Sashe 23
Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Anayin mangariba Gwaggo takirawo su Samira dukansu kuskus sukayi nadan tsawon lokaci kafin su shiga falon Gwaggon inda Lujain take a zaune tana shan tea, ganin Samira rikeda dawani babban jaka yasa Lujain ta tashi da sauri tace “Ya Samira baby yakawo miki wani abu ne”? Daure fuska Samira tayi tace “banace kidaina kiramin saurayi da sunan danake kiranki ba” dan murmushi tayi mai bala’in kyau tace “to yakuri menene amman ajakan” jakan tabata tace “Baba yace mukawo miki ki shirya bayan isha’i yana nemanki” zaro idanu tayi takalli towel din jikinta tace “Kodai yaganni da towel ne saida ya aikomin da kaya na shiga uku” tai maganan tana fizge jakan dasauri tai uwardaka zata fara farke ledan Samira tashigo tace “Malama jeki wanka” daga falo Gwaggo tai ihu tace “da ruwan maganin nan zaki wanka” wucewa bayi tayi itakuma Samira ta zauna abakin gado tana bude jakan wani simple lafaya lace ne mai kyau red and gold, sai Yar cikinta, sai set na dankunne da sarka na zirconia mai kyau shima sai flat shoe na Zara kayan dai gabaki daya akalla Baba yakashe 35k fitowa tayi tana zaro idanu tana kallon kayan tace “laaaa harda sarka da takalmi anya ni Baba yace akawo mawa kuwa saikace zanje biki” tabe baki Samira tayi tace “idan kinje ki tambayeshi nidai Malama kidauko pant da bra kisaka kizo kisa kayan” tsayawa tayi jimm kaman mai tunani Samira tace “kuma kima kanki fada kidaina daura towel akirji kina zama koda yaushe nonon ki duk zasu zube ne” dan yatsine fuska Lujain tayi tace “Ya Samira ni damuna suke wlh na tsani saka bra da pant, pant na cimini cinya” tsakani ga Allah tai maganan, Ya Samira tace “kiba yasa suke cimiki jiki, ciye ciye yamiki yawa babu namijin dazai soki idan kina haka cus yawan kiba is disgusting” tsayawa tayi tana kallon Ya Samira saikuma tajuya mata baya tasauke towel din ta daura a waist zata fara saka bra, saida tasaka bra din tajuyo tace “saisa su Ya Abida basa sona sabida inada kiba I am disgusting” tsayawa kallonta Ya Samira tayi this is the first time take ganin jikin Lujain haka dudda she’s putting on bra tanada very nice fat boobs gasu a tsaye, inda ace batada kiban nan bakaraman Cinderella za’ayi ba anan gwarama da aka mata Auren nan dan nan gaba kar samarinsu suzo suna ganinta sudinga cewa Lujain takeso, ganin yanda Ya Samira ke kallonta yasa dawani kalan sauri takai hannunta takare kirjinta tace “mehaka Ya Samira”? Tsaki Samira taja tace “Malama kizo kisa kayan nan angayamiki ke nake kallo ni I am lost in my thought ne mezan gani anan da banda shi” karasa saka pant Lujain tayi tazo Ya Samira tashiga shiryata bata mata kwalliya ko dayaba kawai lafayan tasaka da dankunne da sarkan ta tayafamata lafayan akai sai Lujain tayi kaman ba itaba ita kanta Samira saida tace “dayake duk wanda yasanki da towel yasanki inbadai kayan makaranta kika saka ba yau sai kikayi kaman ba kanwata Lujain ba, bakiyi kaman Lulu Gwaggo ba daikika fito tsaf Lujainnnn, kidinga saka kaya kinga yanda kikai kyau ne” kallon kanta Lujain tayi amadubi wani kalan murmushi tayi tace “wlh nai kyau amman kinga harsun soma damuna kayan kaman na kwabe su cizona suke” Ya Samira tace “ki kwabesu Baba ya kwabe ki” kyalkyacewa da dariya Lujain tayi sosai hakan yasa Gwaggo ta daga labulen uwar dakan taleko tace “chakulkuli kike mata ne datake dariya hak……” kasa karasa maganan Gwaggo tayi ganin yanda Lujain tayi kyau, Gwaggo batasan lokacin data yafito su Abida ba tace “kuzo kuga kanwarku” dasauri suma duk sukazo kallonta suka shigayi Lujain sai dariya take tace “nai kyau ko Gwaggo na”? Washe baki Gwaggo tayi tace “kaman hurun ini Lulu ta” tabe baki Abida tayi takoma tazauna Habiba tace “kidinga sa kaya haka jibeki saikika fito kaman mai hankali” hararanta Lujain tayi zatai magana Gwaggo tace “barta da halinta yi maza kiyi isha’i gashichan an sallame a masallaci yanzun nan Babanki zai kiraki” gyadama Gwaggo kai tayi tahau kan dadduma Gwaggo tasaki labulen taja su Abida kitchen tabasu manya manyan jakunkunan da Allah kadai yasan meta hadama Lujain aciki tace “su wuce sukai motan Baba” kaiwa sukayi suka dawo Abida tace “Baba yace kije waje” gyadamusu kai Lujain data tashi daga kan dadduma tayi zata saka slippers Gwaggo tace “saka takalmin da Baban naki Ya Aiko miki mana” sakawa tayi dan kuttubin kafanta yay kyau tayi da cute white feet nata da long long nails dinnan kaman kasa abakinka kaitasha, tana murmushi tawuce tafita lullubin lafayan na zamewa baya kyakkywan gashinta Ya bayyana gate tabude tafita, Baba tagani da Baffan ta guda biyu awajen tsaye jikin mota dukansu tsayawa kallonta sukayi ahankali tace “ina yininku” amsa mata sukayi Baba yazo gabanta ahankali yadaga hannunshi yajawo Dan kwalin lafayanta gaba sannan yakama hannunta zuwa bayan motan yasata aciki Baffa Abdullhadi yashiga maxaunin direba yusuf Ya zauna agaba Baba Ya zauna abaya kusada ita sannan aka tada motar.
Murmushi tayi takalli hanya tace “Baba ina zamu”? Anatse Baba yace “gidan mijinki zamu kaiki!”.EPISODE 1️⃣7️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Don’t miss this book for anything dan yanzu aka fara💃💃
Murmushi tayi takalli hanya tace “Baba ina zamu”? Anatse Baba yace “gidan mijinki zamu kaiki!”.EPISODE 1️⃣7️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Don’t miss this book for anything dan yanzu aka fara💃💃