← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 113

Sashe 112

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fitowa Dr yayi da danshi daya kara hada idanu da Kausar, dauke kanta Kausar tayi dasauri shikuma Dr yakasa cire idanunshi akanta har saida Maman Aneesarh ta lura da kallon dayakema Kausar, Babban Dr yace “Alhamdulilah she’s perfectly fine yanzu, fracture din ne kawai yarage shikuma with the help of belt din dake jikinta she will be fine, yanzu dai tai brush agoge mata jiki ta chanza kaya abata abinci taci dakuma lots of fruits, let’s watch her for 24hrs and see idan babu any complication zansa Dr Khalil here my son yazo yasallameta, zanje wani board meeting ne gobe” atare dukansu sukace thank you, Dr yawuce tareda Dr Khalil daketa kallon Kausar, komawa dakin sukayi Gwaggo zataje bayi debo ruwan zafi dasauri Sajida tace “Gwaggo ki zauna ki huta mu zamu debo” murmushi Gwaggo tayi tace “Allah shimiki Albarka” ruwan zafi tadebo sannan tafito tabude akwatin dake dakin taciro wani soft towel da brush, dan dago gadon kadan akayi da kyar ta iya jurewa tazauna kaman zatai kuka brush Sajida ta mata da taimakon Kausar tana zubawa awani kwano tawuce taje ta zubar abayi sannan Sajida tashiga goge mata jiki, bakaramin dadi Lujain tayi ba dudda tanajin kunya, wani half gown black na spongy Gwaggo takawo tace “ga wannan rigan zaku tayata sawa” Hajiya dauke kai tayi ganin yanda Lujain kejin kunya da bargon gadon ta kare kirjinta dazata cire nata rigan aka samata wani sannan ta ture bargon Gwaggo takawo turare aka feffesa mata da hula aka dan rufe gashin tai wani kalan simple kyau saiga Mama dasu Samira kaman sunsan ta tashi hardan murmushi saida Lujain tayi dataga yan uwanta saikuma ga Anty Binta da kunu.

Abee na zaune a office tareda Musty kiran nan yashigo, yana katse wayan yawani kalan daukan key dagakan table dasauri Musty yace “sai ina” batare da Abee ya kalleshi ba yace “Lujain is awake” cikeda farin ciki Musty yace “ohhh Alhamdulillah” biyo bayan Abee yayi atare suka shiga mota, gudu Abee yake agaban wani flower shop ya tsaya katse motan yayi yabude kofa Musty yabishi da kallo yana murmushi wato idan Allah yay shirin kamaka yana kamaka ne well look at Imran who would’ve thought Imrana zai taba so wata aduniya, just look at the small girl da jikinshi ke rawa akai, yana zaune nan cikin motan Abee yafito daga flower shop din rikeda wani red and white roses da aka hadasu tare sukai bala’in kyau ga dan tag akansu na get well soon wife, baki Musty yakama yana kallon Abee daya shigo cikin motan hararanshi Abee yayi baice komiba, Musty yace “wai haka ka iya soyayya dama Imrana banda labari wlh, iyye” tada motan Abee yayi yaja motan batare daya kula Musty ba, agaban wani super market ya tsaya yasake shiga, wani pink babban teddy yasaya mata da wasu lafiyayyen chocholate mai kyau sosai, dasu pringles, da biscuit, yabiya kudi yafito bude bayan mota yayi ya ijiye sannan yadawo gaba yashiga yazauna rufo kofan yayi yay shiru batare daya tada motan ba yana tunani Musty yace “what?” Ijiyan zuciya Abee ya fuzar ahankali yace “I can’t believe I lost my child” dafashi ahankali Musty yayi yace “Allah daya baka zai kara baka wani, kaida kake sharp shooter ma” hararan Musty yayi yatada motan yaja zuwa asibitin.EPISODE 1️⃣0️⃣9️⃣

Duk suna zazzaune adakin Gwaggo ita tama koma carpet ganin Allah yariga yabama Lujain masu kulada ita sama da ita ma aduniyan nan tana kallon kowa suna magana da Mama dakuma Gwaggo dan su ukun ne ke kan carpet, su Kausar dasu Samira duk suna kan gado, Kausar nabata kunun abaki da spoon tanasha ahankali, Anty Binta kuma na kansu supervising yanda Lujain keshan kunun, Lujain tarame idanunta sun fada ciki sosai amman kaman kyanta yakaru ne, duk suna zaune ahaka aka bude kofan dakin da sallama chan kasa ciki ciki dasauri kowa yajuyo harda Lujain, Abee ne tsaye gaban dakin yana sanye dawani black suit dayamai kyau sosai hannunshi rike da flowers din yahaderai kaman baitaba murmushi ba ganin yanda yara suka cika dakin, gefenshi kuma Musty ne yana rikeda teddy, da sauri su Kausar dasu Samira duk suka sauka daga kan gadon ganin Abee, Su Sajida sukace. “Sannu da zuwa Ya Imran” Kausar tace “Abee sannu da zuwa” su Samira sukace “ina yini Abee” dan sunji haka ake cemai, gyadamusu kai Abee yayi batare daya amsaba sannan yashigo dakin anatse batare daya kalli kan gadon ba yadan kalli Hajiya da Gwaggo da Mama yace “ina yininku” atare dukansu sukace “lafiya lau Imran” Gwaggo tace “barka barka ta tashi Imrana je kaji kaga matarka” dan juyoda kanshi Abee yayi ya sauke kwayar idanunshi kan Lujain dake kwance kan gado tana wani irin kallonshi kaman yaune rana na farko data fara ganinshi zuciyanta na bugawa abnormally, tana jin tafiyan wasu butterflies acikin cikinta sokawai take yazo wajenta, lumshe mata idanu yayi yabude batare data karasa gaban gadon ba, wani kalan hawaye ne suka bulbulo suka cika kwayan idanunta tana kallonshi ahankali tadaga hannunta tamikamai alamun yazo yariketa kowa na dakin hatta Musty yabisu da kallo is just like kowa nason love story nasu, kowa kuma nason yanda Lujain kemai kaman har karaman baby shi kaman wata his last born, Abee duk yanda yaso yadaure sabida mutanen dakin kasawa yayi yakarasa gaban gadon yana wani kalan kallon cikin kwayan idanunta gently yasa hannunshi yarike hannunta batare dayace uppan ba but the whole thing is like zuciyoyinsu na magana, fashewa dawani kalan kuka Lujain tayi kaman ba Lujain din da dazun nan take murmushi take shan kunu ba, wani kalan sangartaccen kuka takema Abee daya rikemata hannu yana kallonta, kasa daurewa Gwaggo tayi tace “ammandai Lula akwai tabara jama’a, Hajiya ba nan nan muke ganin yarinyar nan taga yan uwanta dasu Kausar sai murmushi take musu suna hira Kausar na bata kunu ba shine yanzu taga mijinta tana kuka uwa tsungulinta muketayi tun dazu, yau naga iya shege, yaushe Lulu takoyo wannan tabaran” dasauri Musty dake rike dariyanshi yace “Gwaggo zomuje waje muyi magana” tashi Hajiya tayi itama takalli sauran yaran tace “kumuje” dukansu fitowa sukayi daga dakin saida Abee yaga sun fita am maida kofa an rufe yaduko da kanshi ahankali lumshe idanunshi yayi kafin ahankali ya manna mata kiss agoshi.EPISODE 1️⃣1️⃣0️⃣

Yadade ahaka sannan yacire lips nashi daga forehead dinta kafin ahankali yasake dago kanshi yana kallon kwayar idanunta, murya chan kasa yace “stop crying I am here now” gyadamai kai tayi yakai yatsanshi ahankali ya sharce hawayen dake bulbulo mata daga gefen idanunta yana kallon kwayan idanunta stilll kafin gently yadaura lips nashi kan nata, ijiyan zuciya suka sauke dukansu atare sannan gently Abee yashiga kissing nata, irin kissing din dake holding so many messages yana gayamata how much yake sonta and how much he misses her, ahankali itama take maidamai da kiss din sun dade ahaka kafin ahankali yazare bakinshi dagakan nata batare daya raba fuskokinsu ba murya chan kasa yace “I love you Baby” hannayenta tadaga ta rungumeshi so tight tace “I love you nima sosai” dasauri yakalli fuskanta yace “kina sona Lujain?” Gyadamai kai tayi dasauri tace “ina sonka sosai” kissing dinta yasakeyi sanan yasaketa, dan dago gadon kadan yayi sannan yawuce yadauke teddy bear a inda Musty ya ijiye Abee yadawo gaban gadon yana kallon yanda take kallonshi, Teddy yafara bata, amsa tayi ahankali tana murmushi kafin yabata flowers din shima karba tayi takalli abinda tag din yafadi kafin takai fliwers din fuskanta kamshi sosai suke sannan ahankali yabata ledan budewa tayi chocholate tafara cirowa da sauri tabashi ashagwabe tace “ka budemin” hancinta yadanja yace “sweet tooth kawai” bude mata yayi yabata karba tayi takai bakinta shikuma ya zauna kusada ita hakan yasa ahankali tadaura kanta akan kafadarshi takai hannunt kan cikinshi tarikeshi tanashan chocholate din ahankali shikuma Abee na kallonta kaman yau yafara ganinta sun dade ahaka sannan tajuyo takalleshi ahankali tace “dama inada ciki”? Shiru Abee yayi batare daya bata amsa ba, hawayen dasuka zubomata daga idanu ne tashare dasauri ahankali tace “that Man yabugamini kuje……” yatsanshi Abee yasa akan lips nata murya chan kasa yace “I know everything” ga mamakinshi ahankali Lujain tace “I lost my baby” kankameta Abee yayi yace “I will give u another one kikaji sauki” dasauri takalleshi childishly tace “da gaske?” Gyadamata kai yayi, dasauri tace “inason yara sosai” ahankali yace “inhar kina barina to sex you da kyau zakiyita samun yara” adan kunyace ta rufe fuskanta tana dan murmushi daidai ana knocking kofar da sallama hakan yasa Abee yatashi yace “shigo” bude kofan akayi Baba ne dasu Baffan ta adan kunyace Abee ya sunnar da kanshi kasa.
****
Chapter 112 · 0% Book details