← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 50

Sashe 10

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya gyaWa kai, na sanyayar da muryata sannan na ce.

Ka yi ha™uri ka ji.

A a.

Ya faWa ba tare da ya waigo ba, kamar zan yi kuka na ce.

Ba zan sake ba Sardauna.

Ya ™ara girgiza kai, sannan ya ce.

Ki je bacci zanyi, anjima zan ci.

Mi™ewa na yi na fito falo daidai lokacin kuma na ji ana buga ™ofar part falon nawa.

Waye?

Nana Yaya Radiya ce ki buWe.

Wani irim tsoro da fargaba ne suka kamani, ga Sardauna a gida baya son ya ga kowa ya zo wajena, gashi kuma Yaya Radiya ta zo kuma ya ce baya son hayaniya. ˜ara buga ™ofar akayi sannam ta ce.

Wai bazaki buWe ba ne?

Zan buWe, ina zuwa abu nake ajiyewa.

Na faWa tare da nufar ™ofar, daidai lokacin Sardauna ya kira sunana.

Nana.

Na waigo na kalleshi, sannan na ce.

Na am.

Zo.

Ya faWa yana yi min alama da hannu, fasa ™arasawa na buWe ™ofar na yi, na juya wajensa.

Kar ku yi hayaniya bacci zanyi.

Tom.

Na faWa shi kuma ya koma ciki, na nufi ™ofar na buWe. Kallona ta yi sama da ™asa sannan ta ce.

Da uban me ya hanaki buWewa?

Legendspen

08129553971.

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na takwas.

Sosa ™eya ta na yi, sannan na ce.

Bokomai Yaya, ina kwashe abu ne fa a ™asa ke da wa?

Ni kaWai.

Ta faWa tan zama.

Sannu da zuwa Yaya.

Yawwa sannu, ya gidan?

Lafiya ™alau Yaya.

Na faWa ina zama kusa da ita.

Mijinki yana nan? Tare muke da Ra is kuma ya ce bazai shigo ba sai mijinki baya nan.

Yana ciki amma bacci yake yi, ya shigo mana.

Bari na gaya masa.

Ta faWa tana mi™ewa, bayan ta fita nima na koma na ™ara jan ™ofar Wakin da Sardauna ya shiga sabida kar su yi surutu da ™arfi ya tashe shi.

Ban daWe da zama ba suka shigo ita da Ra is, fuskarsa a haWe kamar zai daki wani.

Ra is kai kuma lafiya?

Zama ya yi akan kujera, sannan ya ce.

Ai na Wauka zan tarar da shi mijin naki anan ne.

Murmushi na yi sannan na ce.

Ka dai yi magana a hankali, bacci yake kuma bana so ya tashi yanzu.

Kya ji dashi, muma ba zama ya kawo mu ba.

Yaya Radiya ta faWa, ni kuma na mi™e ina cewa.

Bara na kawo muku abinci.

Da kin barshi dai.

Sai da na shiga na Wauko musu kayan snacks da nake da shi na kawo musu, sannan na zauna. Sai da Yaya Radiya ta kalleni sosai sannan ta ce.

Ni zuwa fa na yi nai miki faWa, amma kuma Nana yanayin ki ya nuna damuwa sosai da sosai.

Kallon jikina na yi sannan na ce.

Ba wata damuwa wallahi Yaya, me kike gani.

Kinyi zuru-zuru, idonunki sunyi ja, ™asan su kuma ya yi ba™i! Nana kamar wacca ke kuka ko yaushe.

Yaya Radiya ta faWa, na buWe baki zanyi magana Ra is ya tare ni da cewa.

Ta yi wani kala ma, kamar a tsorace take.

Sai da na kalleshi na yi murmushi sannan na ce.

Ko Waya fa, ina zaune zaman lafiya.

Ina amaryarki?

Yaya Radiya ta faWa, shiru na yi sai can na ce.

Tana nan, ni dake ba shiga al amuranta nake ba, na kwana biyu banganta ba ma.

Matsowa kusa dani ta yi, tare da kama hannuna.

Nana, idan kina da wata damuwa ko matsala dan Allah ki faWa mana, Nana mune yan uwanki, Nana mune dolenki, Nana duk wani daWi da Wa namiji zai baki wallahi a baki ne Nana, a iya fatar baki ne Nana, ba zai kai yan uwa a wajenki ba, Nana munyi kuskure a baya, munyi kuskure mai girma da mu ka yi shawarar fita daga dukkan al amarinki, muka ™yale ki, muka sallamawa miji ke, tabbas a yanzu mun gane babban kuskuren da muka aikata.

Daidai lokacin wayar Yaya Radiya ta fara ringing, Waukota ta yi daga jaka tana duba, sannan ta Waga tare fa faWin.

Rumaisa.

Kasancewar wayar na Hands-free yasa ake jin muryar Yaya Rumaisan.

Yaya Radiya kun ™arasa? Sai yanzu na fito daga theater.

Eyh Rumaisa! Ga mu a gidan.

Yawwa tho Yaya, bata wayar.

Mi™amin wayar ta yi nasa hannu na amsa, ina amsar wayar na ji ashe Wazu Yaya Radiya rarrashi na take, yanzu ne aka zo kan gaSar maganar.

Rawasiyya.

Ta faWa a fusace, ita daman kullum zuciyarta a kusa take.

Na am!

Na faWa muryata na rawa.

Ke dan uwarki ki buWe baki ki yi min magana, kafin kisa na ™araso gidan na yi miki Wan banzan duka.

Na am!

Na sake faWa.

Nana! Nana! Sau nawa na kira sunanki?

Biyu.

Na faWa kamar zan fashe da kuka.

To wallahi karki bari na kira na ukun, da bazan kirashi da ko Wigon alheri ba, idan ada munyi sakaci mun barki da wancan mahaukacin mijin naki, to yanzu mun farga, ba zamu barki da shi ba zamu dage ta ™arfi ta tsiya akanki, idan ba ya ™aunar zaman lafiya, to nina fishi, idan tashin hankali yake so ni nafi shi.

Ni gaba Waya ma bangane akan me take magana ba, kawai masifa, ™ara da hayaniya nake ji.

Rumaisa, ai bamu kai ga faWa mata sharaWan da muka zo da shi ba.

Yaya Radiya ta faWa bayan ta ™arSi wayar.

To kuma dai kuka sani, ni dai a yanda nake jin zuciyata hakan nan ko Sardaunan tsaf zan iya marin mitsiyaci.

Ki yi ha™uri ki dinga kai zuciya nesa.

Ai da ha™urin ake cutar mutane, Yaya idan ba zaki iya faWa mata ba ni fa yanzu zan iya zuwa.

Kina da matsala Rumaisa, duk ki rikita komai.

Katse wayarta ta yi ba tare da ta bawa Yaya Radiya amsa ba. Kallona Yaya Radiya ta sake yi sannan ta ce.

Nana! A baya kamar yadda na faWa miki munyi sakaci akan ki, mun barwa namiji ragamar komai sabida idan ya yi mana rashin arzi™i muna ha™ura, sannan kema da anyi abu zaki ruWe ki fara kuka, to Nana a yanzu ya ™are munje matakin da ko sakin ki zai yi to sai dai ya sake ki Nana.

Saki Yaya?

Na faWa idona yana tara ™walla, Ra is ya matso kusa dani sannan ya ce.

A a fa, bawai cewa akayi ya sake ki ba, tana nufin idan ya nuna rashin arzi™in da yasa ba, ke kuma ki dinga cewa ke Sardauna kaza ke Sardauna kaza, to mu dai duk hukunci da muka yanke shi zamu aiwatar, ya rage nake ki yi convencing nasa ya yarda ko kar ya yarda, Nana ba mu ce ki yi wa mijinki rashin mutunci ba, ko ki ™i yi masa biyayya, a a muna so dai mu faWa miki Miji biyayya ake masa, saSanin ke da kikewa miji bauta Nana.

Yaya Radiya ta ™ara da cewa.

Nana ni ba ruwana ma da kome za ki yi masa, amma akwai wasu ha™o™™i naki dake kansa, ki sani ba wai iya shi ka Wai yake ha™™i akanki ba, dan haka dole shima ya fitar miki da ha™™inki Nana, dan abun na shi ba hankali ba nutsuwa a ciki.

Na yi shiru ina kallonsu, ni babu wani ha™™i da nake nema a wajen Sardauna, bayan ci da sha da suttura, kuma yana yi min dan haka ni ba abinda nake bu™ata daban.

Nana ko ki so, ko karki so mu dai sai inda ™arfinmu ya tsaya, ko anfi mu kuWi ba afi mu zuciya ba.

Wani banzan kallo na yi wa Ra is, gaba Waya babu abinda ya kawo su gidannan banda su zo su haWa min fitina su tafi su barni, na ce musu ina bu™atar wani abu ne? Ko na ce musu baya ye min abinda ya kamata? Kawai neman haddasa min fitina a gidan aurena.

Nana ina so ki buWe kunne ki saurari duk abinda zan faWa miki.

Tom Yaya.

Nana, dole ki ci gaba da karatu wallahil azim! Kinji ma na rantse miki ko da ci gaba da karatun zai zama sanadiyar mutuwar auren naki baki Waya Nana.

A tsorace na Wago kai na kalleta, ™walla ta fara zirara a idona.

Yaya bangane ba?

Ban bu™aci ki gane ba Nana, amma dai ko ta yane dole ki faWa masa karatunki burin mahaifinmu ne, dan haka dole sai kin cika shi Nana, nauyi ne a kanki. Idan shi bai san darajar iyaye ba, to mu mun sani Nana.

Yaya ai ya ce zamu tafi Turai, kuma zanyi karatun acan wallahi.

Ra is ne ya ce.

Turan bogi? Ko Turan gangan? Nana Sardauna yana amfani da wautar ki ne kawai yana kiWima ki.

Ba haka ba ne Ra is, Sardauna baya ™arya bai taSa yi min ™arya ba.

Na tare shi, muryata na rawa har na fara zubar da hawaye, Yaya Radiya ta ce.

Idan ya yi miki ™aryar fitowa zaiyi ya ce Nana na yi miki ™arya? Nana wai akanki aka fara sone? Ko akanki aka fara aure? Duk kinbi kin kiWime akan wani mutum Waya.

Ni dai Yaya dan Allah abar maganar karatun nan, tun da ya ce zanyi a gaba zanyi.

Idan kuma lokaci ya ™ure miki fa? Nana kinsan yan ajinku yanzu sune Waliban ™arshen shekara, sune zasu gama digira a wannan shekarar da muke ciki, wannan wane irin zalunci ne Sardauna ya yi miki, karatun da kika ci shekarar farko ya datse miki, amma ke sabida kinfi kowa wauta kike ganin zai barki ki yi a gaba?

A fusace na ce da Ra is.

Kai Ra is ka kama bakinki, mijin nawa kake faWawa waWan nan maganganun.

Na faWa ki dake ni.

Shima ya faWa a fusace.

Ya isa haka!

Yaya Radiya ta daka tsawa, sannan ta ce.

Ra is ka yi min shiru, Ke kuma Nana maganar karatu an gama ta nan da sati Waya zan sake zuwa kuma duk hukuncin da yayanke dole ki sanar da ni, idan ya ce Eyh to shikenn, idan ya ce A a to nima zaki ga A a. Wallahi Nana sai na tafi dake gida, kin gama auren Sardauna har abada.

Da sauri na girgiza kai, ina kuka na fara cewa.
Chapter 10 · 0% Book details