← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 50

Sashe 27

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina shiga Waki na kirashi, na shaida masa komai, ya ce gobe ma haka zamu sake, aikuwa hakan muka yi duk wata jarrabawa a haka muke karatunta kuma da an shiga Wakin jarabawa zata dawo min fes, har na samu na kammala jarabawa ta, a ranar na wuce dutse.

Ina sauka daga mashin a ™ofar gida Ra is ga fito da gudu kamar zai rugume ni, yana murna da kiran sunana, ya yan Yaya Radiya ma suka fito suna tsalle suna murna, wani irin daWi na ji ya ratsani, ganin yanda ake murna da zuwa na. Ra is ya Wauki akwatin muka shiga ciki, a tsakar gida muka tadda Hajiya gab da bakin ™ofa tana tsaye, bakinta a washe, ina ganinta wani daWin ya ™ara ratsani, na rugumeta tare da faWin.

Hajiyata.

Cike da farin ciki ita ma ra rumgumo ni tana faWin.

Nana sannu, sannu da zuwa.

Daga nan muka yi seat room, muna zama na ce.

Ina Yaya?

Kin manta ta yi aure.

Ra is ya faWa, na girgiza kai na ce.

Ni ba wanda ya faWamin, nasan dai ta sami aiki.

To ai sai bayan anyi auren ne, waWan nan ma sabida makatanta suke zaune, amma ana hutu suke komawa, sai ya ™are su dawo. Suna shiga junior za a sukoma can.

Allah Sarki, ai kuwa gobe ina gidanta.

Na faWa, Hajiya ta ce.

Hutu kuka samu ne?

Eyh Hajiya, hutun ma na kwana uku ne, amma sai na yi sati anan nikam.

Eyh gaskiyya dai kam, yakamata ki zaga yan uwa har su Hajja ma.

Ra is ya makarantar?

Yanzu zamu shiga final year.

Ma sha Allah, yanzu sai kun shekara kenan?

Eyh.

To ai duk a shekara Waya zamu gama kenan?

Eyh, ai ku karatun naku ne gudunsa ya yi yawa.

Tare kuke da Abubukar ne?

A a yana can kano dai.

Aiy to. Hajiya ta faWa, Ra is ya ce.

Ya kika ga kanon?

Kai Ra is ba haWi chaS.

Ya yi dariya, sannan ya ce.

Ai can zayi service.

Yakamata dai kaga kano, Hajiya naje gidansu Anty adiza wajen sau biyar.

Har biyar yar nan?

Eyh, Hajiya mutaneb arzi™ine na gaske.

Ma sha Allah, ai daga ganinta kinsa daga gidan manyan mutane take.

Sosai Hajiya.

Daga nan muka shiga hira kala kala, na basu wancan labarin, su bani nasu, har yamma muna haka, Yaya Ridwan ya dawo anan nake samun labari shima ya sami aiki, kuma wai duka shi da Yaya Radiya Turaki ya sama musu, kai ni ba abinda zance da Turaki sai godiya, ya yi namijin ko™ari akaina da yan uwana.

Washe gari na shirya fara zuwa ziyara, na zaga yan uwa, sabida bawani dogon zama zanyi ba, ranar farko na fara ta gidan Yaya Rumaisa, na ji daWin zuwa itama ta ji daWin yanda ta ganni, ta yi ta yabon kyan da na yi, ta kuma sanar dani sunyi magama da Dr Na ima Da™ayyawa ta sanar da ita labari mai daWi sosai da sosai, na kalleta sannan na ce.

Yaya wane labari ne wannan?

Ta yi murmushi sannna ta ce.

Su Hajiya duk basu faWa miki ba?

Na ce.

Eyh fa.

Ta ce.

To ki godewa Allah Nana, mahaifarki za ta iya Waukar Wa, amma kuma bawai da ssauri ba, kuma ba wai lallai duk zasu da rai ba, amma tabbas Nana mahaifarki zata haifar da Wa, Allah Ya duba zuciyarki ya ga baki nufin kowa da sharri.

Alhamdulillah Yaya, gaskiyya na ji daWi, kuma na yi wa Allah godiya.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na ashirin da biyu.

Akwai wasu magunguna da aka kawo miki kwanaki, kina amfani da su ko?

Eyh Yaya inayi.

To ai akwai wasu guda biyu da ta ce za a ™ara miki dasu, yanzu zan yi waya da ita sai a kawo kafin ki koma.

Tom Yaya, amma na ji daWi wallahi.

Ai daman Nana na faWa miki, a yanda baki da ha™™in Sardauna, Allah bazai ba shi damar cutar dake ba.

Kinsan yazo makaranta, amma na yi mai kaca kaca, sai kuma satin da zamu fara jarabawa na kama mai bawa fulawa ruwa yana min video idan Turaki yazo yana tura masa.

Lallai Sardauna masifa yake nema, wallahi Nana da badan wani abu ba, wallahi sai nasa anyiwa Sardauna kaca kaca da hula™anci.

Ki barshi kawai Yaya.

Ai na barshi, sabida Allah da bazai barshi ba wallahi.

Na ce. In sha Allah.

Daga nan, muka ci gaba da hira, sai yamma na tafi gidan Anty Adiza itama mun sha hira sosai, ta faWamin yanda yan gidansu suka ji daWin zuwana, nima na yi mata godiya da karamcin da suka yi min, har dare ina can sai da mu ka gaisa da mijinta wanda na daWe ma ni bangansa ba, daga nan na dawo gida.

Washe gari na fara ta gidan Yaya Radiya, ita ma na yini a can muka sha hirar yaushe gamu, sai kuma na ji gidan Hajja da Hajiya ta takura, ban wani jima ba na dawo gida.

Washe gari na je gidansu Fauziyya da Amina aminu, suma mun sha hira kowacce ta yaba da canjin dana samu, a haka na dawo gida na cinye hutu. Ina komawa makaranta muka sake shiga karatu ka in dana in, muna tsaka da karatu Turaki ya kammala course Win ya tafi, amma yana ™o™arin zuwa duk bayan sati biyu, zancen aurensa dai abu yana ta kankama, dan a yanzu na sa shi ya yi min al™awarin bazai Soye min komai ba, duk da ina jin ba daWi, amma na faWa masa zan kasance kai bashi ™warin gwiwa akan komai. Hakan ya sa ya daina Soyemin, kuma abun mamakin shine yanda yarinyar take i™irarin tana son sa amma har yau ta™i bare magana ta haWasu ko ta minti Waya ce, iyaye da yan uwa kam sun dage akan maganar, ni kuma na ™arfafashi akan ya yi musu biyayya.

Sardauna dai ban sake bari na haWu da shi ba, yana garin baya garin ni bansan masa ba, sannan ban sake haWa ido da mai bawa fulawa ruwa ba, karatu na nake yi a hankali cike da nutsuwa, a lokacin da muka kammala aji na biyu, zamu shiga na uku aka sanyawa Turaki ranar aure da matar Islaha, ranar na yi yinin Sacin rai da damuwa, duk da Turaki bai taSa ce da ni Nana ina sonki ba, amma ni dai nasan zuciyata ta kamo da son Turaki, so mai girma, wannan son a cikin zuciyata nake jin shi tare da bugun numfashi na, ba wai a cikin kwanyar kaina ko ™wa™walwata ba.

Wata uku aka sanya komai da komai, a ranar ban iya kiran Turaki ba, kuma ban iya Waga kiran da ya yi min ba, duk yadda nake danne zuciyata nake ™arfafa mai gwiwa, a wannan karon na kasa ™arfafa tawa zuciyar, sai washe gari ya kirani, ba yadda na yi na Waga wayar.

Nana.

Ya kira sunana, ban amsa ba na ce.

Salamu alaikum.

Ya masa da.

Wa alaiki salam, Nana.

Na am.

Na amsa cikin sanyi murya.

Ki yi ha™uri.

Da me?

Da abinda ya faru Nana, ba a sona ba ne kinsan komai.

A take lokacin da Sardauna zai auri Bilkisu ya ce da ni ba a son ransa ba ne ya dawo min tarwai.

Me ya sa duk maza suke hakane?.

Na tambaya a zuciyata, sai dai ya bani amsa a fili, ya ce.

Nana, ba duka maza ba ne Waya, kowa daban yake. Kanar yadda kowacce mace take daban, halinta daban, kammanninta daban, haka maza suke, a baya Sardauna ya yaudareki da cewa ba da son ba ya yi aure, nima a yanzu na faWa miki, nasani Nana abubuwan zasu ke zuwar miki wasu kala dabab, amma ki yarda da ni sa zuciya Waya da gaske nake miki Nana.

Sardauna ya kashe min zuciya, ta hanyar da bana iya yarda da kowanne irin kalaman soyayya, ta hanyar da duk wasu kalamai zanji su a ™arya.

Nana ba ™arya nake ba, Ni Abubukar Turaki gaskiyya nake faWa.

Yaushe ne auren?

Nana na faWa miki wata uku ne.

Allah Yasanya alheri ango.

Ango Nana ba.

Ya faWa yana dariya, na ce.

A a, angon islaha dai.

Idan ba Nana ba sai rijiya.

Na yi wata dariyar takaici, a lokacin na tuna nima fa haka na ce.

Idan ba Sardauna ba sai rijiya.

A fii na ce.

Allah Sarki.

Me ya faru?

Ya tambaya, na ce.

Bokomai.

Kin ha™ura?

Dame wai?

Komai ma.

Eyh, na ha™ura.

Da zuciya nawa?

Sai da na yi dariya sosai, sannan na ce.

Dubu.

Shima ya yi dariyar ya ce.

Ai baki ha™ura ba, da zuciya Waya shine kin ha™ura.

To da rabin zuciya ma.

Uhm, wai kwana biyu babu wani update ne a makaranatar ku?

Sai da na yi dariya, sannan na ce.

Babu ko Waya.

Ina wannan me jan idanun?

Tana nan.

Ta sake yin aljanun?

Dariya na saki, sannan na ce.

Daman kana nan ta yi?

Ina nan mana, kawai ta zubewa mutane a ™asa.

Na yi dariya sannan na ce.

Bata sake ba.

Amma dai ba kya kulata, kar ta goga miki ta ja min masifa.

Suma Allah ne ya Wora musu.

A a Nana, sau nawa ina ganinta anan wajen, har da daddare ma wani lokacin haka take fitowa ko Wankwali babu, ai ina nuna miki ko?

Eyh.

To kinga, ya zaayi ki ce haka, gashi kullum fuskarta da kwalliya, kuma duk kayan kiran mutanen Soye ne, har da daddare fa ba ta wanke fuskarta, wa ya yake sallah ne?

Na yi dariya, sabida yanda ya ™are maganar, sai da na yi sasai sannan na ce.

Ni bansani ba, amma ranar ta ce idan ta yi wannan attach Win da kwalliya sai lokacin da take al ada ne, ba ta yin sallah shine take wannam gayun.

Kinga kuwa dole sheWanu su kamata, ga najasa a jikinta, ga ta ™ara wata najasar, kuma wannan ma ai ba tarbiyar addinin musulunci ba ne Nana, ki duba fa yanzu duk wata ta ganta a wannan shigar tasan a yanayin da take, baga maza ba, ba ga mata ba.

To haka dai ta faWa, ya zaayi mata to?

Allah Ya tsare mana ku.

Na ce.

Amin.
Chapter 27 · 0% Book details