← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 113

Sashe 19

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Koda Gwaggo ta idar da sallan asuba da jan charbinta tashi tayi tafito falo tareda bude kofa ta taho bangaren su Mama bude kofa tayi uwa an biyota tazauna akan kujera daidai Mama tafito daga dakinta ganin Gwaggo taso tafirgita saikuma tace “lafiya Gwaggo da asuban nan” kallon banza tamata tace “lafiyan ce takawo haka” tabe baki Mama tayi tawuce tashiga kitchen abinta bata wani jima afalon ba saiga Babatareda Yayansu kafinma ya gaisheta hannu tamikamai tace “bani kudin sadakinta” dan kallonta yayi da mamaki yace “Gwaggo dama zan cika kudi ne namata kayan daki” cikeda daga murya tace “bakaji ance yanzu anan gidansu zasu zauna ba baa gama gidanshi ba lokacin daya gama gidanshi anemo wani kudin amata kayan daki” zama kawai Baba yayi yana kallon mahaifiyar tashi ganin haka yasa tace “ko baraka bani bane”? Ahankali yace “zan baki mana Gwaggo amman mezakiyi dahar dubu dari biyu gabadaya” cikeda ihu tace “yoo gyaran Amarya mana dudda ma babu wani lokaci mai tsawo yau kwana hudu yarage atafi da ita gidan mijinta amman dai abinda zanyi kenan” Mama dake tsaye cikin kitchen tanajinsu ahankali tace “fitinanniyan tsohuwa inama tamutu ahuta” kallon Yayan su Samira Baba yayi yace “jeka kawo kudaden nan adakina Auwal” tashi Auwal yayi yawuce dakin Baba baijimaba yafito da bandir na yan 1k guda biyu yakawoma Gwaggo yage takardan guda tayi sannan takalli Auwal din tace “kaine Babban jikana kaito ga dubu biyu sadaka kasama Auren kanwarka albarka” gudun fitina yasa yasa hannu yakarba yace “Allah basu zaman lpy” kwalama su Samira kira tayi tace “nasan kuna jina to kuzo nan” kaman munafukai suka fito suka gaida Baba da Gwaggo dake kallonsu tace “nasan kunsan kaddaran daya fada kan kanwarku Lujain, koma baku sani nasan farfesan uwar ku tariga ta fesa muku labarin daga tushe zuwa iri to yanzu dai Alhamdulillah Allah yabata miji nagari son kowa kin wanda yarasa da ake cewa bazata taba samin wanda zai sotaba da wannan kiban babu kalan gorin da baku mata ba to yanzu dai ga sa’an datayi dan haka nan sadakin tane zan muku sadakan dubu dai dai duk ku sanya mata albarka” dubu dai dai tazaro tabasu amsa sukayi kowannensu yace “Allah sanya alheri” tace Ameen, sannan takalli Baba tace “kake kallona kokaima nabaka ne” girgixamata kai yayi tace “bari naje namata abincin kari zan fita anjima, da daddare tarinka amai inhar naji jikinta da zafi zaka kaita asibiti” Gwaggo na maganan tana daga zaninta tana tura kudaden a cikin lalita tawuce tafita tana kaiwa dakin akan dadduma taga Lujain din tai salla takifa kanta akafa tana kuka hararanta Gwaggo tayi tace “aisaikiyi” kitchen tashiga tahau dumamata shinkafan jin kukan kuma taji takasa daurewa fitowa yayi tashiga uwardakan zama tayi agabanta tabuga tagumi tana kallonta tace “wai Lujain saikin kasheni tatas kinga bana numfashi zakiji dadi iyye? Yanzu mikikeso fadamin”? Ahankali batare data da go kanta daga kafanta ba tace “ni banason Auren nan ban isa aure ba kumani Mandawari nikeso” shiru Gwaggo tayi tana kallonta saikuma tace “kikace baki isa aure ba inace nannan Aisha har ajinku ta Islamiyya dake shekaru sha shidda tai aure har anko saida kika tasani agaba namata, su Zainab ma dake sha bakwai ba suna zana jarabawan gama sakandire aka musu aure ba kema inda rashin lafiya yabarki kinfara makaranta da wuri da yanzu kin tsufa da gama sakandire, kawayenki kadai yan layin nan dasukai aure sunkai hudu yanzu da akazo kanki ne zakice baki isa aureba, shikuma Mandawarin yasan ki? Yasan dake? Yamasan sunanki? Ke yarnan ki kiyayi kanki da auran calamburuti ina gayamiki barinma Mandawarin nan mai kamada shaidanu har kitso yakema gashin kanshi” sosai take kuka still bata dago kanta ba tace “wlh shiba shaidani bane Gwaggo yanada kirki, yana bada taimako har gidan marayu yake zuwa, yarabama guraguma keke” Haba Gwaggo takama tace “to akace miki shi kadaine mai kirkin duniya” tai maganan tanajan hanci jin kauri natashi tace “nashigesu wannan yarinya tasa na babbaka abinci” tai maganan tana fita daga kitchen da sauri kashe rishon tayi dan arisho take girki tadawo zama tayi kusada Lujain din ahankali tadagota tace “haba Yar jikata Yar lukutata Yar bulbul Yar kyakkyawa yimin murmushi ingani” ashagwabe hawaye na gangarowa daga idanubta tamakema Gwaggo kafada irin baratayiba, washe baki Gwaggo tayi tace “naji to zan miki abinda kikeso” dasauri tace “zaki raba Auren ki nema mini Mandawari”? Gyadamata kai Gwaggo tayi wani kalan murmushi tayi dayasa dimples dinta suka lotsa tai bala’in kyau tawani rungume Gwaggo Gwaggo na dariya tace “to jekiyi wanka nima fita zanyi amman bari nafara hada abincin ki” tashi tayi tawuce bayi tsaf Gwaggo tahada mata abincin kari da shayi wani green towel ta daura tazo ta zauna tafaraci Gwaggo tadauki mayafi tace “tonatafi kiyi zamanki adaki kada kije konan da chan kinji” gyadama Gwaggo kai tayi.
Tun safen nan sai wuraren 4 na yamma Gwaggo ta dawo da buhu buhu na itace da saiwowi saikuma zabi kaji da tantabaru da aka hadesu aka kullemusu kafafu, wasu yara takira tasa suka yanka mata aka gyara tafito dasu karfi da yaji sukazo suna aiki Gwaggo tun tana yarinya tayi gadon iya hada magunguna lafiyayyun tsumi tayi anan tsakar gida akan ittace daya hada da zuma da mazankwaila babu suga ko digi, sai farfesun su zabin datayi na magungunan hada su Samira tayi da Lujain din duk sukaci sannan tashiga hada farfesun jijjibi wasu magunguna kuma ta shanyasu, sai wajajen shadaya suka gama komi su Samira suka koma dakinsu itada Lujain suka koma dakinsu tsumi tazuba cikin kofi tabama Lujain tasha sannan tahada mata wani ruwan zafin wasu itace data dafa, Lujain dake zaune tana kallon cartoon a falo tanashan tsumin kadan kadan tace “Gwaggo wai magungunan menene” batare da Gwaggo takalleta ba tana saka farfesun daban daban datayi dasuka jera a robobi a dankareren freezer ta tace “shawara tamiki yawa baki gankiba Saura kadan kizama zabiya tsabagen haskenki” yatsine fuska tayi tana gyara daurin towel dake jikinta tun Gwaggo namata mitan tawul harta barta dan bata taba ganin mutumin daya tsani kayaba irin Lujain.
Gwaggo bata kara mata maganan auren ba sai uban magungunan datake loda mata na safe daban na rana daban na dare daban, ita dakeson yogurt saida Gwaggo tasa tasani yogurt sabida yanda take zubamata garin magana a yogurt din daban daban.
****
Chapter 19 · 0% Book details