← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 50

Sashe 26

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana, abubuwa da yawa su kan lalace, wasu su fashe fatsa fatsa, kuma a iya gyarasu har su fi baya kyau da ™arko. Ni Abubakar Turaki na yi miki wannan al™warin, Nana zaki ji daWi, zaki san menene rayuwar aure, zaki yi farin ciki ki yi alfahari na har abada.

To wace katanga ya yi mana?

Nana ya sami hotona ni dake anan kano, ya yaWa su a yan uwa, sannan ya sa wata yarinya ta kunno wuta wai sona take yi, aure na zata yi, sai kuka take ma iyayenta, a rasa gane kan yarinyar, ta dage matu™a akan ra ayinta wai ta daWe da tana sona kuma aurena take so, ya yi amfani da waWancan hotonan ya nuna bibiyarki nake yi a wajen a yanzu, Sardauna ya Satamin suna a cikin yan uwa Nana, Sardauna ya zubar min da mutucina, shi ya sa na shiga damuwa sosai da sosai, ga babban abu ma yarinyar, Nana ban taSa sonta ba, kuma nasan ita ma haka.

Legendspen

08128553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na ashirin da Waya.

Gaba Waya jikina ya yi wani irin sanyi kamar an watsa min ruwa, na so ace Turaki yana gabana, sabida na yi kuka akan idonsa, wani abu na ji yana sama da ™asa a ™irjina, zazzafan abu me nauyi, ina zan sa kaina?

Nana! Nana.

Na ji yana kiran sunana ta cikin wayar, na yi saurin goge hawayen dake fuskata na ce.

Na am.

Kar ki yi kuka kinji, ko mai zai zo da sau™i.

Na rasa me ya sa ™addara ta take zuwa da zafi, na gama da ta gidan Sardauna, yanzu wannan shima tun kafin komai ya yi daidai zai a samu tsaiku.

Bansan ina maganar a fili ba, sai da na ji ya ce.

Ba haka ba ne Nana, komai da kike gani Allah ya tsara shi, bisa tsarin shi, kuma Allah Baya taSa Waurawa rai abinda bazai iya ba, duk wata jarrabawa da kika ga Allah Ya Wauro miki Nana yasan zaki iya ne, ki yi ha™uri ki mai da hankali ga karatunki, zan dawo in a satinan kuma zan maida ke can hotoro gidan yan uwanku, tun da nima course Win nawa yazo ™arshe Nana. A yanzu an ci kusan wata tara, kema shekarun naki sun fara tafiya na makaranta.

Eyh, yanzu jarabawar zango karatu na farko za mu yi a shekara ta biyu, daman haka bambamcin su pravite Win yake?

Eyh Nana, shekara biyu da wani abun zakiyi.

Yanzu yaushe zaka zo?

Nana, ina so mu yi magana da yarinyar ne ta fahimci ni.

Me ya sa ba zaka aureta ba?

Ya yi shiru na yan mintuna, sai can ya ce.

Dalilai da yawa.

WaWan ne dalilai.

Nana abu na farko bana son ta, kuma a yanzu na sake samun wani dalilin, ita ma ba sona take ba, ada na yi tunanin ko sabida biyayya zan aureta, ammma a yanzu na ji bazan iya ba Nana.

Kai Sardauna annamimi ne. Na faWa a raina a fili kuma na ce.

To, Allah Ya zaSa abinda yafi alheri.

Amin Nana, ki yi karatu sosai kinji.

Tom in sha Allah.

Muna gama waya na kira Yaya Rumaisa muka gaisa, sai dai ban faWa musu komai ba, har Ra is ma da muka yi waya.

Tun daga wannan rana bansake haWuwa da Sardauna ba, kuma ban bi ta kansa ba, mussaman a yanzu da exam ta kawo kai, na maida hankali ga karatu na sosai da sosai, muna magana da Turaki lokaci zuwa lokaci, amma kullum ya kance abubuwan sai addu a.

Yau na shirya zuwa gidan ™awata Malaika, ganin mun kusa gama exam, kuma muna gama exam gida zan tafi, dan tun da nazo banje ba, hutun da muke yi gaba Waya sati Waya kwana uku ne, amma dai a wannan lokacin na ce ko kwana Waya sai na je gida.

Ta whatsapp ta turamin location, kasancewar a yanzu nasan garin kano ba laifi, na Wau mota na tafi unguwar da take ShardaWa Quaters, ita ma dai unguwa ce ta masu kuWi, haka gidan ma da kyansa, mun yi hira sosai da sosai, ni kaina na ji daWin zuwa gidan mussaman da ta kalle ni ta ce.

Nana kinga yanda kika canja, kin koma rainon madara rarrafen kafet.

Na yi dariya, sannan na ce.

To Malaika, rayuwa ce shiru, ko magana sai ka yini ba ka yi ba.

Ai fa, duk ya yan masu kuWin nan yan iska ne, basa kula kowa.

Ai kuwa kamar ta soso mun inda yake min ™ai™ayi na gyara zama na ce.

Kinga Wakinmu part uku ne, to wacca ™ofarta take kallon tawa ce kawai muka taSa magana ita ma ina ga baifi sau biyu zuwa uku ba, ita waccan ta tsakiyar mu bamu taSa magana ba, hana ™arya dai munyi ranar da na fara zuwa.

Lallai Nana, haka kike zaman shiru?

Daga ni sai Turaki, yazo, ya kira ni a waya shikenan.

Waye Turaki?

Wannan cousin Win Sardauna fa.

Aouh, nagane shi kuna tare kenan?

Sosai ma.

Ta yi dariya sannan ta ce.

Allah Ya tabbatar mana da alheri, rabon ki sake komawa familyn su Sardauna ne.

Na yi murmushi kawai, ni nasan abinda yake faruwa kawai, daga nan muka shiga hira kala kala, sai wajen dare sannan na tafi, ina zuwa muka yi waya da Turaki yake sanar dani gobe yana hanya, ba ™aramin daWi na ji ba da zuwansa.

Kasancewar a yanzu bama lectures tun da an fara jarrabawa, mu yan dept Win mune ma bamu fara ba sai sati na sama, hakan ya sa yanzu bana ta shi da wuri, wajen ™arfe sha biyu na rana kiran sa ya tashe ni, na Waga wayar ina faWin.

Salamu alaikum.

Bacci kike?

Na ce.

Eyh.

Gani a harabarku.

Ba shiri na mi™e, tare da faWin.

Ina zuwa.

A gurguje na watsa ruwa na shirya na fita, yana inda yake parking Winsa tun da ya kawo ni, anan yake tsayawa, ya yi wani irin kyau mai sanyi, sai na ga kamar wani sabo dal aka fitar daga kwali.

Fuskarsa har wani she™i take na daban, har na ™araso kusa da shi ina kallonsa.

Na canja?

Ya faWa yana murmushi, nima na yi murmushin sannan na ce.

Sosai kam.

Kema kin canja, kinyi kumatu, wane mai kike shafawa naga kin fara haske.

Caro Ac.

Na faWa tare da tuntsirewa da dariya, shima ya tuntsire da dariya, ina son kasancewa da Turaki sabida indai ina tare da shi ina jin dukkan damuwata ta goge, na kan ji zallar farin ciki ya mamaye ni.

Ya exam.

Monday zan fara, kuma ina son naje gida wannan hutun.

Hutun zai kai sati ne?

Na girgiza kai, sannna na ce.

A a, kwana uku ina ga, Alhamis za ayi final, monday adawo, amma ni tun talata zanyi tawa final Win.

Eyh zaki iya zuwa, ko sati ne ki yi, shi karatun yaushe zamu fara?

Ko gobe ko?

Na faWa da alamar tambaya.

To hakan ya yi, bari na je na yi wanka, zuwa yamma may be na dawo.

May be?

Na faWa, ina yi masa wani kallo, ya yi dariya sannan ya ce.

Tom, da yamma zan dawo.

Better.

Na faWa tare da matsawa daga jikin motar, shi kuma ya shiga, sai da yabar harbar ni kuma na shiga, ina gab da shiga na ga kamar mutum a laSe yana kallona, na yi kamar bangani ba, sai dai nasa ™afa kamar zan shiga ciki na yi wata iriyar juyowa, Musa me bawa fulawa ruwa ne a makatanta, hannusa ri™e da waya yana yi min video, a take ™wa™walwata ta haskomin shine idon Sardauna, jikinsa na rawa ya juya zai gudu na ce.

Na ganka, kuma sai na yi reporting Winka yanzu nan.

Ba shiri ya dawo tare da faWin.

Dan Allah ki yi ha™uri, wallahi zan rasa aikina.

Na yi masa wani banzan kallo sannan na ce.

Kana tsoron rasa aikin ka, kake Waukan Waliban makaranta a video.

Ki yi ha™uri, Yayanki ne ya sa ni, ya ce baya so tarbiyarki ta Saci.

Wane Yayan nawa?

Na faWa da alamar tambaya ™arara.

Wanda ya zo wajenki wata rana, wani fari sosai, me yawan sa fararen kaya.

A take nagane Sardauna, na ce.

Ta ya ya ce ma shi Yaya na ne ka yarda?

Yana nuna min hotonan ku tare, ya ce duk ranar da wani yazo wajenki, na yi video zai zo ya amsa yaban kudaWe masu yawa, ranar farko ma dubu Wari biyu yaban.

Akan kuWi, to ba Yayana ba ne, ba Wan uwana ba ne, ban da wata ala™aa da shi, dan haka zan kai ™ararka.

Ki yi ha™uri.

Na tsaya ina kallonsa na da™ika, sai kuma na yi wata shawara.

Zan ™yaleka, amma kuma za ka yi min wani aiki.

Zanyi wallahi.

Daga yanzu kullum ka kira shi ka ce masa mutane daban daban suna zuwa wajena, wata rana ma har mutum uku su kanzo wajena.

Tom, zan yi wallahi.

Idan baka yi ba, kaga nima na yi recording Winka, zan kai wajen hukumar makaranta.

Innullahi, ki yi ha™uri, wallahi duka zanyi.

Ya rage naka, na faWa tare da shigewa ciki, sai da na zauna na fara tunani, me Sardauna yake nufi dani Nana, me ya sa yake min haka, wace masifa ce wannan.

Har yamma jikina ba ™wari, ko da Turaki yazo ma ba wani shiri na yi na mussamaan ba, mu ka fita, yau wajen wasa muka je wai shi SKY PARK sai dai akwai nisa sosai sa sosai, amma na ji daWin zuwa wajen sosai, na ™ara samun lokuta masu daWi tare da Turaki, washe gari ya zo makaranta mu ka fara karatu a libarary tare, ina yi yanayi, yana min bayanin wasu da hausa yan da zan ™ara ganewa, sai yamma ya tafi ni kuma na koma Waki, ko a Waki na ci gaba da maimaitawa a cikin salon da ya yi min, abun farin ciki washe gari da naje Wakin jarabawa, wasu tambayoyin da na tuna wani lokaci ko wani abu da ya yi min a lokacin da muke karanta wajen, sai na ji komai ya dawo min fes a kaina, haka na ™are jarabawar nan zuciyata fal da soyayya, har na fito na dawo Waki.
Chapter 26 · 0% Book details