← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 113

Sashe 7

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

5 na asuba tabude ido ahankali takalli inda Gwaggo take kan dadduma sannan ta tashi zaune ahankali tana jaye zanin gadon tana murmushi tasauka dagakan gadon da sauri tawuce bathroom na cikin dakin da ruwan zafi tai wanka tai brush sannan tai alwala tafito daure dawani towel din bayan ta wurga wanda tacire kan washing machine tazo dakin bataga Gwaggo awajenba hakan yasa tadauki wani dogon hijabi tadaura akan towel na jikinta tahau kan dadduma, tana sallame sallan ta tashi batare datayi azkar ba tawuce tafita daga dakin tashigo falonsu wani chocolate dake kan center table na cabry diary milk tadauka da sauri tana budewa tai wajen kofa daidai nan Gwaggo tafito daga kitchen tace “ina kuma zaki gari bai gama wayewa ba Lulu”? Batare data kalli Gwaggo ba tace “wajen Ya Samira zani” baki Gwaggo tabude zatai magana amman tuni tabude kofan tafice Gwaggo tabita tana kwalamata kira tace “bazakizo kisa kaya ba da asuban nan kina yawo daga ke sai tawul babu dan kwali akanki Lujain” ko juyowa batayi takalli kakartata ba saina kara sauri datakeyi zuwa babban flat din gidan tana tafiya kaman Kazan agric dataci takoshin nan tana tafiya da kyar tana tafiya tana ballan chocolate din hannunta tanaci, gidan dan Babba ne ba laifi kana ganin yanayin tsarin gidan kasan ba laifi gidan masu rufin asiri ne daidai gwargwado, bude kofan flat din tayi tashiga dakin tsaf tsaf sai kamshi yake babu kowa afalon direct tawuce wani daki dake corridor dataji hayaniya budewa tayi tashiga da sauri tana murmushi, yammata uku ne acikin dakin dake dauke dawani babban gado na daidai rufin asiri ga daddumai da hijabai akasa kana ganinsu hancinsu zaisa kagane sudin duka sisters ne saidai su kaf dinsu black beauties ne kuma ko kadan basu da jiki kaman ita su sirara ne yammata sosai, duk kallonta sukayi suka watsar amman ko ajikinta wani kalan murmushi tayi tamaida kofan tarufe takaraso cikin dakin tana kallonsu daya bayan daya, Babban cikinsu wacce akalla zatayi shekaru 23 ne da waya ke kunnenta tace “Baby ina zuwa zan kiraka” sannan ta katse wayan takalli wacce ta shigon tace “Lujain ba jiyan nan da daddare Baba yagama miki magana kan zama da towel dakuma rashin daura dankwali ba” dan yatsine fuska tayi kaman zatai kuka ashagwabe tace “mancewa nayi ban daura dan kwallin bafa Ya Samira” dasauri wacce takira da Ya Samira tace “to towel dinfa” dan turobaki tayi tace “wlh zafi nakeji idan nasa kaya” daya daga cikin sauran biyun matan ne taja tsaki tace “yarinya gabaki daya Gwaggo tamaidata mara saiti, ba dole kidingajin zafi idan kinsa kaya ba, jibeta kaman buhu” da normally ne da yanzu tai kuka da aka kirata da buhu but yau she’s extremely happy hakan yasa tace “wlh banda lokacin ki Ya Abida amman gobe ki tareni ki kirani buhu kiga abinda zai faru” yunkurowa Abida tayi kaman zata daketa hakan yasa da sauri Lujain din takoma baya Abida tace “maimaita abinda kikace”? Dauke kai tayi dayan sister da tundazu batai magana ba tace “Ya Abida inba so kike yau duk mutafi school da bakin ciki ba kada kitaba yarinyan nan yanzu dan wlh bamuba har Baba da Mama ransu yau saiya baci akanta kindaisan fitinan Gwaggo sarai” kaman jira Lujain din take jin ankira Gwaggo kwafa tayi tace “barta ta tabani ma tagani Ya Habiba” ganin rikici zasuyi yasa Samira tace “ni dan Allah ku kyaleta zonan kifadamin meya kawoki wajena da asussuban nan keda nasan war haka baki tashi ba” murmushi tayi ta harari Abida da Habiba tawuce wajen samira kaman maison gulma tace “ni akunnenki zan gayamiki” kunnen Ya Samira tabata magana tayi mai tsawo sannan ta tashi wani mugun kallo Samira tamata tace “chabdi wlh bazan baki ba hakanan” kaman zatai kuka tace “please Ya Samira kome kikeso zan miki Allah” shiru Samira tayi tana kallonta hakan yasa tace “wlh kuwa” murmushi Samira tayi tunawa da wani abu tace “inhar kin yarda zaki fasa asusun ki kibani duka kudin ciki zan baki wlh dama banda kudin ankon Aisha kinga nasamu” kaman zatai kuka tace “kai Ya Samiraaa duka fa kikace” hararanta Samira tayi tace “ashe baki cika crush din Mandawari ba, ni wlh idan inason wani celebrity babu abinda bazan iyayi akanshi ba, kikasan ma ko a live din dazaiyi yau yaraba ticket na zuwa kallonshi a stadium idan zai buga kwallo basaikije ba, kuma yana ganinki zaice yana sonki kinga yanda kikeda kyau ne” wani kalan mugun murmushi tayi dayasa kumatunta ya lotsa abin kaman wani machine ne awajen ya bala’in haska fuskanta, Abida dakejin firansu ne ta tsoma baki tace “Ya Samira stop deceiving this girl for your personal interest, international player irin Muhammad Mandawari kyakkyawan footballer hadadde ga kudi bazai taba cewa yanason wannan buhun yarinyar ba ko itace last woman on earth wlh” wani abune yatokarema Lujain wuya tajuya tana kallon Abida dake kallonta hararanta Abida tayi tace “yarinya abincin dazataci dukanmu nan bamu iya cinshi, tsakar dare kaman diyar aljanu dansu ke fatin abinci tsakar dare haka itama ketashi taci nata, Gwaggo kawai tabude mata ciki, tayaya ma Mandawari zai dauketa? Wlh tafi karfinshi” daga Abida har Habiba suka kwashe da dariya itakuma Samira tarike nata dariyan dan tana hango samun da zatayi, Habiba dake dariya tace “Mama ma tace babu wanda zai taba cewa yana sonta balle harma Ya aureta bakiga ba duka yan class nasu nada saurayi ita mazan ajin ko kallonta ma basayi bata burgesu everybody gets irritated with cin abincin Lujain da kibanta” juyawa Lujain tayi fuuu zata fice dasauri Samira tariketa tahararesu tace “don’t mind them yan bakin cikine Mandawari will acknowledge you one day as his die hard fan sannan zai soki harma ya aureki” sosai hawaye yacika mata idanu ahankali tace “are you sure Ya Samira bazaice nacika kiba ba” murmushi Samira tamata tace “ai kiba halitta ce kuma shi so comes from heart inhar na gaskiya ne ko kinfi kowa kiba aduniyan nan he will love you and cherish you, now smile for me muje mukarasa deal din inhar zaki kawo kudin yanzu zan baki wayan ki kalli live dinshi idan nadawo daga school na karbi wayata kin yarda” dasauri ta gyadakai murmushi Samira tayi tace “to jeki kawo kudin kafin nan nagama waya da Baby” da sauri tajuya tafita su Abida suka bita da harara sukace “wawiya kawai tama dawo ta dauke ledan chocolate din nan data ijiye mana anan dan nan ba dakin kakarta bane data maida bola ba”.EPISODE 6️⃣

Tana fita daga dakin daidai wata mata wacce kana ganinta kasan itace mahaifiyar yammatan datafito daga dakinsu sabida yanda sukai kama da mahaifiyar tasu, tsayawa tayi ahankali tace “Mama ina kwana” kallonta Mama tayi daga sama har kasa taja tsaki tawuce hakan yasa itama tawuce daidai tabude kofa zata fita daga falon taji Matar tace “duk randa aljanu zasu shigeki wlh saina bada sadakan dubu ashirin” batace komiba bude kofan dakin tayi tafita daidai lokacin wani magidancin mutum na karasowa gaban dakin sanye da jallabiya shima tareda wani babban yaro wanda bazai wuce 25yrs ba, wani mugun kallo dayama yarinyar yasa kawai jikinta yahau rawa kafinma yayi magana kaman zata fashe da kuka tace “Baba dan Allah dan Allah Baba kayakuri karka doken dan Allah” juyawa tayi zata koma dakin tsabagen rudewa saikuma tasake juyowa da sauri ta kwasa aguje tai side din kakarta mahaifinta yabita da kallo kaman zai doketa da idanu, ahankali yaron dake taredashi yace “kamata hakuri Baba please” dan ijiyan zuciya Baba yasauke saikawai yabude kofa suka shiga falon shida yaron.
Chapter 7 · 0% Book details