← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 50

Sashe 36

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In sha Allahu ba zaka sameni da wata matsala ba, zan kasance me biyayya a gareka, zan kasance mai duk wani ™o™ari wajen sanya ka farin ciki Mijina.

Wani dogon tsaki ta ja ji kake. Mitchewwwwwwwww. Tare da ta shi ta fice, har ta kai ™ofa sannan ta ce.

Bazawarar arzi™i dai kwana uku ake mata, amma kishiyar waje bamu sani ba.

Ka yi ha™uri, kar ka damu da komai, nasan daman zan tarar da abinda ya fi wanan.

Na faWa ina komawa kusa da shi, ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki, sannan ya ce.

Nana, islaha daman an aurota ne dan ta zama tsaiku a zaman aurenmu ni dake, bansan me ya sa ba, amma ina jin kamar na sake ta a yanzu, Nana ban shirya zama da abinda zai dame ni ba akan ki, Nana ina sonki, son da zan iya Satawa da kowa akanki.

Da sauri na girgiza kai, sannan na ce.

A ah, karka fara dan Allah! Dan hakan wani ba™in jinin zai ™ara jamin daga zuwa na ka saketa. Tin da mun san manufarta sai mu ci maganin zama da ita.

Shikenan Nana, Allah Ya yi miki albarka, mu tashi mu shiga ciki.

Na mi™e shima ya mi™e muka shiga Waki, muna shiga ya yi toilet ni kuma na tsaya ina ™arewa Wakin kallon, Šakin Turaki ma ya tsaro abunsa, komai ya dace da inda aka sanya shi, shawarar fita zuwa nawa Wakin na yanke, naje na yi alwala na canja kaya dan wannan rigar ta isheni.

Ina shirin buWe ™ofar na ji an ce.

Ina zaki?

Sai da na waigo na kalleshi sannan na ce.

Zanje can na yi alwala, na canja kaya.

Ba tare zamu ba?

Na girgiza kai na ce.

Ai yanzu zan dawo.

Tom. Nima bara na canja.

Ina faWin haka na fice na nufi nawa Wakin, toilet na nufa na fara watsa ruwa, bayan na gama na yi alwala na fito, sif Wita na buWe zan Wauko riga. Sai dai ina buWe sif Win na ji murya sama sama, a hankali na saita kunnena, hayaniya ce kamar ta Sardauna, da sauri ma rufe sif Win na yi baya, sai dai na daina jin hayaniyar, kenan idan na buWe sif Win shi nake jin maganarsu? Iko sai Allah.

Ban mai da hankali ba na sanya riga ta na fito, ina shiga Wakin ya ce.

Yanzu nake shirin bin bayanki, sa kaya kamar ba za a dawo ba?

Sai da na yi wanka.

Na faWa ina ™arasa shigowa.

Shine kika yi ke kaWai? Maimakon nazo na yi miki?

Na yi ™asa da kaina, sannan na ce.

Kai ma ai ka kaWai ka yi.

Matsowa ya yi kusa dani, ya dafamin ka faWa.

Nana kinji ha daWi? Ki yi ha™uri dan Allah.

Na girgiza kai, sannan na ce.

A a, ba haka ba ne.

Bana son ace darenki na farko a gidana na yi miki abinda zaki ji ba daWi, Nana ina sonki.

Nima ina sonka, kuma bana jin zan iya jin

haushinka.

Allah Yasa Habibty, mu yi sallah.

Ya faWa yana mi™ewa, nima na mi™e na shimfiWa abun sallah muka tayar, ko da muka idar ya yi mana addu a, sannan ya shiga jeramin irin girman soyayyar da yake min, irin yanda yake jina a zuciyarsa, duk wasu kalmomi da Turaki yake faWa ina jinsu a cikin zuciyata.

Washe gari.

˜o™arin mi™ewa nake daga kan gadon, ya yi saurin matsowa kusa da ni.

Habibty na Good morning.

Na kawar da kaina gefe ba tare da na amsa ba.

Ta so Habibty.

Ya faWa yana ™o™arin kamani.

Na Waga ki?

Na girgiza kai alamar a ah, amma kamar ce masa na yi Turaki sama da ni, ya Waukeni ya yi sama dani, bai sauke ni ko ina ba sai a toilet, daman ya gama haWa ruwan wankansa. ˜o™arin cire min kaya ya fara, na ri™e tare da faWin.

Zanyi da kaina.

A a bazaki iya ba Habibty, bari na yi miki.

Duk yanda naso da Turaki amma ya gagara ™yaleni, sai da ya saSe ni tas. Haka ya sake Waukoni zuwa Wakin, ya ajiye ni a gaban mudubi, na girgiza kai tare da cewa.

Ai ba nan zan shirya ba.

Au, namanta Habibty bari na kai ki can.

A a dan Allah, zan iya zuwa.

To taso.

Ya faWa, na fara ko™arin mi™ewa sai dai ban kai ga mi™ewar ba ya sunkuce ni, ya yi waje.

Ka sauke ni na je da kaina.

Na faWa bayan mun fito.

Ai sai na kaiki fa.

Ina ™o™arin ya sauke ni, shi kuma yana tafiya muka yi kiciSus da Islaha, wani banzan kallo ta watsa mana, ta yi gaba. Muma mu ka wuce zuwa Wakin nawa.

Kabarni na shirya da kaina dan Allah.

Na faWa bayan ya sauke ni, ya girgixa kai tare da cewa.

A a fa.

Ni dai a a.

To wane kaya zan Wauko miki?

Kowanne, amma kabarni na shirya.

Šauko min kayan ya yi ya ajiye min, sannan ya ce.

Na jiraki ko zaki same ni?

Aina?

Dinning mana.

Ohky, gani nan.

Na faWa, shi kuma ya fice.

Sai da na shirya tsaf, sannan na fito zuwa Winning Win yana zaune yana danna waya, yana ganina ya sakar min murmushi, nima na mayarsa. Sai da na zauna sannan na ce masa.

Ina take?

Ta ce ba nan zata yi ba.

To waye ya yi girkin?

Ni mana my love, idan ban miki girki ba wa zanyi wa?

Na yi dariya, tare da girgiza kai.

Bari na zuba miki, ki ce girkin mijinki.

Ya faWa yaba mi™ewa ya fara zubawa, soyayyen da dankali ne, sai soyayyen ™wai a gefe, sai wata miyar attaruhu da ya yi, sannan ya zubamin tea.

Gashinan ranki ya daWe.

Na yi murmushi, sannan na ce.

Tom Mijina.

Šan aiki ba.

Na girgiza kai, na ce.

Ni ba abakina ba.

To ni a baki na, Habibty akanki komai ma a kira ni.

Fara cin dankali na yi, ina jin daWinsa tare da shayin, sai da na ci da yawa, sannan na Wauke hannu.

Kin ™oshi?

Eyh, ya yi daWi.

Abinda zan miki gobe ma, sai yafi na yau daWi.

Gobe ai da kaina zanyi.

Kai Habibty, indai ina nan kisa a ranki ni zan miki breakfast.

Wani sanyi na ji a raina, tabbas Turaki ya cika masoyin na ha™i™a, ina ma ace rayuwar ta tsaya a haka, bana fatan wani abu ya shigo rayuwata da Turaki wanda zai kawo mana tsaiko.

Gani na yi ya fara kwashe kayan abincin, na yi saurin tare shi da cewa.

A a bari na Wauke.

Banza ya yi min ya kwashe kayan ya nufi kicin, na mi™e na kwashe ragowar na bishi kicin Win.

Kina son wahalal da kan ki Habibty.

Bawami wahalal da kai.

To ya ne.

Ya faWa yana nufar sink, na yi saurin cewa.

Me zaka yi?

Wanke kwanakun da muka Sata mana.

No&

Ya tare ni, tare da cewa.

Karki Sata yawon bakin ki.

Matsawa na yi kusa dashi, na fara ta ya shi wanke kwanunka, haka muka wanke su muna hira yana hanani amma na na ce, daga kicin Win muka koma Waki muka zauna.

Habibty.

Na am.

Yau wa™a zan miki.

Wa™a kuma?

Eyh, wacce kike so?

Wacce ka rera da kanka?

Ya yi dariya sannan ya ce.

Ba wacca na rera, sai dai wacca wani ya rera.

Tom.

Habibty, wane mawa™i ne yafi iya wa™a.

Na girgiza kai, sannan na ce.

Ni ban wani cika sauraron wa™a ba.

Sai kallo?

Na girgiza kai shima.

To sai me?

Nifa ba komai?

Habibty babu wani abu na nishaWi da kike yi?

NishaWi?

Na maimaita kalmar, a raina na ce. Babu, nishaWi na Waya, kula da Sardauna.

Legendspen

08129553971.

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na talatin.

Cikin sanyin Ac da ke ratsa Wakin, ina zaune a kan kujera mai laushi, na takure waje guda ina kallon dukkan motsinsa. Hasken da™in ya kasance mai sanyaya idanu, wanda ya ™ara wa fuskarsa wani irin kyau da kwarjini na daban.

Yana tsaye a tsakiyar Wakin, ri™e da remote Win Ac a hannunsa tamkar abun magana na makirofon, yana bin sautin wa™ar da ke tashi a hankali. Idanunsa suna kaina, cike da wani irin murmushi mai taSa zuciya, yana girgiza jikinsa kaWan-kaWan cikin ™warewa da kazar-kazar.

Muryarsa tana fita a hankali, yana haWa ido da ni yayin da yake rera wa™ar.

In dai akan ki ne na yi nisa dan ba kiran da zan amsa.

Wani irin daWi na ji ya mamaye mini dukkan jikina. Na lumshe idona ina jin yadda kalmar na yi nisa take ratsa kowacce jijiya ta jikina.

Ina buWe idona, na ga yana takowa zuwa inda nake, har yanzu idanunsa suna narke a cikin nawa, muryarsa tana daWa zurfi.

Tilas ganin mu tilas barin mu ™aunarki tun da nai nisa.

Wani gajeren kallo na jefa masa, wanda na san ya isa ya gaya masa dukkan abinda da ke Soye a raina na soyayyarsa. Na gyara zama, ina jin yadda shau™in soyayya yake neman huda kowane sashi na jikina. Kalamomin da yake faWa na kowanne baiti ba a iya baitin wa™a nake jin su ba, jin su nake tamkar suna bin jinina ne suna zazzaga a cikin zuciyata.

Murmushi ya suSuce mini, na kasa Soye farin cikin da yake shirin fito mini da hawayen daWi. Shi ma ganin murmushina, sai ya fashe da wata daddaWar dariya wacca ta bayyana kyakkyawan hakoransa, ya mi™a mini hannu tamkar yana roko na na karSe shi.

Yana daWa matsowa kusa da ni, har ina iya jiyo hucin numfashinsa, ya tsaya daidai gabana sannan ya cike baiti na gaba cikin wani irin salon mai ratsa zuciya.

Sam ba batun na fasa ko za a ce mini in ba da rai fansa.

A lokacin da ya fadi kalmar Rai fansa , sai na ji wani irin shock ya ratsa Waukacin gangar jikina. Nima na fashe da dariyar. A daren nan, babu abin da zuciyata take gani sai shi, babu abin da nake ji sai kalaman sa, na sake tabbatar wa kaina cewa, babu wani abu a duniya da zai iya raba ni da shi na har abada.

Habibty ta yi daWi?
Chapter 36 · 0% Book details