki kallesu direct ki Wanyi kamar abu kike dubawa.

Ni dariya ma ya bani, yanda yake ™asa da kai da yanda yake ™asa da murya.

Nana wai me ya sa kike shiru? Nifa bana so kike shirun nan, shi ya sa nake miki gulmar mutane sabida musami abin faWa, bana son kina wannan shirun, sai naga kamar kina da damuwa.

Ni bani da wata damuwa, kawai yanayin wajen nake mamaki.

Mamakin me?

Acan bamu da irin wajaje haka.

Muna da su Nana, kawai ba tsarinki ba ne, may be a gida baki sami damar zuwa wajen ba, sannan kuma mijinki na farko bai da wannan ra ayin.

Amma wajen ya burgeni.

Shi ya sa Nana ake son ma aurata su dace da yanayi halaiyar juna, ko da ba halayensu sun kasance duka iri Waya ba, Waya yasan halin Waya ya kuma ko yi zama da wannan halin.

Hakane kam.

Na faWa, daga nan muka ci gaba da hira, kamar yadda yake Wauko zancen na baya na ya kawo min, haka nake Wauko zancen na bayansa na kawo masa, yanayin ya yi min daWi sai na ji kamar ma kar mu rabu, kamar mu dauwama a haka, idan a baya aka ce min bayan na rabu da Sardauna zan ga rayuwa irin haka bazan taSa yarda ba, idan aka ce min zanyi farin ciki ina tare da wani namiji bayan Sardauna bazan yarda ba, dukkanin farin cikina na Worashi ga Sardauna.

Tara da rabi daidai, ya sauke ni a bakin hostel Winmu, bai tafi ba sai da yaga shigata sannan ya shiga tashi motar ya tafi, ina shiga Waki na canja kaya na kwanta, sai dai ina rufe idona babu abinda nake ganin sai sassanyan murmushi Turaki. A haka na yi baci da murmushi a fuskata, babu abinda nake tunawa sai Turaki.

Washe gari da safe, bayan na yi wanka na dafa wata taliyar na ci, sabida bani da wasu isassun kayan shayi, bayan na shirya ne na kira Hajiya a waya muka gaisa, sannan na kira Yaya Ridwan shima muka gaisa, bayan nan na kira Yaya Rumaisa ita ma mu ka gaisa, Anty Adiza kuma na ce sai na dawo, ina son ma na bawa Turaki addresss Win gidansu ya kaini ko cikin weekend ne. Da map Win na duba ajin da zamuyi lectures wanda ke jikin time table Wita, group Win ma tun jiya Turaki ya yi min joining, amma naga a rufe yake Admin ne kawai zai iya magana a ciki. Ajin babu wasu hayaniyar Walibai, bamu fi mu talatin ba, malamin yana daga sama kowa yana zaune tsilli-tsilli.

Cikin sauka™a™en turanci malamin yake bayani, wanda muke ganin a jikin computer da take gaban kowa, awa Waya da minti sha biyar daidai ya yi ya fita, ina duba wayata naga ashe Turaki ya yi min message daidai lokacin da na shiga ajin, ina fitowa daga ajin na kira wayarshi, bugu Waya ya katse ua kirani, ina Wagawa ya ce.

Har an fito?

Eyh an fito.

Sai yaushe kuma?

Bayan awa Waya.

Tom, Allah Ya bada sa a, kunyi waya da su Hajiya?

Eyh, munyi.

Tom Allah Ya yi albarka, nima meeting zamu shiga, idan muka fito zan kiraki, idan baki shiga ajin ba.

Tom, Allah Ya bada sa a.

Na faWa tare da kashe wayar, wani waje nagani mai inuwa ga korayen ciyayi masu daWin kallo, ga kuma kujeru da mutane tsilli-tsilli, nufar wajwn na yi na sami wata kujera na zauna, ganin kowa da waya a hannunsa yasa nima na Wauko tawa na fara dannawa, rasa abinda zanyi da ita na yi, sai kuma shawarar gwada amfani da facebook ta faWomin, na shiga wajen searching na rubutu, zawarawa, sai kuma na goge, na rubuta yaya ake samun taimako akan karatu, shima na goge, mutuwar aure a yau, shima na goge, na yi shiru ina tunanin me zan rubuta, sai can na yi tunanin rubuta matsalal rashin haihuwa, ina rubutawa naga sun watso min bayanai, posting ma mutane kala kala, kowa da kalal nashi bayanin da irin maganin da yake rubutawa a nema, na maida hankalina gaba Waya ina dubawa, na karanta wannan n karanta wancan, na shiga wannan comment Win na fita na shiga wannan, na samu ilimi mai tarin yawa a wannan posting Win da comment da na duba, idan kuwa hakane lallai Sardauna ya daWe yana cuta ta, na rasa exprience nasanin abubuwa da yawa, yanzu da ace tun asali mahaifar tawa bace ™wari ai da ina bibiyar nan akwai tarin magungunan da zanyi amfani da su, ina cikin dubawa ma naga wani group wai shi mu gyara kan mu mata, ba shiri na yi joining, na ci ga ba da dubawa, na ga wani ma sirrin ya mace, shima na faWa, nasan ba za a rasa group na banza da na gari ba, duk wanda naga abinda ake yi bai yi min ba sai na fita, haka naga wani ma magani a gomar yaro, duk na dinga shiga ina duba abubuwa da yawa, har lokacin shiga Waya lectures Win ya yi, na tashi na shiga.

Shima wannan cikin sau™a™en turancin yake komai, shi ta awa Waya da rabi ya yi, kuma abinda ya ™ara burgeni yadda komai ake magana akai sai an sami samfirin shi an gwada muku komai.

A haka aka tashi na koma Wakina, na watsa ruwa na kwanta, ba ni na tashi ba sai wajen huWu, ina yin sallah na shiga kicin na dafa farar shinkafa, a yanzu duk na koyi ™iwar yin girki gaba Waya. Sai da na ci abincin na duba waya ta na ga she Turaki ya kira ina bacci, ina shirin bin kiran na shi ya ki rani, abinda yaban mamaki bai fara yi min maganar kin Waga kira ba, sai ya fara ce min.

Ya karatun?

Na ce.

Alhamdulillah.

An dawo ko ana can?

Na dawo, yanzu ma na tashi daga bacci, naga kiranka ina son kira kuma ka kira.

Sai yanzu kike cin abinci? Karfe hudu fa?

Lokacin da na dawo bana jin yunwa.

A a kar ki yi wasa da abinci.

Tom, in sha Allah.

Šazu ma Ra is ya ce min wai Hajiya ta ce ya tura miki kuWi, zaki yi siya kayan shayi ko? Me ya sa nj bazaki faWan baki da kayan shayi ba?

Na yi shiru, ni dai nasan banyi wata magana da Hajiya ko Ra is ba, amma kuma ya aka yi suka yi masa maganar.

Eyh Nana.

Nifa banyi magana dasu ba, sai dai idan sune suka tuna ba a sa kayan shayi ba anan, shine Hajiyar ta ce masa ya turamin.

To amma baki faWan ba tun farko, ko da yake laifi na ne da ban bibiyi kayan abincin ba ki yi ha™uri.

Ha™uri kuma?

Eyh mana.

Na yi shiru ni bansan me zan ce masa ba,

Kinyi shiru.

Bakomai fa.

Ya karatun ana ganewa.

Sosai da sosai.

Yawwa hakan nake son ji, kinsan wani abu?

Na ce a a.

Shikenan tun da baki sani ba.

Na yi dariya, muka shiga hirarmu. A kullum sai munyi waya da Turaki sama da sau biyar, duk da ba kullum yake zuwa ba, amma a kullum ji nake kamar ina tare da shi, ya siyo min duk wasu kayan bu™ata, ya ™ara Waukana sau Waya munje wani wajen daban, kwana biyu aikin da yazo yi ya Wan sa shi a gaba, amma ko da yaushe muna tare a waya, a yanzu ji nake kamar ba zan iya ™wak™waran awa guda ba tare da na ji mostin Turaki ba.

Yau tun safe na shirya zuwa gidansu Anty Adiza, na kira Turaki ya ce da ni yana aiki amma zai yi min Bolt ya tura min, ina zaune bayan na gama shiryawa aka kirani a waya, wai me mota ne yana wajen gate Win Hsotel, ko da na fita naga motar sai da nasa ki baki, wannan makekiyar motar ake haya da ita? Kai kano ko da me kazo anfi ka. Shiga motar na yi muka fara tafiya, tunda muka hau babban titi na ji gabana yana wani irin faWuwa, wadda na rasa dalilin hakan. Muna tsyawa a danja kamar ance Nana kalli hagu, na ganshi a cikin mota, yana sanye da farin men lace kamar ko yaushe.

Innullahi wa inna illahir raji un.

Na faWa ina ™o™arin kawar da kaina gefe.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na sha ashirin.

˜asa na yi da kaina, na yi saurin zuge gilashin motar, a raina ina addu ar Allah kar ya haWa ni ido biyu da Sardauna, a gefe guda kuma ina mamakin mene ya kawo shi kano, kuma shi kaWai ba Bilkisu? Cikin sa a danjar ta saki muka wuce ungwuar su, Hotoro GRA sunanta, unguwa ce ta masu kuWi sabida gaba Waya manyan gidaje ne a ciki, har ™ofar gidan ya kai ni; ina sauka ya kira Turaki a waya ya faWa masa, shi ya tura masa kuWin ni kuma na shiga gidan, na yi matu™ar mamakin yadda mutanen gidan su ka tarbe ni, kamar sun sanni kafin yanzu, haka yara ma Anty Nana, Anty Nana. Na ji daWi sosai kuma naga karamci a gidansu Anty Adiza, abinci a kawo wannan a Wauke wancan, sai yamma Turaki ya zo ta Waukeni, kafin mu koma Hostel ma wani wajen mu kaje.
Chapter 24 · 0% Book details