← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 113

Sashe 22

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Asabar!
Karfe 4:30 yabude kofanshi yafito yana sanye dawata white jallabiya dayasha karin guga yasaka hula fara sai wani kalan kamshi yake mai kwantarda hankali, bakaramin kyau yayi ba saida kana kallon kwayar idanunshi zakaga yadan fada sosai yarame, direct dakin Hamza yashiga bubbuga bakin gadonshi yayi Hamza yabude idanu ahankali ganin Ya Imran har sake goge idanu yayi zaiyi ihu yatuna maganan Dr, “bazaka tashi bane” Abee yay maganan ahankali murmushi yayi ranshi fess yatashi da sauri yace “natashi Yaya Imran” ficewa Abee yayi daga dakin yashiga dakin Abdallah dake bacci Abdallah daya bude ido yaga mahaifinshi saura kadan yafada jikinshi yadaure baiyiba yatashi yawuce bayi yana murmushi kaman anmai kyautan dream car nashi c300, dakin Kausar yawuce ya kunna wuta yana kallon yanda ta kudundune abargo dakinta kaman fridge AC yafara kashewa sannan yabubbuga gadon yana karbe bargon hakan yasa tabude idanunta ganin Abee dawani kalan sauri ta mike tsaye daga gadon kawai tafada jikinshi dan lumshe ido Abee yayi yabubbuga bayanta, sakinshi tayi tana murmushi tace “Abee sorry na rungumeka banyi wanka ba mafarki nayi na rungumeka saisa ina ganinka nayi” hancinta yaja yace “talkative” washe mai baki tayi yajuya yafice daga dakin kap yatada sister nashi duk wanda yaganshi saikaga smile of happiness akanshi sauka kasa yayi zuwa dakin Hajiya dayaga wutan a kunne ganinshi batasan lokacin data shafe addu’an datake ba tace “zaku wuce masallacin”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya” murmushi tayi tace “incedai wannan mayen baccin Hamza yatashi” dan murmushi yayi yace “yatashi” daidai nan daga waje Hanza yace “to natashi Hajiya kuma naji abinda kikace” murmushi yayi yafito daga dakin Hajiyan suka fice Hajiya tadaga hannu tareda godema Allah daya fito yau dakanshi.

Hi GGM, did you know just because you act different baya nufin kai mahaukaci ne, sometimes is just PTSD! Now check on your family members and share ❤️EPISODE 1️⃣6️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Wuraren 8 yashigo gidan na safe sabida yanda Baba Liman ya tsaidashi sunyi maganganu masu tsawo, da sallama yabude kofan falo yashigo ganin Musty, Harun da Abdul police a tsakar falon kan lallausan carpet suna breakfast da waina yaji man shanu da farfesu, ganinshi yasa da hannu Musty yace “zo wlh saura kadan su Abdul su cinye maka wainar ka” dan murmushi yayi ga mamakinsu tahowa yayi yazauna kusada Musty cikinsu yadauki spoon yafaracin wainar dasu babu wanda hakan baimai dadi ba, sosai yaci abincin kodan baici abinci yau kwana nawa bane oho saida yaji yakoshi sannan yatashi daga wajen dauke da mug na coffee Hajiya sai farinciki take sabida yanda taga yaci sosai, laptop Abdul yaciro daga jaka yakunna yaduba wani abu saikuma yarufe yatashi zuwa gaban TV yace “BBC sun fara sanarwan kuyi shiru muji” BBC suna sanarwa cewa wani ma’aikaccen company shi yahadamai wannan shairin sabida bai bashi miliyan dari ba dakuma takardun company tareda saka hotonshi a tashin kan cewa duk wanda yaganshi hukuma na neman yaron, saikuma nabiyu Alhaji Imran mijin yarinya da ake cewa yay fasikanci da itane ga shaidanan daga iyayensu nan aka fara nuno su Baba dasu Hajiya suna cewa ma’aurata ne, sannan video edit ne su kansu tashar BBC sun tabbatar da hakan sabida ma’aikatansu dasuka tabbatar dahakan, saikuma na karshe suna kirada Al unmma sudaina yada karya idan kunne yaji gangan jiki ya tsira shikuma wannan gayen duk inda yashiga hukuma zasu bishi har wajen akamoshi” adaidai nan news din yakare, yan dakin kowa yashiga cewa Alhamdulillah Alhamdulillah, kurban shayin Abee yayi ahankali su Musty suka shiga janshi da hira sai wajajen 11 yatashi dan yaje ya kwanta, sama yawuce ganin Anty Binta nafitowa daga wani dakin da dagashi sai corridor shiga dakinshi rikeda kaskon turaren wuta bamata lurada shi ba saida tajuyo ganinshi yasa tace “Yaya ina kwana” Gyadamata kai yayi batare daya amsa ba hakan yasa tawuce ahankali yakarasa gaban dakin harzai wuce saikuma yadawo kaman baiso yamika hannunshi yabude kofar dakin, gidansu nada bala’in kyau bana wasaba but dudda haka dakin nan standout agidan gabaki daya yakai kusan 2min tsaye gaban dakin yana kallon cikin dakin batare daya shiga ciki ba saikuma yajawo kofan yamaida yarufe yawuce dakinshi.
*****

Yanda Lujain kejin jikinta ita kanta har mamaki take maganin shawaran kesata jin haka, gashi Gwaggo kullum saita mata dilka ta gurgurza mata jiki hakan yasa fatarta yawani kalan kara kyau dudda tanada fata mai kyau, jikinta yakara wani kalan lumu lumu dawani extra taushi daman yawanci masu kiba nada taushin fata barin ita da fatarta is ultra soft yanzu saiyazama wani extremely soft.
Yauma kaman kullum daga ita sai wani pink towel data daura akirji an tsife nata kalaban dake kanta da alamu ma an wanke gashin sabida yanda bakin keta uban shinning gashinta is so silky and coily ga tsayi an mata parking nashi dawani blue ribbon mai kyau anyi donut da bakin gadhin, tana zaune a tsakar gida kan tabarma kusada Gwaggo dake tankade wani gari hannunta manya manyan chocholate ne guda biyu tanaci tana kallon yanda Gwaggo ke tankaden, dan juyowa Gwaggo tayi takalleta tace “mekike kallona nan nan dazan fita babu yanda banyi dakeba muje tare kinki fita akanme zaki dinga tsoron fita, rabon dakimaje jikin gate kibude ki leka waje harna manta, nace babu abinda mutane zasu miki dazun baki tashiba BBC sun saka sanarwan an wanke ku tass to mezai faru, koma ba’a wanke kiba akwai wanda ya isa yamiki kallon banza ne ina taredake eh”? Dan turobaki tayi tace “Ya Samira fa tanunamini Gwaggo wlh muryana ne sarai ni bansan ya akayi yay tsawon nan ba” hawaye ne yacika idanunta, murya chan kasa tace “kowa yanzu har yan islamiyyan mu kallon Yar iska sukemini koni banmantaba tayaya wayanda suka kalla zasu manta wlh kaman in mut…..” buge mata baki Gwaggo tayi tace “wlh kika karasa fadin kalman nan saina dokeki wawiyar yarinya kawai asalin yan iskan duniya masu fasikancin na rayuwansu suke abinsu ba saike dabaki komiba duk kinbi kin dami kanki duk jibi yanda kika fada kalli wuyanki har yau idanunki basu koma daidai ba sabida kuka” tashi dagakan tabarman Lujain tayi da gudu tashige dakinsu tana kuka Gwaggo tabita da harara tace “aisaiki tayi bakida damuwa ne yarinya tunda inasa kudina ina sayamiki kayan kwalama ubanki nasaya miki ne” Gwaggo tai tsaki tacigaba da tankaden datakeyi Gwaggo tacigaba da masifa tace “yarinya sabida ita yau kwana nawa kenan ban samu nahuta ba amman ta isheni Alhamdulillah yau zanyi bacci nai munshari wahalar ki kuma saidai takoma kan mijinki Imrana nahuta” Gwaggo takarashe maganan ahankali sabida tunda ta tasa rigiman batason auren Gwaggo ta zuzxuba mata karya bata sake mata maganan ba ko anjima akazo kaita da ubanta zata barta ai bata isa tama Babanta wannan haukan da shirmen ba tuni zai karairayata yabama karnuka kashin itane dai data raina takema yan abubuwa, jin kukan yay yawa yasa Gwaggo takasa daurewa dan jin kukan Lujain take har cikin jinin zuciyarta kakkabe hannunta tayi tawuce dakin.
Chapter 22 · 0% Book details