Sashe 77
Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
narke agado tana sharan bacci, binta da kallo Gwaggo tayi dan sai yanzu take ganinta da kyau data daura towel karasawa cikin dakin tayi ta tsaya akanta kawai tana kallonta kaman yau tafara ganinta saikuma ahankali tasa hannunta tadauki hannun Lujain daya tana duba tafin hannun kafin ahankali 53| ta ijiye wani kalan murmushi kawai tayi tace "yi baccin ki Lulu Allah dawo da babanki daga kasuwan zansa yakirasu, bari naje nayo cefene namiki lafiyayyen abinci nakuma hadamiki magunguna" Gwaggo tai maganan tana daukan hijabinta da lalitar ta tafice, Gwaggo ta tsufa amman karfinta na nan abin mamaki yake bama yan anguwansu, babu wani kwana da lung na kasuwa dabata sani ba ko abu kakeson saya a kasuwa kazo ta tambayi Gwaggo a ina zaka samu zata maka kwatance. Har Gwaggo tadawo daga kasuwa tayi duka girke girke da dafe dafen abincin dazatayi da magungunan dazata dafa Lujain bata tashi ba, harsu Samira suka dawo daga school Gwaggo dukta hanasu kada su tadata abarta ta tashi dan kanta cewa tadata zai samata zazzabi, sai wajajen 3 a yamma Lujain ta tashi daga baccin, ahankali ta tashi zaune jikinta is sooo weak sauka tayi daga gadon tawuce tashiga bayin Gwaggo wanka tayi da ruwa mai zafi sosai tafito daure dawani sabon towel, zama tayi abakin gadon daidai Gwaggo tashigo tace "kin tashi" gyadama Gwaggo kai tayi tana yatsine fuska tace "Gwaggo salla nakeso nayi amman jikina babu karfi ko kadan wh" dan murmushi Gwaggo tayi tace "sannu bari nakawo miki abinci kici zakiji karfi saikiyi salla" kuloli Gwaggo tashiga shigowa dasu kusan guda 6, zaro idanu Lujain tayi Gwaggo ta zauna tace "sauko kasa kema" tashiga bude kulolin, daya soyayyan kaji ne sun soyu kayau irin suyan tsofaffin nan, daya wani farfesu ne, daya shinkafa da miya, daya taliya da miya, saikuma daya burabusko da miyan kifi, yatsine fuska tayi jin kaman zuciyanta ya tashi dataga kifin tace "Gwaggo rufe wannan banso" dasauri Gwaggo tadauka tarufe tace "to, nadama miki kunun gyada, ga Samira chan das Abida suna sova mashe zasu kawo miki" Gadamata kai tayi tadauki naman kazan tafara ci, babu mai sangartata aduniya kaman Gwaggo tun tana yarinya bata taso tanacin abinci kala daya ba saidai kaloli dayawa, she miss her Gwaggo so much kusan komi saida ta taba amman ba kaman da ba dasauta cine komi abin mamaki yabama Gwaggo saikuma tai shiru tunanin wani abu datayi, kunun gyadan nema tasha sosai, sannan tamike tace "bari na kuskure baki nai salla" fitowa tayi daga bayi tasa hijab tai azahar daidai ana kiran la'asar, sallan la'asar din shima tayi sannan tamike tafita falo jin hayaniyan su Abida afalo nan fa ta watsake kaman basu Abida dakoda yaushe suke fada ba sai hira suke sunyi kewanta haka itama, taci mashen sosai kuma Gwaggo sai murmushi take tana dama mata wasu magani. 4 dot as usual agaban makarantan tama Hamza, sauke glass kasa yayi yana kallon yanda yan makarantan ke fitowa amman bai hango Lujain ba da kullum idan vazo daukanta tana cikin yan sahun farko zaka ganta tafito agajiye tana shigqwa mota zata fara gyangyadi, ganin student sun kare har baya ganin kowa cikin makarantan yasa yabude motan yafito yaje wajen security yabasu hannu vace "Lujain Muhammad fa ko zaku dubamin ajinsu"? Dasauri security yace "ai yau batazo makaranta ba" zaro idanu Hamza yayi yace "what are you saying" saikuma kawai yawuce yashiga ciki ganin kaman basune yagani a gate dasafe ba maybe suna shifting ne, direct class nasu Lujain vawuce babu kowa a ajin saiwata teachers dake tattare kayan lesson note nata ganin Hamza tace "how can I help you sir"? Anatse Hamza vace "Lujain Muhammad"? Dasauri tace "ohh Lujain batazo school yau ba ai, who are you to her"? Baison yay causing wani matsala yasa kawai yace "never mind" yajuya wayanshi yashiga cirowa yay dialing number Abee. Abee na cikin meeting dawasu arab wayanshi yay vibrating kallon wayan yayi gain Hamza yasa yay dan jim why is he calling him around this time na tashin school su Lujain, tashi yayi yadanyi excusing kanshi yanama Ibro alamu da idanu yacigaba da attending to them yafita daga conference room din ya tsaya a corridor yakai wayan kunne batare dayace komiba, cikeda damuwa Hamza yace "Ya Imran can you hear you" anatse yace "yes" cikeda damuwa Hamza yace "gani nan a school din su Anty Lujain, Ya Imran kowa yafito banganta ba I asked the securities wai batazo yauba, bayan da kaina na sauketa yau da safen nan, shine nashiga ciki to their class I met one of teachers nasu she assured me cewan yau batazo school ba banson na nuna something happen kawai shine nafito nakiraka what should I do? Konakira gida na tambaya kota koma maybe yau bata tsaya tayi lesson bane, mezanyi Ya Imran" dudda yanda kirjin Abee ke bugawa but daurewa yayi batare daya nunaba anatse yace "don't call anybody just stay there ina zuwa" katse wayan Abee yayi sauri sauri gudu gudu yajarasa office nashi yadauki car key shi yawuce yafito yashiga mota. Ko 5mins baiyiba yay parking babban motanshi agaban school din dasauri Imran dake tsaye yay wajen saukowa Abee yayi yakalleshi daidai asalin mai school din abokin Abee na zuwa parking yayi suka shiga ciki direct to his office, wajen babban computer shi dake wajen sukayi ya kunna yace "around what time kuka iso nan Hamza" dasauri yace "around 7:50 thereabouts" CCTV footage na that time mai school din yaciro Abee na kallon screen din, ga lokacin da Hamza ya ijiyeta nan yajuya ga lokacin dataje waien mai motan taleka tana magana sai chan tabude tashiga lumshe idanu Abee yayi ahankali, mai makarantan yace "bata shiga school dinba at all saisa sukace yau batazo ba" gently Abee yamike tsaye ahankali yace "sorry for bothering you" murmushi yayi yace "kaga Imrana da magana kaima kasan i can do anything for you" murmushi E3 Abee yayi yafito Hamza biyedashi abaya saida suka fito waje yakalli Hamza da dan idanunshi dasukai ja kadan yace "not a word to this to anyone" gyadamai kai yayi dasauri yace "to Ya Imran" anatse Abee yace "just go home idan ance tana ina tell them she's with me" gyadamai kai {Hamza yayi yawuce yashiga motanshi yatafi shikuma Abee yakoma motanshi.Abee yadade zaune cikin motanshi kaman ya kurma ihu vakeji yasan babu inda taje sai gidansu, gashi kunyan zuwa shikadai yake baima dace yaje shi kadai ba, yanzu dole saiya nemi Musty kenan why is this girl putting him through this mess, maisa yara sun cika matsala ne da problem eh. 834 @ Wayanshi yaciro yadade yana kallon wayan kafin yaciro number Musty yay dialing ringing daya Musty ya dauka yace "how far Ango" dan shiru Abee yayi kafin ahankali yace "kana ina?" Anatse Musty yace "gani nan yanzun E3 nan nabar office a barrack driving home to my beautiful wife" dan shiru Abee yayi saikuma ahankali yace "kaje gida ka chanza kaya kasameni a company zamuje gidansu Lujain bayan magrib" dan zaro idanu Musty yayi tunda yaji muryan Abee yasan dawani abu saikuma ahankali yace "what happen Imran"? Shiru Abee yayi kaman bazai amsa ba saikuma chan yace "this girl is frustrating me Musty, I don't even know how to handle Lujain again, she's so stubborn tagudu gida, she's driving me crazy can't even think straight again kaman bani ba" tunda yake maganan Musty murmushi yake yanda Abee ke maganan kaga wanda yanda Abee ke maganan kaga wanda tsantsan soyayya ke wahalarwa, daurewa Musty yayi batare daya nunamai komiba yace "Imran common she's just a child dole you have to bring yourself down to her level and understand her" ahankali Abee kaman zaiyi kuka yace "bazanyi ba da girmana zan tsaya ina abin yara" wanna karan saida Musty yay dariya dan already he's doing it baima sani ba, yace "gani nan zuwa yanzun nan" tada motan Abee yayi yawuce company shi. 834 5:57 PM Da magrib Musty ya iso anan masallacin kampanin Abee yaga Abee tare sukai salla sanan suka koma ciki chanza kaya Abee yayi zuwa manyan kaya daga suit, sannan suka fito Musty ke driving yace "zamu tsaya muyi siyayya fa so bani ATM card naka" babu musu Abee yabashi agaban wani super market yay parking yasauko yashiga ganin Abee baidama energy fitowa, siyayya Musty yayi harda na Allah ya isa aka fiffitonai dashi aka loda a jeep, sannan yadawo yajefamai card din Abee yamai wani mugun kallo Musty yace "wlh ka karamin wannan kallon barinka zany katafi kai kadai, nasan meka mata dayasa tagudu gida yanzu danzan rakaka kana kallona kaman zaka kasheni da idanu" dauke kai kawai Abee yayi Musty yay dariya koda sukakai anguwan ana kiran isha'i hakan yasa suka shiga mosque anan sukaga Baba ma da shima dawowanshi daga kasuwa kenan mamaki yayi ganinsu ganin baisan komiba yasa dasauri Musty yace "munzo gaisheku ne Baba saimu tafi da Luiain ai tun safe tana nan" bakaramin dadin hakan Baba yajiba yace "aiko bansani ba ya akayi Gwaggo bata kirani tafadi mini ba" atare suka fito daga masallaci Baba yace "bari nashiga ciki nazo" side din Gwaggo yawuce dasauri ita kadaine dan Lujain na Dakinsu Samira yace "Gwaggo ga mijin Lujain da abokinshi sunzo gaishemu" washe baki Gwaggo tayi tace "Kawomin su nan bangarena" Gyadamata kai Baba yay yawuce yafita yashigo dasu Abee kan Abee akasa Musty nema ke hira da Baba har dakin Gwaggo, duk akasa suka zauna Baba yace "bari naje na sanar dasu" hakan yasa daga Gwaggo sai Musty afalo dan rage murya tayi kaman wacce zatai gulma tace "nagode muku da baku fadamai gudowa gida tayi daga makaranta ba dan bakaramin aikinshi bane yahau jibgan yarinya datake ba ita kadaiba ina dalili" tai maganan tana kallon Abee dakanshi ke kasa tace "wai Imrana anya ma kasan matan naka juna biyu ne keda ita kuwa!" Wani kalan dago kanshi Abee yayi dasauri yakalli Gwaggo, cikeda jin dadi Gwaggo tace "ita kanta batasani ba kasan yau tunda tashigo gidan nan wajajen takwas da rabi take bacci sai wurin uku na rana ta farka, gashi batada kuzari, saida nadubata kasan lokacin nan damuna kauye nice unguwan zoman kauyen mu ai saisa nasan magunguna da sauransu, dana dubatama duka duka cikin baima gamakai sati hudu ba, karamin