Sashe 47
Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ji na yi jikina ya yi wani irin sanyi, zuciyata ta yi wani irin haske, wani irin jindaWi ya shige ni, na kama hannunsa da ya mi™omin na fara tafiya, ai kuwa Sardauna ya yi wani irin ihu ya kama Turaki yana ™o™arin yin baya da shi, Turaki ya kwace, ya Waga rigarsa ya fito da bindigarsa ya ce.
Wallahi Sardauna ka matso nan sai na fasa kanka da bindiga, idan kuma kana musu ka matso, kasan Allah na harbeka na harbe banza, a dokance zan ce Wan ta adda ne kai, a addinance ma rayuwar azzalumi irinka bata da rana, fasaqi, mai zina da matar aure, shima kisa ne ya rataya akansa, dan haka na kasheka, na kashe banza wallahi.
Tsit ka ji ba motsin Sardauna, sai faman mamatso baki yake yi, yana son ya faWi magana kuma ya kasa, babu abinda ya girgiza shi jin kalmar zina da matar aure, ko ba a faWa ba yasan ansa abinda yake faruwa tsakaninsa da islaha, Bilkisu ce ta ce.
Duk abin kunyar da kake cewa na yi, na kamani ina yi maka barbaWe a abinci, bai kai naka abun kunyar ba, zina da matar aure? Sardauna me zai sa na wahalal da kaina wajen mallalke? Kai da nasan ba wani lasting zaka yi a duniyar ba? Na gode Allah da na zubar da mahaifata, ban Wauki cikinka na tsahon wannan lokacin ba, da zunubin ka na zina ya shafi ya yana, sharrin da ka ™ullawa Nana da mijinta a wancan lokacin shine ya dawo kanka, nasan Sardauna ba kaga komai ba a rayuwa, nasan nan gaba sai ka kwashe duk wani abu da ka shuka.
Kamar jira yake kuwa ya kai mata duka, Turaki ya jani mu ka yi ciki abunmu, ni duk kaina ma ya Waure, Bilkisu ta zubar da mahaifarta, amma kuma shi bata lalata masa nasa ba kamar yanda ta faWa, tin da ga Islaha da cikinsa.
Legendspen
08129553971
SARTSE BOOK 2
(Sayyid legendspen)
Shafi na talatin da tara.
Habibty kin ji wani abu ko?
Turaki ya tambayeni, na gyaWa kai sannan na ce.
Habiby abubuwa duk basu yi daWi ba.
Ki kwantar da hankalinki, kaWan Sardauna ya gani, in sha Allah komai sai ya girbe.
Ko a yanzu ma ai ya girbe, Allah Ya tsare mana imaninmu.
Amin Habibty, ki yi wanka mu kwanta da wuri, duk gajiyar biki kin gaji.
Kaga ma mun manta jakar kayan ma a mota.
Ma Wauka da safe, idan sun gama tashin hankalin.
Na shiga Waki na watsa ruwa, na fito na dawo na zuana akan gado, na shiga tunanin yanda Sardauna ya yi amfani da Bilkisu suka yaudareni, suka ci amanata, yanzu gashi ba aje ko ina ba, duk a ™asa da shekara biyar komai ya caSe, mai hankali dole ya fahimci duniya babu tabbas a cikinta, ka shuka abun alheri kawai. Ina zaune Turaki ya shigo, sai da ya zauna kusa dani ya ce.
Habibty wai damuwar su Sardauna?
Na girgiza kai, sannan na ce.
A a, ina tunanin yanda rayuwa take, yanzu amana ta zama ba komai ba, mutumin da aka aminta dashi sama da komai, shine mutumin da zai tura ka rana.
Habibty me ya faru? Waye ya ci amanar wani?
Anan dai babu, amma abinda yake faruwa a rayuwa kenan yanzu, mutane babu amana.
Hakane Habibty, shi ya sa ake cewa ka koyi yanda zaka ri™e sirrinka, sannan kasa waWan da zaka raba damuwarka dasu.
Amma kasan me? Habibi wani abun fa baka da yanda zaka yi, dole sai ka raba shi da wani, kuma mutane ba a gane na gaskiyya ko na banza a ido.
Hakane, amma kuma ai Allah baya barin ha™™in wani, yanzu ke akan ki baka ga izina ba? Yanzu waWan da suka yaudareki suka ci amanarki, suka cutar dake, suna rayuwar daWi ne ko akasin haka?
Hakane kuma, Allah Ya bamu wucewa lafiya.
Amin Habibty.
Ya faWa tare da janyoni jikinsa, mu ka kwanta. Washe gari da safe ma wani sabon faWan ne ya tashe mu, ta window na le™asu dan shi Turaki ko akansa, kamar ma baisan suna yi ba. Sardauna sai fitowa da Bilkisu kayanta yake, ita kuma tana mayarwa, a raina na ce.
Sardauna ya haWu da daidai shi a rayuwa.
Ina aiki ina gulma, haka na gama haWa breakfast na kawo wa Turaki, mu ka yi breakfast ya fita, ni kuma na hau shirin ofis. ˜arfe sha Waya daidai na fito daga part Wina, ina ™o™arin shiga mota na ji ana kira.
Nana! Nana.
Na waiga naga Sardauna, na buWe mota zan shiga ya ri™e murfin motar.
Nana tsaya mu yi magana dan Allah.
Sardauna wace magana? Mene ala™a ta dakai? So kake mijina ya zo yaga ina magana da kai, ranshi ya Saci?
Nana dan Allah ki saurareni, Nana wallahi tun fitar ki daga rayuwata abubuwa suka canja min, rayuwa nake amma kwata kwata bana jin daWin komai Nana, ki yi wa Allah ki dawo mu zauna.
Mu zauna kuma? Ka fara haukane? Da aure na zan dawo mu zauna? Kowa Islaha ce?
Nana, kin san ina sonki, ™addara ce ta rabani dake, kuma nasan kema kina sona.
Eyh kam, ada na so ka Sardauna, son hauka wanda babu hankali a ciki, amma yanzu kam, babu.
Nana ki fahimce ni., kiji abinda ke zuciyata?
Wace fahimta?
Nana, a duk ranar da naganki da Turaki ina jin zafi a zuciya, zuciyata tana ™una.
Wallahi Sardauna da ina da yadda zanyi ido biyu da zuciyar taka sai na sa mashi na cake ta, ko ta ™arfi ne na fito da ita, na yayyanka ta na watsawa karnuka ita, dan dabbobi ne suka da ce da ita, Sardauna na tsaneka bana son ko haWa ido da kai, Sardauna wallahi ina danasin mai girma idan na tuna wai a baya naso mutum mai kama da kai, kuma idan baka matsamin daga nan ba, sai na take ka da motar nan wallahi.
Ina gama faWin haka na buWe motar na shige, ya yi saurin ri™e murfin motar.
Nana Sardauna ne fa.
Mitchewwwww. Na ja wani dogon tsaki na fisgi murfin mota ta na rufe. Mai gadi ya buWe min na yi waje. Ni ko sha awar ganin Sardauna bana yi wallahi, natsani ganin Sardauna ko kaWan. In shiga asibiti na je wajen Dr Halim, likitar da take duba ni akan mahaifafa, ina shiga na sameta zaune tana duba files.
Good morning Ma.
Na faWa ina zama,
Morning Nana, Ya mai gidan?
Yana lafiya kam, Dr akwai wani bayani ne?
Eyh Nana, kamar yanda aka faWa miki a baya cewar mahaifarki ta warke dagaske ne, sai dai haihuwr ce shiru har yanzu Allah bai kawo ba.
Na yi shiru, jikina duk ya mutu, ina son haihuwa, ina son naga ya yana, nasan Turaki ma haka, kawai soyayya ta ce ta rufe masa ido, baya ganin hakan, amma tabbas nasan zai damu.
Dr Nana, karki sa wata damuwa a ranki dan Allah, haihuwa nufin ubamgiji ne, wasu sai su shekara goma da aure sannan su haihu, wasu ma fin haka, ki yi ha™uri kawai ki dage da addu a, mussaman ke da aka cutar dake, Allah baya barin ha™™in wani akan wani.
Shikenan Dr Na gode sosai.
Na faWa tare da ficewa na koma namu ofis Win, haka na yi aikin duk jikina babu daWi babu kuzari, ko da mu ka yi waya da Turaki na ce masa kar yadawo cin abincin rana dan ina ofis, daman yawanci juma a da asabar da lahadi ne yake dawowa kullum, sauran ranaku sai ya tambayeni ina gida ko ofis, sai da ya tambayeni me ke damuna na ce masa bakomai. A haka na tashi na dawo gida, ina shiga gida na watsa ruwa na kwanta sabida wani irin yanayi da nake ji, ji nake kamar fa ni bazan haihu ba, ba zan ga ya yana ba.
Allah ka sakamin nagani, Allah ka ™ara sakamin, bazan iya yafewa Sardauna ba.
Na faWa ina zubar da hawaye, ina nan kwance har yamma ta yi, na shiga kicin. A sau™a™e ma dafa masa taliya na dawo Wakin na zauna, ko da ya shigo ma ban ji shi ba har sai da yazo Wakin da nake kwance.
Habibty lafiya wai? Tun Waxu na jiki wani kala, ko an miki wani abu?
Na girgiza kai, bance komai ba.
Tell me Habibty, wani abu ne, ko nine?
A a kawai munyi magana da Dr Halim ne, ta cr haihuwar har yanzu Allah bai bamu ba, amma mahaifar tana lafiya.
To sai me? Dan Allah bai bamu ha shine kike fushi? Allah kikewa haka, ko me? Nana baki gode da ni imar yan uwa masu ™aunarki da ya yi miki ba, kin manta Wan uwanki ya baki kyautar yara har rai biyu a ranar da aka haifa masa? An faWa mik baya son su ne da ya baki? Ba zaki yi wa Allah godiya da wannan ni imar ba? Haba Habibty, ya yan Ridwan Win baki Waukansu a matsayin ya yanki? Kinga Habibty idan kin san bazaki so yaran nan ba kamar ke kika haifesu to kar mu Wauko su, ni dai Allah Ya gani ina son su, ina jinsu a raina kamar nawa ya yan, ina sonki dan haka ina son duk wani abu sa ya fito daga wajenki Habibty.
Na share hawayen dake idona, sannan na ce.
Ina son su, kuma na godewa Allah, amma nasan kaima kana son kaga na ka ya yan.
Ni na faWa miki Habibty? WaWan nan yaran guda biyu kaWai idan Allah Ya raya mana sun ishemu, duniya da lahira, kuma ni bazan taSa yi musu wani kallo wanda bana ya yan cikina ba, ni dai ta wajena ba za asami wani matsala ba.
Nima haka nasani, nasani kuma in sha Allah bazan sake damuwa akai ba.
Yaww Habibty, dan Allah karki damu, wallahi bana son abinda zai dame ki, ko kaWan bana son naga wani canji yanayi a tare dake Habibty, ki kasance mai godiyar Allah ako da yaushe.
Dole na godewa Allah ko da iya baiwar miji irinka da ya yi min.
Wani irin bugu muka ji ana yi wa ™ofar mu wanda ya sa muka fito a guje.
Nana! Nana! Nana!.
Kallon Turaki na yi, na ce.
Kamar fa muryar Sardauna?