← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 113

Sashe 8

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bata kara fitowa daga dakinsu ba sabida tsoron gamuwanta da Baba, saida tasake wanka dan haka take kaman kifi arana zata iya wanka sau ashirin sannan ta shirya cikin kayan makaranta, shima makarantan sabida Baba na nan ne da wlh bazataje ba, wani white long sleeve rigane daya tsaya a cinya sai kuma wani dogon gown ash dazaka daura akan farin rigan sai abun yayi kaman biri da wando dayay mata kyau sosai, zama tayi Gwaggo dakanta tashiga samata safa akafa itakuma tana kirga kudin asusunta data bude Gwaggo tace “wai Mezaki da kudin ki dakike tarawa ma salla iyye”? Turo baki tayi tace “wani abu zanyi” tabe baki Gwaggo tayi tana karasa saka mata black cover shoes nata tace “kyadaiji da rigimanki baran biyemiki da safen nan ba dan na lura neman abinda zaisa bazakije makaranta kike ba” Gwaggo tai maganan tana kawo mata wani fine black bag pack tace “ga jakan ki” karban jakan tayi tabude da sauri chocolate daban daban da aka zubamata ta kalla da biscuit da juices kala uku da goran ruwa saikuma wani dan karamin flasks na snacks sannan tadago kai takalli Gwaggo kirji Gwaggo ta dafa tace “menene kuma ni Safarau dazaki dallamin miyagun idanuwan nan naki” amugun shagwabe tace “baki samin yoghurt ba Gwaggo” kaman Gwaggo zatai kuka cikeda lallashi tace “wlh bansan yoghurt dinki sun kareba Lulu kiya kuri zansa Baban ku yasayo yau tashi muje chan palour” makema Gwaggo kafada tayi idanunta sun cikada kwalla har kyalli suke amman basu zuboba rudewa Gwaggo tayi tazauna kusada ita cikeda bala’in lallashi takai hannunta tanajan kumatunta tace “haba mana Lulu na yarinyan datafi duka yaran duniya kyau so kike ajimu, kema kinsan kome kikeso sai inda karfina yakare ko wannan ma bansan yakare bane kiyakuri kina dawowa zaki tadda yogurt naki” makema Gwaggo kafada tayi still ita bata yarda ba Gwaggo tace “to yanzu mekikeso? Ni wlh kin fitineni Lujain kin hanani sakat aduniya, zanfa tattara nakoma kauye nabarki” kaman jira take fashewa tayi da kuka sosai kaman ana yankata ta tashi fuuu tafice ko jakan bata daukaba da sauri Gwaggo tadau jakan tabita abaya tana kwalamata kira tace “Lujain zoga dubu daya saiki saya wlh wasa nake babu kauyen dazani nabarki, nima ina zan iya rayuwa babu ke kinmini nisa” kojuyowa Lujain batayiba sai kukan datake daya cika gidan gabaki daya yana eco daidai Baba yafito daga falo chak ta tsaya anan tsakar gidan kukan yamakale awuya Gwaggo takaraso dasauri tana hararan Baba tace “kaikuma meya fito dakai ina ruwanka damu ai magananmu mukeko Lulu” da sauri Lujain ta gyadama Gwaggo kai tana goge fuskanta da bayan hannu, strictly Baba na kallonta yace “collect your bag muwuce school” ahankali tamika ma Gwaggo hannu, Gwaggo tace “yauwa diyar albarka zan sayamiki kafin kidawo kinji ga jakan” karban jakan tayi ta goya Baba yafito zai gaida Gwaggo tace “jeka kaisu kadawo ai ina nan babu inda zani” girgiza kai kawai yayi yawuce Lujain tabishi haka su Samira ma dasuka fito duk sun shirya su sun fara university, suna shiga bayan motan murya kasa kasa Samira tace “ina kudin”? Mikamata kudin Lujain tayi aboye itama taja jakan Lujain tasamata wayanta da earpiece aciki tace “ai kinsan password dina” Gyadamata kai Lujain tayi tana murmushi kaman ba ita tagama kuka ba, a school dinta Baba yafara parking school ne mai kyau ba laifi ga buses awaje an jerasu sabida excursion din daza ayi sauka tayi Baba yakalleta yace “zagayo tanan” zagayowa tayida sauri ta tsaya wajen glass din motar daya sauke yana kallon fuskanta dukta tsure dan tana tsoron Baba sosai, dan jim yayi yana kallonta kaman mai tunanin wani abu saikuma yace “menene bakida shi dakike kuka?” Adan tsorace kaman mai tsoron fadi tace “yooo………ghurt Baba” murya chan kasa still yana kallonta yace “ana saidawa acikin school din naku?” Gyadamai kai tayi ahankali, yace “nawane”? Ahankali tace “500 ne Baba” dubu daya yadauka yabata yace “gashi to kisaya” wani kalan murmushi tayi daya bayyana fararen hakoranta tass irin na yara din nan tace “thank you Baba” murmushi yamata yace “excursion zaku yau ko”? Gyadamai kai tayi tana rikeda 1k din yace “ina”? Hannu tanunamai alamun batasani ba tace “amma ance wajen ceramic ne, zamuje muga yanda ake yin su flower verse, broken plate, bowl, tiles da sauransu” gyadamata kai Baba yayi yace “is a good thing makesure kinyi paying attention and learn everything kinji” gyadamai kai tayi tace “too” juyawa tayi tubur tubur zata wuce Baba yace “Lujain” dasauri tajuyo takalleshi tace “na’am Baba” ahankali yace “be careful okay” gyadamai kai tayi tajuya tawuce saida Baba Yaga shiganta school sannan yasauke ajiyan zuciya yatada motar duk cikin yaranshi yafijin tausayinta bawai sabida ita marainiya bace kadai ba sabida many things, she gets bullied a lot a school, a islamiyya, har agidama, wani zubin yanaso yarabata da Gwaggo but idan yakalla abin deep down badadan Gwaggo ba da yanzu she’s depress Gwaggo nakoya mata komi ba komi bane karta sake tai taking maganan mutane to heart and she should be confident kiba is beauty kuma haka takeyi Koka cemata me kiba da sauransu wani zubin zata iya kuka but give her one hour ta kakkabe jikinta tayi moving on gashi ko kadan batada riko her heart is as pure as white paper.EPISODE 7️⃣

Tana shiga school ana cewa sufito afara shigan bus dan 9:30 zasu bar school yan class nasu yan SS2 akace sufara tafiya bus nasu ita hartama saba batada friend shiga tayi itane sit 1 dan ita tafara biyan kudi tana zama tabude jakanta tadauko ledan biscuit tafaraci yan ajin saikaga wannan yataba wanchan anunata sai akwashe da dariya ko kallonsu batayiba dake bude jakan tayi ta leka wayan Ya Samira tareda dannawa taduba time dan 11 Mandawari zaizo live a IG, murmushi tayi maida jakan tarufe tana cigaba da cin katon biscuit dinta wata Yar class dinsu tamike tsaye a bus din bayan an gama shiryasu an koma wani bus ana shirya wasu yan ajin base on payment tace “Hey Class mate I have a story to tell u tantadaaaaa” duk kallonta akayi wasu yan mata da samari click dinsu sukace “we are listening princess” dariya tayi tace “I want to call some part of the body kugayamin uses dinsu” duk akace okay, tace “the eyes is for whattt?” Yan ajin sukai ihun “seeing” tace “the ears is for what”? Suka kara ihun “hearing” cikeda zolaya from her tone tace “and the mouth is for whatttttttt?” Yan ajin sukai ihu atare “eating” tace “for what” sukace “eatingggggg” Haba sai dariya duk Lujain najinsu hakan bai hanata cigaba da cin abinta ba, komawa princess tayi tazauna tana dariya saiga wata ta tashi da ake cema Lily tace “aga aga” dayake dudda akwai Christian a ajin but duk sunajin hausa universal language sukace “aga” tace “aga chop chop din aji” atare duka suka nuna Lujain sukace “aaaagannntaaaaaa” sai dariya tace “aga mara kawa” suka nunata sukace “aaaaagannnntaaaa” tace “aga mara aboki” sukace “aaaaagannnntaaaa” sanan tai wani ihu irin na final one din nan tace “aga mara boyfrienddddddd” duk aka nuna Lujain akace “aagannnnnnntaaaaa” kwarema Lujain tayi ba kakkautawa dasauri tashiga bude jakanta taduko ruwa da sauri tashiga sha saida tasha sosai sannan click din su princess din sukazo inda take tsabagen son ta kulasu Princess tace “ke miss chubby bakijimu bane Fatty bom bom” wani mugun kallo Lujain tamata batai wata wataba tamike tsaye tareda ajiye jakanta kan sir din dasauri Princess suka koma baya dan sun zaci dukansu zatayi ko zaunesu cikin kunanrai Lujain tace “Ohhkayyy you want me to say something ko” boldly takalli yan cikin bus din tace “aga aga” Yan makaranta fa akwai son bala’i da fitina, they live for it shine the joy and the fun that comes with being in school da sauri sukace “aga” Lujain tace “aga masu satan amsa during test and exam masuyin chokes olodon aji amman sunfi kowa iya makeup” habawa sai dariya kyakyalya bakaramin kunya princess da Lily sukaji ba, Lujain tanunata da hannu tace “idan kika kara kirana Chubby kowani stupid name saina fasa miki ciki, my name is Lujain but I prefer idan ankirani da LJ, and I am pretty, prettier than this bullies, and I am brilliant cus banayin choke, and I am beautiful I don’t need makeup kuma I have boyfriend a celebrity for that matter” tanunasu habawa sai ihu ajin ana bubbuga kujeru da kasan motan da kafa ana dariya yan class din suka fara matching ana tafi “LJ! LJ!! LJ!!! LJ!!!!” juyawa tayi takoma sit dinta dasauri ta bala’in danne kukan datakeji Gwaggo tasha gayamata kada tasake tayima yan ajinsu kuka idan sun kirata da sunaye dan zasu cigaba saisa bata sake tai kuka and bata taba nunawa wani dan ajinsu she needed them ba tana homework dinta tai karatunta da kanta dan Allah yamata brain.
Chapter 8 · 0% Book details