← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 50

Sashe 48

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shine, neman uban me yake miki?

Le™a da kanka, ji yanda yake abu kamar mahaukaci.

BuWe ™ofar ya yi, Sardauna ya yi wani tsalli ya shigo, yana zuwa ya zube a ™asa ya fara cewa.

Nana, Nana, ki taimakamin dan Allah, zan rasa raina, wallahi Nana ko minti Waya bana iya yi sau na kira sunanki, idan naganki zuciyata wani bugu take yi da ™arfi.

Ni gaba Waya ma tsoro ya bani, na fara ja da baya, ya yi ™o™arin ri™e min ™afa, na ™walla ™ara tarw da faWin.

Habiby.

Turaki ya yi kaina, yana cewa da Sardauna.

Karka firgita min mata, ka fita anan.

Nana dan Allah.

Ka fita na ce ma.

Turaki ya sake faWa, ni kuma na ™ara ru™un™umeshi ina faWin.

Habiby dan Allah ya fita, ni tsoro yake ban, kar ya dake ni.

Akan me zai dake ki, Sardauna fitar mana.

Nana wait, ki taimaka dan Allah, wallahi ina sonki, ki yi ha™uri dan Allah.

Karka ™ara cewa kana son matata, tun da baka da hankali.

Turaki ya faWa tare da jan shi, ya dinga jan Sardauna har sai da ya fita da shi, yana fita dashi ya dawo ciki ya rungume ni, ni kuwa na fashe da kuka, har ga Allah abun Sardauna yanzu tsoro yake ban, mussaman Wazu da naga idanunsa suna wani irin ja, gashi yanzu ma yazo nan, ni ko wani makircin ma ya shirya tin da shi lamarinsa babu Allah.

Habibty ki yi ha™uri, zanyi maganinsa.

Nifa tsoro yake ban, Wazu m zanje asibiti ya dinga ri™e murfin motar, kar dai wani makircin yake son sa™e ™ulla mana.

To Habibty duk makircinsa ai sai da ya ha™ura damu, a yanzu fa mun riga da munyi aure kuma babu wani abu da ya isa ya raba mu, ko ™addara bana fatan ta rabamu Habibty.

Ni dai duk tsoro nake, ko gida zan koma, ko mutashi kawai mu bar masa nan?

Idan kina so Habibty sai mu bar masa.

Ya faWa daidai lokacin wayarsa ta fara ringing, ya zaro daga aljihu, ya kalle ni sannan ya ce.

Big Daddy.

Wani irin bugu na ji a ™irjina, mai kuma ya ce mu yi? Wane sharri ya ™ulla mana, tabbas tashinmu daga nan shine alheri.

Habibty kinga Big Daddy.

Nagani, ka Waga.

Šagawa ya yi, ya sata a hands-free Big Daddy ya ce.

Abubakar kana ina? Hajiyata ba lafiya yanzu zasu tawo daga abuja, ka shirya kaje ka Wauko su, idan jikinta ya yi tsanani ku kaita asibiti, idan ya yi very worst ka faWa min yanzu ku shirya ku tawo nan.

Tom Big Daddy, bari naje waye ya tawo da ita?

Usman ne.

Tom.

Ya faWa yana mi™ewa, nima na mi™e na ce.

Muje tare, bazan iya zama anan ni kaWai ba.

Okay sa mayafi.

Na buWe sif na Wau mayafi muka fita, Sardauna yana tsaye yana kai kawo a parking spaces mu ka shiga mota muka fice, daidai lokacin da muka isa airport daidai lokacin jirginsu ya sauka, muka sa ta a mota muka wuce asibiti, jikin na ta baiyi tsananin da za ace har an tafi wata ™asar ba, sai da kuma al amuran sa masu kuWi ba gane kansu ake ba, abinda bai kai ya kawo ba zasu ce sunje turai ganin likita.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na arba in.

Sai wajen ™arfe sha biyu da kwata muka bar asibitin mu ka dawo gida, sai a lokacin Turaki ya Wan sanar da waWan da yakamata ya sanar, washe gari ma na yi mana breakfast muka ci, sannan mu ka tafi asibitin, daga asibitin ya wuce ofis ya barni, kasancewar yan gidansu Turaki ne a wajen jinyar sai kuma yan uwan Sardauna ya sa ban wani damu ba, ™arfe sha Waya nima na wuce ofis.

Wajen ™arfe biyu na tashi daga ofis Win na yi gida, ina zuwa na dafa musu doya da miya na shirya na yi asibitin, lokacin da zan fita na ga Bilkisu ma ta shirya cikin yar iskar shigarta ta fita, a raina na ce. Mai hali baya fasa halinsa. A mota ta naje asibitin, ina shiga Wakin na tarar da Mommy, Mama Amina, da Mamansu Sardauna sai sister seemah, har da su Islaha, gaisuwar gaba Waya na yi musu na ce. Ina yinin ku?. WaWan da suka amsa sun amsa, waWan da basu amsa ba sun yi banza, ina zama Mama Amina ta ce.

Sannu da ™o™ari Nana, tun jiya kuke hidima asibitinan, Allah Ya saka da alheri.

Na yi ™asa da kaina bance komai ba, Sister Seemah ta ce.

Ai Mama Nana kam ba daga nan ba, a yanzu zamu ce ta canja, tana da kirki tana da son mutane, ba kamar baya ba.

Ai ina ga a bayan dama ce ba ta samu ba.

Lamrah ta gidan Big Daddy, ™anwar Sister Seemah ta faWa. Sister Seemah ta tare ta.

Waya sa da ke?

Bakowa Sister, kawai yanzu abun nata ya zama abun burgewa, har son zuwa gidan ta nake.

Ai kya so zuwa gidanta, tun da sa ar ku ce.

Mama Amina ta faWa, sai a lokacin Momy ta ce.

Sa ar su ce mana, dan Nana a shekaru ban jin ta haura 22.

Kunzo kun dame da zancen wata banza a waje, sai wani yabon ta kuke.

Mamansu Sardauna ta faWa, a take Hajiya Falmata ta cafe da cewar.

Abinda nagani kenan, yarinyar da bata kai ba sun zo sunsa zancen ta a gaba, ita wacca ma tana ta wani washe baki an yabi surikarta, sabida rashin kara da ta ido.

Mamansu su Sardauna ta ce.

Ai ni Hajiya Falmata, wallahi matar nan mamaki take ban, tun da ta amince Wan ta ya auri yar iska, ko da yake shi ya Sata ta, wai amma yanzu su Amina sabida basu da kunya sun manta yanda muka zauna muka tsaya tsayin daka akan kar aka sake kawo mana wannan yarinyar cikin family, shine yanzu suka zo suke yabonta.

Mama Amina ta ce.

Ai ba a sanin halin mutum sai an zauna da shi, anan da kowa ya yi tunanin Nana yarinya ce marar mutunci marar tarbiya, duba da ko shiga yan uwa ba ta yi, ba ta zuwa gaida iyaye, ga miji yana ta ™ofarinta, amma a yanzu da ta yi wani auren gashinan duk halinta yana fitowa, kunga kenan idan aka yi duba za a ce daga Sardauna ne, tun ga amaryarsa ta yanzu nan, babu inda take zuwa.

Kya faWa mana, kuna zaune da matar da ta yi iskancin da ™anin mijinta, bayan da aure akan ta, sabida ba kwason gaskiyya, shi Turakin yana sakar muku abun duniya.

Mamansu Sardauna ta faWa, Sister Seemah ta ce.

Haba Momies mene haka? Me Turaki yake da shi? Dan Allah a iya baki, ™age da ™azafa babu kyau, akwai abubuwan da idan aka ce za a baje su ba kowa bane zai iya Wauka, Nana ce ake magana akai, da bata da zumuncin, bata son yan uwan mijinta, a yanzu kuma ta canja, shikenan.

Ke rufe mana baki, tun da baki da kunyar da zaki iya shiru idan iyayenki na magana muma muna da bakin da zamuyi magana.

Kar ki yi min rashin kunya Alisha.

Ke ba daWi kika sa baki a maganar iyaye?

Yanzu jinyar Hajiyar zakuyi ko yada magana?

Mommy ta faWa, daga nan kuma aka yi shiru, kowa ya ja gefe ya ci gaba da abinda yake, Hajiya Falmata da Mamansu Sardauna suna ta haWe kai suna hira ™asa ™asa, ni dai ina zaune jira nake kawai Turaki ya zo ya Waukeni mu tafi, dan zaman ba daWi ba kwata kwata, ana haka Sardauna ya shigo, yana shigowa na kauda kai na yi gefe, ya shigo suka gaggaisa. Sister Seemah ta ce.

Bross mu yi magana.

Ta faWa tana ta shi yabi ta suka fita, sai da suka kwashe kusan mintuna goma sannan suka dawo, yana ta haWa gumi, a raina na ce. Allah yasa ta faWa masa cewar Islaha na da cikinsa, ko za a samu zuciyarsa ta buga. Sai wajen bakwai Turaki yazo, yana zuwa na matsa kusa da shi na ce masa.

Dan Allah mu tafi da wuri.

Ya gyaWa min kai kawai na koma na zauna, ba mu muka tafi ba sai bayan takwas duk na gaji, muna zuwa gida na kwanta ban ma kula shi ba, duk yanda Turaki ya kaWa ya raya na™i kulashi, gaba Waya bana jin daWi. Washe gari kam shi na bawa abincin ya kai, ni na™i zuwa. Ko da na tashi daga asibiti ma ni banje ba, gida na dawo. A ranar kam naga zallan Sacin ran Turaki, ina zaune a falo ya shigo, sallamar ma a zuci ya yi ya wuce ni, na mi™e ina faWin.

Sannu da zuwa.

Ya yi banza ya shige ciki, na bi shi ina faWin.

Me ya faru Habiby?

Habibty kin kyauta? Kakata, mahaifiyar Abbana, abinda kika yi kin kyauta, ace daga jiya anyi miki abinda bai miki daWi ba shine zaki ™i komawa.

Ka yi ha™uri dan Allah.

Ha™urin me? Tun da abinda kika zaSa ai shikenan.

Jikina ya yi sanyi, na fara kuka amma Turaki ya yi banza da ni ya wuce Waki. Ba shiri na tashi na bishi Waki.

Habiby, dan Allah ka tsaya ka saurareni.

Habibty me zan ce miki? Me zanyi miki, kin yi fushi kin daina zuwa ba shikenan ba, so kike na tursasaki?

A a, ba zaka tursasa ni ba, yau Win ne bana jin daWi kwata kwata, dan Allah ka yi ha™uri.

Habibty dan Allah je ki, jeki Wakinki.

Ni kake cewa na tafi?

Jeki.
Chapter 48 · 0% Book details