← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 113

Sashe 17

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Dan gyaran murya Abdul yayi yakalli Gwaggo yace “Kaka mu bangaren police muna bukatan video da statement naku dazaku bayar amatsayin shaida cewa sudin mata da miji ne sabida duniya tagani hakan zai siliencing kowa kafin ayi tracking yaron shima muna kan hakan” dasauri Gwaggo ta ijiye kwalin tace “to fara dani” kunna video yayi yace “Kaka waye Imarana” washe baki tace “mijin jikata ne, jikata matarshi ce” yama su Baba dasu Baffa sannan yama Hajiya tace “Lujain Matar d’ana ne” saida yagama sannan yay murmushi yamaida wayan aljihu yazauna dakin aka karayin shiru anatse Liman yace “Alhamdulillah yanzu an daura aure Imrana Lujain matarka ce yanzu sai magana tagaba aahhh yaushe zata tare”? Gamgam Musty yarike hannun Abee dayaji na rawa sosai, Baba na shirin magana Gwaggo tace “zakudan bamu kwanaki mudan shirya, tunda yau litinin ranan asabar idan Allah yakaimu mahaifinta dakanshi zai kaita dakinta ko”? Gyadamata kai Baba yayi yace “in sha Allah” Gwaggo tai murmushi tace “yanzu ma dan tai bacci ne dana turota ta gaisheku tunda nake bantaba ganin Lulu tai irin kukan datayi yauba har muka dawo gida har magrib kuka yarinyar nan take Allah dai yasaka muku dagakai Imrana har Matar taka Lujain, kutashi kutafi gida shima yaje yahuta Allah kadai yasan yanda zuciyanshi ke tafarfasa Dan mutum kamili dashi wani gantalalle chan Ya batamaka suna ana kiranka da fasiki, Allah ubangiji ya saka muku yakuma bimuku hakkin ku, yanzu fa anxama daya zamu hadu mu kare mutunci yaranmu ne murufa musu asiri, kai dan nan idan akwai wani video dakakeso nayi kuma kazo zan maka In har hakan zai kawo saukin lamarin nan” dan murmushi Abdul yayi, Baba Liman yatashi hakan yasa Gwaggo da kowa na dakin suka tashi gaggaisawa akayi Gwaggo da Hajiya sukai sallama sannnan har waje suka rakasu suka tafi.EPISODE 1️⃣4️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Gwaggo kotakan su Baba batabi ba bangarenta takoma tana shiga tamaida kofan dakinta tarufe tasaka sakata ta ijiye kwalin sweet da goron data shigo dashi akasa sannan tawuce uwardakan tana kallon fuskan Lujain dake kwance kan gado daure dawani farin towel kanta babu dankwali idanunta sun kumbura sosai da fuskanta ma, karasawa gaban gadon Gwaggo tayi tazauna ahankali tana kallon fuskanta murya chan kasa tace “bantaba sanin kankanin abu na faruwa ba dazai kawo wani rayuwanka wanda hakan yake kaman aya agareka ne sai akanki Lulu, ninafi kowa sanin yanda kikeson wannan gantalallen dan kwallon Mandawari, yau agabana kika fasa zunzurutun asusunki kika kaima wanan kuran kudin Samira dan kawai ta aramiki waya ki kalli dan daudun mesaka hakorin makka, ni tsabagen yanda nama tsani yaron da kullum kike nunamini awaya idan yana magana zan ma iya zanashi da pencil naganshi, ranan sabida shi bokon ma bakiso zuwa ba dan kada yazo baki kalli video ba amman Allah bless yasa kikaje makarantan, jibidai yanda nida idona da muna kallon video naga bayin dakiketa nema akasa ki shiga baki ganiba domin Allah ya daukemiki idanun awajen so yake kije sama kihadu da Imrana, kikaje saman kika bangajeshi kika bata mishi kaya da fanta amman fuskanki nakan waya shaidanin nan kike kallo kika wuce bayi nafi kowa sanin yanda kike neman waje shiru ki natsu duk sanda zaki kalli Mandawari dan ko ni nan idan zaki kalla uwardaka kike shigewa ko nazo ina kwalamiki kira shiru kike ki kyaleni” shiru Gwaggo tayi sannan ahankali tace “Allah ne ya aiko miki Imrana diyata, shima kuma Allah ne ya aikamishi ke rayuwanshi saikuma Allah yakaddara cewa ba kaddara mai dadi bace zata fara hadakuba hasalima na batanci ne, na kalli fuskan yaron nan nakara kallo babu abinda nagani kan kwayan idanunshi Sal dumbin alkhairai, nasan baki sonshi shima bayi sonki, baki sanshi ba bai sanki ba amman kuma Allah yahadaku! Allahandaya hadaku shinake roka ya dawwamar daku awanan rayuwan Auren har abada Allah yasamishi sonki da kaunar ki dakuma tausayinki kema Allah yasamiki haka, koyau nafadi namutu Alhamdulillah, kullum banda zullumin daya wuce wazaki aura wazai auri Lulu na, amman kinga wannan mutumin yanada yara da sunma girma miki Dan haka ina mai kyautata zato zai iya tafiyar dake da kyau” hannu tadaga ta tottafa addu’a sannan tashafama Lujain a fuska kafin takashe wuta ta kwanta kaman jira Lujain take kankame Gwaggo tayi Gwaggo tace “ahap aini nasani duk yanda takai ga bacci inhar taji dumin mutum saita kwakumeshi” kafin kaceme Gwaggo tafara jan minshari.

Suna kaiwa gida Abee bai kula kowaba fita yayi daga motan dasauri yay flat dinsu Hajiya zata kirashi Liman yace “kul Hajiya kubarshi, kubar yaron nan shi kadai yasan meyakeji” yajuya yakalli su Ibro yace “ku kira likitanshi kuji” gyadamai kai yayi sannan Baba Liman yace “saida safen ku” godiya duka sukamai yawuce, Musty da Harun ma sukama Hajiya sallama dan tun ahanya suka sauke Abdul ya sauka a police station dinsu sukuma sauran suka shige gida.
Chapter 17 · 0% Book details