← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 50

Sashe 40

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A a Turaki, kuje idan Allah Yaso zaku sasanta idan abun ya gagara, kawai ka dawo da ita.

Shikenan Mommy.

Ya faWa yana mi™ewa, su ma su ka mi™e duka muka fice, motarmu muka shiga suma suka shiga tasu, a yanzu ma bayan motar na shiga na zauna, ita kuma ta sake zama a gaba. Muna tsaka da tafiya Turaki ya ce.

Habibty, ya asibitin?

One month ya rage, ban ma san yaushe zan koma ba.

Monday ya yi ko?

Eyh ya yi.

Na faWa, sabida bana so aja hirar, zai zama kamar cin fuska ga Islaha, wacca ta rakuSe kamar ba ita a motar, a raina na ce.

Kina wahalal da rayuwarki, babu abinda zai sa Sardauna ya aureki, mussaman a yanzu da ya zama mijin ta ce.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na talatin da uku.

A haka muka ™arasa gidan, ya koma Wakin Islaha bansan yanda suka yi ba, ni dai fatana kawai kwana na ya dawo, cikin ikon Allah ya dawo muka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, Monday ta zagayo na koma asibiti, Turaki ke kai ni na dawo da kaina, tun da na koma sau Waya na haWu da Dr Aliyu, ko kallon arzi™i bai samu daga wajena ba, kuma bansake bi takan shi ba, haka ma Sardauna idan zan ganshi sai dai safiya, amma lokacin dawowa ta bana ganinshi.

Haka rayuwa ta fara tafiya a cikin gidan Turaki, hankali na kwance bani da wata damuwa, Islaha ta fita daga sha anina, nima na fita daga na ta, Sardauna ko kaWan bana ganinshi, Bilkisu ce ma kulluk da safe sai mun haWu amma ko kallon banza ba ta yi min bare na arzi™i, ita rayuwarta kawai take kullum tana waje, ta san ™ana nan kaya ta fita ta dawo a lokacin da ta so, masu aiki ne da ita sunfi kala biyar, hatta girki suke yi. Turaki kam soyayya kullum da sabuwar da yake zuwa da ita, kulawa ma ta daban, ba ruwansa da idon kowa, nuna min soyayya yake, a zamana na wata Waya zuwa biyu naga soyayya daga yan gidansu na ga bambamci da zaman gidan Sardauna. Yau ce rana ta ta ™arshe a asibiti tun sha biyu naga ma komai na tawo gida, ina tunanin na zarce gidanmu, ina tunanin na wuce gidana kawai, ™arshe na yanke hukuncin wucewa gidana.

Kasancewar a ™afa na shigo layin yasa na bi ta ™ofa maimakon gate, rana ta take ta buWe iya ™arfinta, haka na shigo part Wina, ina shiga na yi Wakina na shiga toilet na watsa ruwa, na fito na buWe sif zan Wauki kaya, sai da na ji sautin magana ™asa ™asa, har zan rufe na ji ance.

Islaha, idan baki raba auren nan ba sai dai mu yi ta rayuwa a haka ni dake.

Muryarta ™asa ™asa na ji ta ce.

Yaya Sardauna na rasa hanyar da zan raba auren nan, kaima ka yi shiru ka barni, bana so na Wauki ciki muna rayuwa a haka, da wane ido zan kalli jama a, Turaki dai ba abinda zai sa ya amshi cikin nan.

Nima ba zan ba shi ba, zan ri™e abuna, ki yi ™o™ari ki raba auren a satin nan, mu samu a Waura namu, nima na gaji da zama da Bilkisu, ina son na sake ta amma ko ido bana iya haWawa da ita, sai rashin mutuncin da ta ga dama take yi min, na girki, ba sannu da zuwa, ba zama a gida kullum tana wayo atiti, sai dare. Gashi ta cika gida da masu aiki kuma duk ni nake biya, gashi ta™i ta haihu kullum tana yawon kwararo.

Idan ka aureni komai zai kau, kasan yanda nake son ka, kasan al™awarinka akaina.

Islaha, aikin ki shine ki yi ta tada tarzoma a tsakanin zaman Nana da Turaki, naga har wata soyayyar munafurci suke yi, ranar nan sun kusa sa zyciyata ta buga, idan har baki kunna musu matsala ba, zan rabu dake na nemi wata hanyar, kuma zance cikin dake jikinki ba nawa ba ne, zance wani abu bai taSa haWani da ke ba, tun da ba hujja gareki ba.

Yaya Sardauna, zan yi, zan shiga zan fita, zan haWa da yan uwa ayi ta kunna mata bala i, har sai zaman gidan ya isheta ta fita dan kanta.

Idan kika yi haka ni kuma ba zaki yi sati ba sai na raba aureki da Turaki na aureki.

Da sauri na saki sif Win, tare da faWin.

Islaha sai dai ke ki bar min gidan nan, amma zama da Turaki da izinin manzan Allah yanzu na fara, kai kuma ba kishi ba, wallahi sai na ™ona ma zuciya.

Na faWa tare da dawowa kan gado na zauna, na zuba uban tagumi na rasa abin yi, al amarin Sardauna na daban ne, dole na dage kai da fata, tin da alhamdulillah tun shigowa ta gidan nan kullum Turaki sai y tashe ni sallar dare, sia da fa, kaina da shi da iyaye da yan uwa nakr ro™o, tun da na yi aure na manta da Sardauna, dan aganina ga tarin bu™atu me zai sa na kama suna Sardauna a gaban ubangiji.

Ji na yi wata ™aras. Tas.. tas.. tas. Kamar ana fasa abu, da gudu na fito falon na ga Islaha tana faman duka Tv Wina da taSarya.

Tanan kika biyo?

Na faWa tare da shiga cikin camera a wayata na fara mata hoto da video, a fili na ce wannan faWan da ilimi za ayi shi, zaku san Nana ta yi karatu me tsada, sai da na gama Waukan tsaf sannan na fito falon na kalleta na kawar da kai, sai da na ji kan kujera na zauna sannan na ce.

Ashe ciwon hauka ne ya tashi? Muna zaune da mahaukata.

Uwarki ce mahaukaciya.

Na saki wata dariya sannan na ce.

Au Falmata, na ga ni kuwa ta dinga hauka agaban big Daddy.

Allah Ya tsine miki Nana, wallahi yau sai naga gatanki.

Na mi™e tsaye sannan na ce.

Ashe zaki gatana, bayan ubangijin da ya hallice ni, Islaha bazan yarda ke ri™a™™iya ba ce sai kin fasa duk wani abu na nan, kinje kin fasa na Wakin ki, shine zan tabbatar da arzi™in ku sai naga tsakanin ni dake wace za a fara canjawa wasu.

˜arya kike yar mitsayata, zan je na fasa nawa ki gani cikin ™asa da awa 24 sai an canja min komai.

A raina na ce. Tafi jaka. A fili kuma na ce.

Ni kuma a ™asa da awa biyar zan a canja min komai nawa, shege kafasa muje zuwa.

Ai kuwa ta tafi da gudu ta yi Sangarenta, ni kuwa na bita a baya na laSe ta can na fara Waukanta hoto da video irin ba a san ina Wauka ba, ina gamawa na yi cikin Wakina, na Wau number Lamrah yar gidan Big Daddy ce, zuwan ™arshe da ™annen Turaki su ka yi har ita suka zo. Ina kira ta Wauka, na fara magana cikin muryar kuka.

Lamrah, dan Allah kuna da driver available, na kira gidansu Mommy duk wayarsu is nt reachable, na kira Turaki akashe, kisa driver yaje gidan ya ce musu su taimaka su zo nan, ba lafiya wallahi Islaha sai fashe fashe take ita ka Wai, ta fasa kayan Sangarena ta je tana fasa nata shigowa daga asibiti kenan, yanzu ina toilet na kulle kaina, tsoro duk ya cikani, dan Allah Lamrah da wuri.

Innullahi wa inna illahir raji un, yanzu ke kina ina?

Toilet.

Mama! Mama.

Naji tana faWa, da kuma sautin gudu alamar guda ta yi, ta cikin wayar na ji Mama amina na cewa.

Lamrah kin Waga hankali mene?

Yanzu Anty Nana ta kirani, wai a taimaka mata Islaha sai fashe fashe take a gidan, ta kira number su Mommy ba ta shiga, Yaya Turaki ma haka.

Subhanallahi, fashe fashen me? Šauko min gyalena.

Katse wayar na yi, duk sai na ji ba daWi na ruWa mutane, amma gwanda na nunawa Isalaha makirci, idan sharri take ji, ni kuma zan nuna mata na koyo ilimin rayuwa nasan yanda zan sa reshe ya juye da mujiya cikin ™an™anin lokaci, sai ta bar gidan, shi kuma Sardauna sai mu fafata da shi, wanda ya fasa Allah Ya tsinema uwarsa.

Daga nan na koma Sangaren Islaha, na tsaya ta bakin taga na ce.

Ai baki yi musu kaca kaca ba, kamar nawa, ko kina tsoron kar kuWin gidanku ya ™are akan siyan kayan ne.

Ai arzi™i ba zai ™are a gidan Ta ambo ba, sai dai ku naku da ba asan inda suke ba.

Gashinan nagani.

Na faWa tare da barin wajen, ina shiga Wakina na ji alamun shigowa, kusan a tare motoci biyun suka yi parking, ina jin sun shigo na fito da gudu, na faWa jikin Mama Amina ina kuka.

Nana nutsu, faWamin mene?

Kuka nake wiwi, ina nuna musu Sangaren Islaha, aikuwa suna le™awa suka ganta ri™e da taSarya tana make make.

Ke islaha! Kin yi hauka ne?

Mommy ta faWa, a tsorace ta saki abun hannunta, nasan a ranta mamakin yanda aka yi suka zo take, ni kuwa na ce baki ga komai ba, nima fa macece, kissa da kisisina ai sai dai na koya wa wani, zama da Sardauna na shekara uku ai sai dai na zama malamr koyar da makirci.

Me ya shiga kanki haka?

Mama Amina ta faWa, Lamrah kuma ta yo kaina tana faWin.

Anty Nana ki daina kuka, gamu munxo ba abinda zai faru.

Fitowa Islaha ta yi zuwa falona, idonta ya sauka a kaina da nake ta kuka.

Kunga kamar ta yi hauka, ni bana so ta fasan kayana.

Na faWa ina kuka, a fusace Islaha ta ce.

Uwar ki ce ta yi hauka.

Da sauri na tashi zan gudu, Lamrah ma ta kwasa gudu, a lokacin kuma Turaki ya shigo.

Innullahi me yake faruwa?

Jin muryarshi ya sa na tsaya.

Me ya faru, Islaha mene haka? Nana waye ya yi abun nan?

Gatanan.

Mama Amina ta faWa tana nuna Islaha, ya matso zai yi kusa da ita, Mommy ta ce.

A a, kar ka je kusa da ita fa, tsaya daga inda take.

Haba Mommy, me ta yi ne? Hauka ne?

Ya faWa yana nufar ta.
Chapter 40 · 0% Book details