← Book details Sartse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 50

Sashe 13

Sartse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na faWa tare da rufe idon, nan ya karanto min addu o in kwanciya bacci ina maimaitawa, har ya gama sannan na ji yana tofa min ajiki, sannan ya tashi ya fice, ina rufe idona na kwanta.

Hasken ranar da ya biyo tagar Wakin ne ya daki idona, ba shiri na buWe idona da sauri na mi™e zaune. Ji na na yi wata falau kamar ba abinda ke damuna, sai dai ganin hasken ranar da na yi ya tunasar dani cewar safiya ta yi, gari ya yi haske kuma ban kaiwa Sardauna komai ba, ™ila ma ya fita.

Ba shiri na mi™e na fito falon ina kiran sunan Sardauna, sai dai babu shi babu alamunsa. Daidai lokacin aka tura ™ofa aka shigo, Turaki ne ya shigo fuskarsa Wauke da fara a.

A a Nana an tashi?

Na sunkuyar da kaina, sannan na gyaWa shi sama alamar Eyh. Ya ™arasa shigowa sannan ya ce.

Nana ina kwana?

Ina kwana?

Nima na faWa, bai amsa ba ya ce.

Yau kin makara, Sardauna sai a wajena ya yi breakfast, na faWa masa baki da lafiya ne shi ya sa bai tashe ki ba.

Har ya fita?

Na tambaya, ya ce min.

Eyh mn, kema ga naki.

A a, yanzu zan dafa nima.

Ai shi ya ce kici, kuma ya ce wai ba kya ja da dukkan abinda ya faWa.

KarSa na yi na nufi kan dinning Win, shi kuma ya juya, sai da ya kai ™ofa sannan ya ce.

Ya jikin naki?

Da sau™i, Alhamdulillah.

Allah Yasa kaffara ne.

Amin.

Sai da ya fita, sannan na ce.

Kowanne jiki yake nufi? Oho.

BuWe plate Win na yi naga soyayyen dankali da plantain, sai kuma ™wai. A kufin kuma daman Wumin da na ji ya sa nasan shayi ne, sai dai ina buWe na ga coffe ne. Kamar wasa na fara ci, aikuwa sai da na ci da yawa sosai, sannan na shiga Waki na sha maganina, na dawo kan kujera na zauna. Tabbas nasan jiya da daddare na yi wata firgita, kuma Turaki ya shigo, amma sai dai na manta duk wani abu da ya ce dani ko na ce dashi, na kusa minti talatin ina faman tunane-tunane, amma na kasa tuna komai. Wajen ™arfe biyu, bayan na iddar da sallar azahar ina zaune akan daddumar da na yi sallah, na ji murya a falona, yin™urin mi™ewa na fara yi, sai dai kafin na mi™i an shigo Wakin. Na yi matu™ar mamakin ganin Sister Seemah a gidana, matar da gaba Waya sau biyu na ganta a rayuwata, shima a zuwa family meetings ne nake ganinta.

Sannu da zuwa, ina yini?

Na faWa a dabarbarce, wani kallo na ga tana bin Wakin nawa da shi, bayan ta gama ta sauke idonta a kaina, sannan ta ce.

Lafiya ™alau, ya gida?

Lafiya, ya su Momy.

Lafiya, ke haka Wakin gadon naki yake? Ina kayan da iyayenku suka yi miki?

Cikin rawar baki na ce.

Mun barsu acan gidanmu na da.

Ina kuma wanda shi Sardauna ya yi miki da zaki dawo nan?

Suna wancan Wakin, nan ba Wakin bacci ba ne.

Uhm, biyo ni falo.

Ta faWa tana ficewa, ba musu na bi bayanta zuwa falo, ta zauna akan kujera ta yi WaiWai.

Bari na kawo miki ruwa.

Na faWa ina nufar hanyar Wakin Sardauna.

A a barshi, ina shi Sardaunan kira shi mu yi magana.

Ya fita.

Tun yaushe?

Šazu da safe.

Kin tabbata?

Eyh.

Bilkisu fa?

Na kwana biyu ban ganta ba.

Mi™ewa ta yi sannan ta ce.

Idan yazo ki ce mai nazo

Tana faWin haka ta fice, na bita zan rakata sai dai na hango su tare da Turaki, suna magana. Kasancewar glass din taga ta a rufe yake ban iya jiyo me suke cewa ba, na dawo na zauna. Ba afi mintuna biyar ba sai ga Turaki nan ya shigo.

Nana, ashe sister Seemah ce tazo.

Eyh.

Na bashi amsa a da™ile, zama ya yi aka kujera sannan ya zaro wayarsa.

Nana kinga Sardauna yana kira na.

Ya faWa yana sa wayar a kunne.

Hello Sardauna.

Sai kuma ya yi shiru, wajen sakan talatin sannan ya ce.

Ta tashi tun Wazu, na kai mata ma abincin ta ci, yanzu Sister Seemah ma ta tafi.

Ya sake yin shiru, sai ya ce.

Ina?

Ya ™ara yin shiru, sannan ya ce.

Na kai ta gidan big daddy, ta yi me to?

Gabana ne ya faWi, me zaayi a gidan big daddyn? Ba haihuwa ba ce, na ga ya auro Bilkisu.

Kasan Nana fa ba lallai ta fita ba, amma zan jarraba.

Yana faWin haka ya katse wayar, sannna ya kalleni.

Ya ce na kaiki gidan Big Daddy.

Na girgiza kai sanna na ce.

A a bai ce na fita ba.

To yanzu ya faWa min.

Ni bazan fita ba.

Na faWa mai?

Na gyaWa kai, na ce.

Eyh.

Shikenan karki je, kunfi kusa.

Yana faWi haka ya mi™e ya fice, ni kuma na shiga tunani kala kala, daman yadda naga Sister Seemah nan, nasan ba mutunci a idonta, ga shi kuma ance wai naje gidan Big Daddy. Ni dai na shiga uku ni Nana, duk Bilkisu ta ja min, ta cuceni da ta zubar da cikin nan. Na faWa a raina. Gaba Waya gidan ya daina yi min daWi, duniyar ta tsaya cak, wani irin zafi ya gaureyi gidan gaba Waya, na mi™e na fara zagaye gidan gaba Waya, na shiga can na fita can, na shiga can na fita can.

Daidai matattakalal da zata sadani da falo ™afa ta ta gurWe, wani zafi ya ratsa ™ashina. Ina tsugunnawa a ™asa na ji kaina ya fara juyawa, idanuna suka buWe tar, suka fara haskamin lokacin da muka shigo falon nida Sardauna, har zuwa lokacin da Bilkisu ta ce kar na zauna mata akan kujera, komai ya dawo min fes, harda sakin da Sardauna ya yi min.

Tabbas Sardauna ya sake ni, innullahi wa ina illahir raji un.

Sai a yanzu nake jin zafi sakin da ya yi min, sai a yanzu nake ganin hula™ancin da Sardauna ya yi min ta hanyar sanya Bilkisu ta rubuta min saki.

Amma zaman me nake yi a gidan?

Na tambayeki kaina, da sauri na mi™e na shiga duba ko ina, ina neman Sardauna, amma babu shi babu Bilki. Šakina na shiga na ga babu wata sip babu gado, zama na yi akan kujera na fara tunanin yaushe rabona da Sardauna ne? Kamar fa Sardauna da Bilkisu sun daWe ba sa gidannan, ni kaWai ce a cikin gidan, ni kaWaice ke shirme na.

Ya salam.

Na faWa, sabida wani sarawa da na ji kaina ya yi, a take jiri ya Webeni, na ri™e kan nawa da na ji yana wani irin sarawa. Sai da na Wauki kusan mintina goma sha biyar ina cikin wannan halin, sai can na ji kan ya tsagaita da sarawar da yake, a lokacin kuma na ™ara tabbatar da cewa babu Sardauna babu Bilkisu a cikin gidan nan, Sardauna ya sake ni, yabar gidan shi da matarsa, ya barni a ™as™ance, ya barni ina zaune kamar mabaraciya. Sai a yanzu na tuna kallon da me gadi yake yi min a ranar da na fita raka Sardauna mota, domin kuwa ni kaWai ce na fita ina shirmena, Sardauna baya nan, haka ma girkin da nake yi nake ganin ba yaci, ni kaWai na kewa kaina bana ganin Sardauna bana ganin kowa, na taSo ne kawai nake ganin abubuwa a haka.

Wani irin matsanancin kuka na saki wanda ya haifar min da wani irin ciwon kai, me jiri da hajijiya, Wakin ya fara juyamin na fara ganin dishi dishi.

Wai ni Sardauna ya saka? Ni Sardauna ya hula™anta.

Abinda ke yi min yawo a cikin raina kenan, yanzu duk soyayya da biyayyar da na yi wa Sardauna ta tashi a banza kenan, babu wata riba a duniya?

Innullahi wa inna illahir raji un.

Abinda na faWa kenan, sai kum na tuna da kalaman Bilkisu, na yanda Sardauna ya dinga amfani da wauta ta yana sani ina zuwa wajenta, ina kiranta a waya, tana hula™anta ni duk da sanin& & kai na ne ya Wauke lokacin da kalmar ba zaki taSa haihuwa ba ta shiga kunne na. Na mi™e a zabure, sai dai kuma jirin da nake ji ya kayar da ni.

Ya Hayyu Ya Qayyum.

Na faWa tare da fashewa da wata iriyar razananniya ™ara, na fara kuka. Sai da na yi na gaji sannan na dawo falo, tunani nake ta ina zan fara komawa gida? Me zance da mutanen gidanmu? Mutumin da na zaSa sama dasu, sama da kowa ya sake ni? Mutumin da nake yiwa soyayyar da tafi ta kowa ya lalatamin mahaifa? Innullahi wa ina illahir raji un.

Allah Kasheni na huta ni Nana.

Na faWa ina fashewa da wani irin zazzafan kukan, gaba Waya bana jin komai sai zafi, duniyar ta hirgitsemin. Yau ni Nana da na ce Sardauna ne ni, Sardauna ne abun so da ™auna, yau ni Sardauna zai hula™anta.

Sallamar Turaki na ji yana shigowa, da sauri ya yo kaina yana faWin.

Ke mene? Me ya faru kuma?

Mi™ewa na yi da niyar tafiya na barshi, amma wata juwa ta Webeni na zube a ™asa, cikin sa a na ji na faWa a ™irjinsa. Ni dai nasan sai da ya haWa da gudu kafin ya tareni, sabida yadda nake nesa da shi.

Ki yi ha™uri Nana, yanzu zan kai ki gida.

Sama sama na ji muryarshi ya faWa, ni daman neman hanyar da za a kaini gidan ma nake, dan bani da idon da zan taka na nufi gida, na ce wai Sardauna ya sake ni, wai ™uruciyata ya aura, wai so yake ya raba ni da Wan uwansa, ya killaceni ga wasu mazan. Šauka ta ya yi a hannu kamar ya Wauki jaririya, ya taka ya nufi hanyar fita. Fitar tamu ta yi daidai da parking Win motarsu Sardauna. Da wata iriyar hayagaga ya fito daga motar yana faWin.

Gidan ubanwa zaka kai ta, shege kwarto.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 2

(Sayyid legendspen)

Shafi na sha Waya.

Bansani ba!

Turaki ya faWa, muryarsa cikin tsawar da ta daki kunnuwana, na yi matu™ar mamakin jin bana sha awar ko ganin Sardauna ne.

Sauke ta!
Chapter 13 · 0% Book details