← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 50

Sashe 3

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga wannan rana na Wauki al™walin duk wani abu da zan faranta ran Sardauna shine zanyi, wanda zai ba™anta ransa ba zanyi ba, na rage rayuwa a Sangarena gaba Waya da zarar Bilkisu ta fita zan dawo nan na zauna, wani lokacin ma yana bacci take fita, sai na je na yi masa girkin yake tashi ya ci ya shirya ya fita, ni zan gyara idan suka Sata amma banda Wakin baccinsu daban bazan iya shiga ba, amma ko ina nakan gyara, na yi girkin rana na ci ni kaWai, dan Bilkisu kullum sai biyar da rabi take dawowa, shi kuma sai gab da magariba, gashi gaba Waya ya daina wannan fitar majalisar da ya dawo ta dawo zasu shige ciki sai kuma da safe.

Turaki kuwa bansake bari na haWu da shi ba, dan ba inda ma nake fita, wayata ma gaba Waya na tarkata ta na ajiyeta, babu wani abu da nake yi a yanzu, kullum ina cikin Waki.

*********

Yau takama Asabar, tun da Sardauna ya sake aure ya daina fita ranar asabar sai yamma, ita kuma ba ta zuwa makaranta asabar da lahadi, tun safe na shiga Samgarensu yin ayyukana na kullum, dan tunda na yi shawara da zuciyata na yanke zan dage tu™uru na yi duk abinda Sardauna zai so ko zai ji daWi, nasan idan ya ga ina yi masa biyayya tabbas zai dawo da kallon sa yake yi min na sanyin idaniyansa.

Aiki nake tu™uru ganin na yi musu cake da shayin na a na a, nasan Sardauna zai ya ba kuma zai ji daWi sosai da sosai, kamar daga sama na ji muryar Bilkisu.

Me yake ™auri ne haka?

Ta faWa tana shigowa kicin Win, kallona ta yi sannan ta ce.

Yanzu dan ba™in ciki Nana me kike babbakamin haka? Kayan nawa zaki lalata muguwa? Baby!

Da mamaki nake kallonta, ko me ta gani ya yi kama da za a lalata oho mata? Jikinsa har rawa yake ya shigo cikin kicin Win, da sauri na tsugunna ™asa tare da faWin.

Ina kwana?

Baby kaga abinda take yi, so take talalata mini oven.

Bilkisu ta tare masa numfashi ba tare da ta bashi damar amsamin ba,ban daddara ba na sake cewa.

Ina kwana?

Ke dalla bama son surutu, abinda ake magana akai kenan?

Bilkisu ta ™ara faWa, yayin da Sardauna ya kau da kai kamar bai jini ba, ko bai gani ba.

Muje na nuna miki wani abu.

Ya faWa yana ri™e mata hannu, ta saki wani ihun.

Ah! Baby ai bazan iya tafiya ba, jikina ciwo.

Šaukarta ya yi a hannu kamar wata jaririya ya fice da ita, ™walla ta fara zirara daga idanuna, ba™in ciki da takaici suka haWu suka ™unsu a zuciyata.

Allah ka sakawa Sardauna akan abinda Bilkisu ta yi masa, Allah ka bi masa ha™™insa.

Na faWa ina share ™wallar da ta fito daga idona, na ci gaba da aikina tare da hira da zuciyata, kalaman Sardauna suka shiga dawo min a kunnena kamar yanzu ya faWesu.

Nana ina so ki ci gaba da yi min uziri akan komai na rayuwa.

Allah Sarki mijina, ina sonka, Allah Ya kare ka, Allah Ya dawo min da kai, Allah Ya yi maka arzi™i marar iyaka, ina sonka Sardauna.

Daga nan na ci gaba da abinda nake yi, har na kammala ban sake jin wani motsin Sardauna ko Bilkisu ba, ina gama na fito da su zuwa kan dinning Win Bilkisu na ajiye, bayan na Webi nawa da zanci na yi nawa Sangaren. Ina shiga na zauna akan kujera, ban wani iya ci yadda yakamata ba na hau gyaran Sangaren nawa, sai a lokacin tunanin nawa kayan Wakin na can gidanmu na farko ya faWo min, ko suna ina oho? Da dai Sardauna ya ce za a bada su, ko an bayar Allah masani.

Tun daga can Sangaren nasu na ji ana ta ™walamin kira.

Kee! Kee Nana!

Jikina har Sari yake na fita zuwa falon nasu, suna zaune akan dinning suna cin abincin, wani tausayin Sardauna ne ya faWo min a rai, tabbas da nice da bazan bar Sardauna ya zauna haka ba, ni da kaima zan bashi komai a baki, wani haushin Bilkisu ya kamani kan abinda take yi, gaba Waya ba ta iya biyayyar aure ba, iyayenta basu wani ba ta tarbiya ba.

Zo nan.

Sardauna ya faWa, a hankali na taka zuwa inda suke.

Mene wannan kika dafa? Bilkisu ta ce ba ta iya ci ba.

Duk abun babu taste Baby.

Kallon Bilkisu da ta yi maganar na yi, ni a yanzu haushinta da nake ji gaba Waya na yadda kwata kwata ba ta iya kula da Sardauna ba, abun ta gaba Waya babu biyayyar aure, kuma nasan Sardauna ba wai sonta yafi ba, kawai ita amarya ce.

Nana! Na yi wata shawara, ganin a yanzu ni dake babu aure a tskaaninmu, kuma bake ce matar gidan ba dan haka dole zan banbantaku da matar gidan ta dole.

Tom.

Nana, duk wasu kayan Waki zaki cire na cikin Wakinki, amma za abar na Wakina sabida idan maganannun yayunki sun zo sai ki nuna musu na Wakina, sannam zaki bar kujerun amma Nana inda ke kaWai ce ban lamunce miki zama akansu ba, Wakin ki zaki bar katifa kawai, kayanki kuma zaki barsu a akwati a ™asa, Wakin zai zama daga katifa sai akwati, idan kinyi ba™i sai ki kaisu nawa Wakin kuma ba kowa bama, ku ™araci zamanku a falo, kin jini?

Na gyaWa kai sannan na ce.

Eyh na ji.

Yawwa, daman kayan duka mallakina ne, dan haka za afita da su a yau.

Sannan ba zaiyu ace ni matar gida ina sa kaya na kece raini ba, ita tama tana sawa dole asan yadda za ayi.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na uku.

Kallon Bilkisu na yi, bansan me ya sa ita nake jin haushin duk abinda ta yi ba, amma Sardauna kome zai faWa ina yi masa uziri, a yanzu haka nasan bayin kansa ba ne, kuma nasan ba zaiyi haka dan ya cutar da ni ba.

Kike kallona da idanu kamar mayya.

Bilkisu ta faWa a tsawace, na watsa mata harar sannan na ce.

Bazan yi ba, wallahi ba zan zauna babu sutturu ba.

Lallai yarinyar nan wuyanki ya yi kauri, to wallahi Allah sai kin sauya shigarki, Baby ka ji fa.

Baby, ba ta da wasu kaya masu tsada, kinsan dai daga inda ta fito dan haka bana ganin hakan zai dameki.

Cuno baki ta yi gaba, sannan ta ce.

Zuciyana tashi take idan na ganta fa, yanzu haka ma amai nake ji.

Tashi ki bar wajen nan, ki fitar da kayanki daga sif yanzu, ki sauke katifar ma.

Ba musu na tashi na nufi Sangarena na barsu anan, ina shiga na samu waje na zauna.

Wai shin me ya sa Sardauna yake min haka ne?

Na tambayi kaina, sai kuma wani tunani ya faWo min. Sardauna Wan Adam ne, ajizi me yawan laifi ina ganin bai kamata na zargeshi ba, tunda tabbaa a baya Sardauna yana sona kuma ya nuna min soyayya, dan haka dole ni ce na yi abinda ya ja Sardauna yake min haka tabbas?

Amma me na yi masa?

Na tambayi kaina, can kuma na girgiza kaina.

Nima bansaniba, amma tabbas duk abinda ya ja haka laifi na ne dole, dole ma.

Shiru na yi, na shiga kiciniya da ™wa™walwata ko zan iya tuna wani abu da na yi wa Sarauna, sai dai na garara tuna komai, sai ma ™o™arin tunawa da Dr Na ima Da™ayyawa da na yi, tabbas ta faWa min wani abu, amma gaba Waya na kasa tuna abinda ta faWa min, haka na yi ta faman kwance kwance da Waure Waure a cikin ™wa™walwata amma nakasa tuna komai.

Nana!

Na ji andaka min wata razananniyar ™ara, azabure na juya na kalleshi.

Abinda na ce miki kenan? Kin raina ni ko?

A a.

Na faWa ina jijjiga kai, ya matso a fusace yana wuci kamar zaki.

Wallahi Nana sai na SaSSarar dake, idan baki daina min wannan haukan da kika gada ba, shashasha da ba tasan ciwon kanta ba.

Yana faWin haka ya Waukeni da wani azababben marin da sai da naga taurari sun gifta.

Ka yi ha™uri zanyi.

Ina ma da lokacin jiranki kenan? Masu kwashe kayan suna waje suna jira, shine zaki wani ce na yi ha™uri? Na ™i.

Ya faWa yana nufar sip Win, a fuskata na ji ana watsomin kayan wasu kuma na zubewa a ™asa, yana watsarwa yana faman faWa, ni dai ina tsaye na zubawa Sarautar Allah ido.

Wallahi idan baki sauke katifar ba, idan suka zo har ita zasu haWa, sai kina kwana a ™asa daman anan kika saba.

Da sauri na juya, na yi ™asa da matashin da kuma bargo da zanin gado, na fara kiciniyar sauke katifar sai dai gaba Waya tafi ™arfina ko kusa ko alama, da dukkan ™arfina nake Waga katifar ina yi ina nishi, amma ko jikin Sardauna, waya ma ya tsaya yana dannawa bayan ya gama zubar min da kayan ™asa, har da sarko™i na da Wan kunne duk ya watso su ™asa.

Ku shigo ku kwashe kayan.

Ya faWa bayan an Waga wayar da ya buga, sannan ya juyo ya kalleni.

Karki sauke, wallahi da ita zasu tafi.

˜ara dagewa na yi da dukkan ™arfina, cikin ikon Allah na yi wani irin nishi kamar mai na™uda na Wage katifar, cikin rashin sa a ™asan siket Wina ya harWe da katakwayen gadon, ina tafiya na ji kamar an janyoni bayan an maka ni da karagar gadon, na buge goshi na, hannuna kuma ya yi wata karciya mai azabar zugi, wadda sai da na saki ™aramin ihu, daidai lokacin kuma suka shigo na mi™e ba tare da na ci gaba da jin zafin faWuwar ba ko karcewar, ganin samarin guda huWu kuma uku ne suke ™o™arin Waukan sif Win, Wayan yana tsaye ya sa na yi masa magana.

Bawan Allah, dan Allah kama min na sauke katifar nan.

Tom Hajiya.
Chapter 3 · 0% Book details