← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 50

Sashe 18

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Radiya ta faWa, Hajiya ta sake cewa.

Bazan iya kwantar da hankali na ba, sai na ga yaron nan ya rabu da yarinyar nan, ya ™yale mata rayuwarta, mu yi jinyarta ta warke ta koma yadda take.

Hajiya Nana zata warke, komai zai wuce, zai zama labari in sha Allah.

Allah Yasa.

Na faWa daga inda nake, dan nima na ™osa na ga komai ya wuce, na ™osa na ga komai ya zama kanar ba ayi ba.

Yau tun da na kwanta banyi wannan firgitar ba, har asuba. Ni kaina na ji daWi sosai kuma alamun na fara warkewa, dan a tsorace nake da wannan yanayin da nake ciki.

Wajen ™arfe 12 na rana Yaya Rumaisa ta zo, muka haWu mu uko sai Ra is da Yaya Ridwan su kuma a mashin Win Yaya Ridwan muka nufi gidan, bayan kuma manyan motoci ne guda biyu da za a kwashen kayan, sai samarin da zasu Wauki kayan.

Tun da muka nufi unguwar na ji gabana yana wani irin faWuwa, sai na ji ina tsoron shiga unguwar, ina tsoron haWa ido da Sardauna, motar da muke ciki ce ta fara shiga gidan, sai mashin Winsu Yaya Ridwan sai kuma manyan motocin guda biyu. Kamar me tsoron taka ™asa haka nake fitowa daga motar, gabana yana wani irin faWuwa a duk lokacin da na yi taku zan shiga cikin part Win, mun kusa minti goma sha biyar muna bugu sannan aka zo aka buWe. Bilkisu ce cikin wata iriyar shiga, ta watsa mana wani kallo da yafi harara ciwo sannan shige.

Shiga mu ka yi gaba Wayanmu, Yaya Rumaisa ta kalle ni ta ce.

Kujerunku suna ina? Ai wannan basu ba ne asalin naki?

Shiru na yi nama rasa me zance, sai da ta ™ara cewa.

Ba magana nake miki ba?

Sune, waWan can da zamu canja gida ya bar su acan.

Da zaku dawo gidan ya siya waWan nan?

Yaya Radiya ta tambaya, na gyaWa kai sama alamar eyh.

To shi ya sani, mu dai su zamu kwasa.

Yaya Rumaisa ta faWa, sannan ta ce da masu kwasar kayan.

Ku fara da waWan nan.

Ta nuna musu kujerun, sannan ta sake kallona.

Wanne ne Wakin gadonki?

Nasa hannu na nuna mata nawa, na ce.

Shine wancan, amma babu kayan gado anan sai a wancan, shi ya ce na dinga kai mutane.

Shiga suka yi, na bi bayansu Wakin komai da akwai amma babu komai a sip Win, zallan zalunci ne kawai na Sardauna ya sa ya ce na ajiye kayana a akwaiti.

Ina mai Sallewar? Ya zo ya fara Salle waWan nan.

Ta saki faWa, Yaya Radiya ta ce.

Kayan sawarki fa?

Suna wancan Wakin.

Ta fice ba ta ce dani komai ba, na bu bayanta zuwa Wakin. Ina shigowa ta kalleni ta ce.

Nana kinyi zaman azaba, ga Waki can guda da kaya complete amma kinzo nan kin ™are kamar almajira, Allah Ya wadaran Sardauna.

Na yi mamakim tsintar kaina da cewa Amin, ta matsa ta fara jawo akwatin tana fita dasu. Sai da ta fito falo ta ce da Yaya Rumaisa.

Katifa Waya muka kawo ta da ita, Waya zamu Wauka.

To me zamu yi da kayansa daman, kayan tsiya. WaWan nan ma daga nan kasuwar katakwaye zamu kaisu a siyar, mu canja mata wasu ko a ajiye mata kuWin, da ba zamu shigar da irin masifa cikin gidan ba.

Wata uwar ™ara ce ta taso daga Wakin Bilkisu, wata shegiyar wa™ar Ado gwanja aka ™ure uwar volume, me shiga tsakiyar kai. Yaya Radiya ce ta ce.

Ke wannam kishiya take kwai sheWaniya.

Yaya Rumaisa ta ce.

Ni kam na ji daWin aurenta da Sardauna, wannan kina ganinta kinga sheWaniya, zasu goge juna ne.

Amma fa akwai kazanta, ji wani wari da gidan yake.

Yaya Radiya ta faWa, tana toshe hanci. Muna tsaye a falon suka kwashe kujerun tas, sannan Yaya Rumaisa ta ja su Wakin gadon, nan ma ta sa su fara kwance kayan kafin su fara fita dasu.

Sai kuma kicin Winki, shima ba abinda kika Wauko acan?

Na gyaWa kai sannan na ce.

Mun tawo da kurfoti.

Mene kurfoti?

Yaya Rumaisa ta faWa, na ce.

Abin girkin gawayi.

Au, Nana da gawayi kike girki?

Na gyaWa kai, ta watsamin uwar harara sannan ta ce.

Na gaisheki uwar asararru, wallahi Nana kinyi asara.

Yaya Rumaisa ta faWa, Yaya Radiya ta ce.

Nana anyi bautar aure.

Anyi fa.

Ra is ya faWa yana dariya, sai na tuna lokacin da Anty Adiza ta zo, take cemin miji biyayya ake masa ba bauta ba, yanzu yau gashinan gaskiyyarta ta fito, duk na matsu ta dawo daga Kano, gidanta ma zanje na yi ko sati ne.

An gama kwance kayan gadon.

Šaya daga cikin masu aikin ya faWa.

Yawwa to, ku fara fito dasu, suma ku sanya a wancan motar.

Yaya Rumaisa ta faWa, sannan ta ce.

Muje muga kicin Win.

Daidai lokacin kuma muka ga Bilkisu ta fito ta nufi ™ofa, ™awayenta ne guda biyu suka shigo, suna shigowa suka tsuntsire da wata shegiyar dariyar da bamu san dalilinta ba.

Kicin Win muka shiga, muna shiga Yaya Rumaisa ta ce.

Allah Ya tsareni fasawa yar mutane kai.

A a Rumaisa ki kama kan ki, mu yi abinda zamu yi mu kama gabanmu.

To amma Yaya ki ji iskancin da suke yi.

Barsu su yi, Wa namiji ne fa, ana zaune zai yi mata fin abinda ya yi wa Nana.

Hakane kuma.

Ta faWa suka fara kwashe kayan, Ra is ne ya shigo yana faWin.

Ga Sardauna can, zasu fara faWa da Yaya Ridwan.

Ya salam.

Yaya Radiya ta faWa tana ficewa, Yaya Rumaisa kuma tsayawa ta yi tama faWin.

Ki barsa ya ci kutumar ubansa, daman shi ya sa na ce kar ya shigo masa gida ya tsaya daga parking space, barshi ai Sardauna ko me yake haWiya Ridwan yafi ™arfinsa.

Ni dai ina tsaye bance komai ba, ta kalleni ta ce.

Zaki ta yani ko sai na danna miki zagi.

Yaya bara naje dai.

Na faWa tare da ficewa, ina zuwa na ji hayagagar Sardauna yana faWin.

Get out from my house.

Shi kuma Yaya Ridwan ya ™ame yana faWin.

Bazan fita ba, dalili ne ya kawo ni, kuma duk wani abu da yake na yar uwata sai mun Wauke shi.

Ita ta ce muku tana da wani abu anan ne?

Yaya Radiya ce ta ce.

Ridwan, matsa gefe ka cika shi.

Ba musu Yaya Ridwan ya cika Sardauna ya matsa gefe, Yaya Radiya ta ™arasa kusa da Sardaunan ta ce.

Mun zo mu kwashi kayanta ne, tun da dai kasan da muka kawo bata ita kaWai tsilau muka kawo maka ba.

Ya buWe baki zai yi magana idanunsa suka sauka akaina, ina tsaye na harWe a jikin ™ofa ina kallonsa ido cikin ido, tunani Waya ke yawo a raina, mene abun so a sardauna, wannan mummunan farin? Ko wannan fuskar tsofaffin? Allah Ya isa. Na faWa a raina, tare da kawar da kaina gefe.

Gatanan ku tambayeta idan da wani abu wanda kuka kawo ta dashi gidan nan?

Eyh ta ce babu kasiyar, me zuciyar mitsiyata, ka siyar. Amma wallahi kasani yanda kasiyar ka yi amfani da kuWin kai kaWai a cikin ka muma sai mun kwashi na ka kayan da ka sanya mun tafi dasu, ai ba zi™au muka kawo ta ba.

Yaya Rumaisa dake bakin ™ofa ta faWa.

And who the hell you think you re? Ni Sardauna zako cewa me zuciyar mitsiyata? Me kuke da shi? Ina da arzi™im da zan siya duk ma™waWaitan danginku, ina da arzi™in da zan siye ki na siye talakan mijinki.

Wata muguwar dariya ™awayen Bilkisu suka saki, ita kuma ta tako kamar wata jaSa, ta ™araso inda yake.

My Baby, ka daina asarar miyan bakinka wajen musayar da mitsiyata.

Wallahi yanzu zan tattaka ki anan, naga uban da ya tsaya miki.

Ra is ya faWa yana wuci kamar mayunwacin zaki, Yaya Rumaisa ta tako a hankali ta ™araso inda Sardauna yake.

Haka dai, fariya. Sardauna na kira ka da me zuciyar mitsiyata, ba ta mitsiyatan bace? Arzi™i irin naka Sardauna dashi gwanda babu, gwanda rayuwa cikin talauci. Arzi™in na baki na fatar baki, arzi™in da bazaka iya morawa kanka bare wani naka, Allah ya wadaran arzi™inka Sardauna. Kuma wallahil azim kayane duka sai mun kwashe waWanda suke ha™™inta, kuma daga nan sai kasuwar katakwaye muje mu siyar dasu domin bazamu bar kayan tsiya a cikin gidanmu ba, amma dai Sardauna ko wuta kake fesarwa duk wani abu da yake irin wanda muka sanyawa Nana sai mun Wauke shi.

Tana faWin haka ta juya ta yi ciki, cikin rashi sa a ta yi gaba sa wata ™awar Bilkisu ta hankaWata cikin Wakin, aikuwa su ka yi kan Yaya Rumaisa sa hayagaga, sai dai kafin su ™arasa Ra is ya sa hannu ya fisgo Waya baya ta faWi ™asa shaSar.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na sha biyar.

ShaSar haka ta faWi ™asa, Bilkisu ta buWe baki ta lailayo wani uban ashar, wanda kafin ta rufe baki Yaya Rumaisa ta mayar mata da shi, sannan ta ™ara da cewa.

Idan tijara da rashin arzi™i kuke ji dashi, to wallahi munfi ku.

Tana faWin haka ta shige ciki, Yaya Ridwan ma ya shigo muka jera a tare muka shige, haka duk sanda za a fito da kaya Yaya Ridwan yana bayan masu fita da su. A haka aka gama kwashe komai aka sanya a mota, Bilkisu da tawagar ™awayenta dasu kaga anfi ™arfinsu sai suka ja jiki suka koma Sangarensu. Ni dai ina tsaye a falo ana kai komo wajen kwashe komai da yake da sunan nawa a gidan, a raina ina ta nanata. Shikenan nabar sardauna, na barshi har abada.

Sai wajen ™arfe 4 aka gama kwashe duk wani abu nawa, sannan muka sa kai muka tafi, fitar da nasan ita ce ta ™arshe, nasan har abada babu abinda zai sake dawo da ni gidan Sardauna, nasan tsakanina da Sardauna komai ya ™are, soyayyar da nunawa Sardauna bata amfani ne da komai ba, sai wahala.
Chapter 18 · 0% Book details