← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 113

Sashe 107

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana parking yazagayo zai dauketa, makemai kafada tayi tace “ni dakaina zanyi tafiya” matsawa gefe Abee yayi ahankali tasauko yamaida kofan yarufe, hannunta yakama yarike batare daya biyemata ba suka shiga tafiya ahankali dan da kyar take iya tafiya, har cikin asibitin, direct office na Zuzu suka wuce knocking yayi tareda bude kofa tana ganinsu tace “yauwa Yaya daman kunake jira dannatafi gida yau night nayi, Hello Mrs Imran” sauke kanta kasa Lujain tayi adan kunyace tace “ina kwana” murmushi Zuzu tayi takaraso inda take tace “zomuje naduba ki ancemini kinata amai ko kinsan dalilin hakan” hada ido Zuzu tayi da Abee dayamata wani kalan kallo dayasa dasauri tace “hau gado naduba cikinki nagane maisa kike amai” Ahankali Lujain ta kwanta gabanta sai faduwa yake Abee takalla sai kawai tafashe da kuka tana mikamai hannunta tace “ni tsoro nakeji Uncle” Abee mantawa yayi da Zuzu na wajen dasauri yazo wajen hannun yakama cikeda so yace “shiiii stop crying gani nan tareda ke” murmushi Zuzu tayi ta daga hijabinta tareda daga riganta sama, tajawo machine na scanning gaban gadon tazuba mata wani abu aciki tadaura injin din takalli Abee tareda murmushi tamai alamu daya kalli screen din, ahankali Abee yake kallo ga babyshi nan dudda dan kankani ne baka gane komi but is his child, abin da Dr Zuzu tazuba acikinta Lujain takalla wani sabon amai taji yazo mata dasauri Zuzu tabata kwanon amai Abee yadan dago kanta sai amai taje na misting yellow ruwa babu komi ciki, saida tagama tabata ruwa ta kuskure Zuzu tagoge abin cikin nata tass sannan tace “sorry ko, yanzu zan rubuta magunguna da zaku saya zanso namiki allura” dawani kalan sauri Lujain ta diro daga gadon tashige jikin Abee tanason tafashe da kuka, hakan yasa Abee bako kunya yace “banson kimata allura just give us drugs” dan dariya Zuzu tayi ganin ikon Allah tace “ai shikenan” tawuce table dinta tana satan kallonsu ta wutsiyar ido yanda Abwe ke lallashinta yana gayamata maganganu da ita kanta Zuzu dake office din bata jinsu, saida tagama rubuce rubucen tass sannan tabasu takardan karba Abee yayi yace “thanks” jakanta Zuzu tadauka tace “uw” wucewa Abee yayi yafita tareda Lujain din anan reception yawuce ya zaunar da ita, ko kunyan mutanen wajen baijiba yace “sit here bari na karbo magunguna daga phamarcy sainazo mutafi ko”? Gyadamai kai tayi ahankali tana kallonshi kaman yanda ya tsaya yana kallonta, saikuma ahankali yakai yatsanshi yashare mata dan guntun hawayen daya zubo yace “stop crying ingoyaki”? Makemai kafada tayi dasauri ahankali yace “to me kikeso? Kukan nan nadamun zuciyata, me kikeso namiki”? Murya chan kasa tace “ni ka kaini wajen Gwaggo na zan daina aman” shiru yayi yana kallonta ahankali yace “nikuma yaya zanyi kikaje chan zaki iya tafiya ki barni”? Gyadamai kai tayi ahankali, yunkurin tashi yayi adan zuciye dasauri tarikemai hannu for the first time tasaki murmushi tace “ai dakai zani Gwaggo na ai Gwaggon kane kaima” ga mamakinta murguda mata baki yayi hakan yasa ta kwalalo manyan idanunta, saikuma tashiga bin wajen da kallo irin taga ko wani yaga abinda Abee yayi hada idanu taga kaman tayi da Mandawari zata kara gasgatashi tagani Abee yace “wakike kallo Mrs Imran”? Dasauri tajuyo takalleshi tace “dubawa nayi naga how many people sukaganka ka murgudamin baki” dan murmushi Abee yayi yace “tom yanzu dai lemme get ur drugs zamu karasa magana din amota” gyadamai kai tayi Abee yatashi yawuce dasauri tajuyo da kanta zuwa inda taga kaman taga Mandawari wani mutumi tagani daban to maybe idanunta ne amman saitaga kaman shitagani.

Tana zaune awajen tanabin kowa da kallo bakinta babu dadi jikinta babu dadi aka shigo dawani mara lafiya daya kone jikinshi yay alamun kuna jitayi zuciyanta yatashi amai yazo mata sosai, ganin tana neman tai amai awajen yasa dasauri ta tashi ta taushe bakinta, ganin aman yazo kaman ana turoshi yasa ta kwasa da gudu tafita daga reception din, wajen da akai parking motoci taje ta dugu a tsakankanin wasu motoci guda biyu sai amai, sosai tayi aman awajen tana duke, ganin kaman mutum agabanta yasa ahankali tadago kanta, ido da ido tayi da Mandawari dataga yarame yayi duhu kaman ba farin Mandawari data sani ba ga hannunshi da alluran drip makale alamun baida lafiya, dawani kalan sauri tamike tsaye baki tabude zatai magana kawai Mandawari yakai hannunshi yadaki gefen wuyanta daidai wajen dake sa mutum yasume ko zare hannunshi baiyiba Lujain ta sume tai baya zata fadi yatarota dasauri yadauketa chak yakifa fuskanta akirjinshi yafito daga lungun motan yana tafiya da ita dasauri dasauri zuwa wajen motanshi yana zuwa yabude bayan ya wurgata yakoma gaba dagudu yashiga yaja motan yabar asibitin..EPISODE 9️⃣9️⃣

Daidai an bama Abee ledan drugs nata a pharmacy kawai yaji gabanshi yawani kalan fadi ledan na fita daga hannunshi yafadi akasa dasauri pharmacist din yace “Sir are you okay”? Gyadamai kai Abee yayi ahankali ya tsugunna yashiga kwashe magungunan yamaida aledan sannan ahankali yamike tsaye taredakai hannunshi yadaura akan kirjinshi dayake wani kalan bugawa yafito daga corridor da phamarcy ke ciki zuwa reception yana kallon kujeran da Lujain kekai yaga wayam batakai, dasauri yay office din Zuzu kotaje amai taje chan tayi ne, ayanda yabude kofan office din Saura kadan kofan yabugi Zuzu dake shirin fitowa dan tundazu wayane ma yariketa data tafi gida, baimabi takanta ba office din yashiga dasauri yace “is Lujain here”? Dasauri Zuzu tace “a’a Ya Imran bata shigo nan ba” juyawa yayi yafito dasauri yayi wajen kujeran datake zaune Zuzu tabiyoshi dasauri abaya ganin kaman ba lafiya, jama’an dake wajen Abee yace “sannunku dan Allah kuga Yar yarinyar dake zaune anan datasa maroon hijab”? Dukansu girgiza mai kai sukayi sai wata Yar tsohuwa ce tace “naga ta tashi dagudu tafita waje tana taushe baki uwa wacce kejin amai” cikeda farin ciki Abee yace “thank you” yayi hanyar fita daga reception din Zuzu biyedashi, karo Abee yaci da mutane tsabagen saurin dayake baima tsaya kallonsu ba yafice Hadi ne da Abee ya bangaje yace “kai ba mijin Lujain bane wanchan ba incedai lafiya” dasauri kaninsu yace “gaskiya muje muji Ya Hadi ko lafiya” suna maganan suma suka juyo, babu wajen da Abee bai duba a premises na asibitin baiga Lujain ba har motanshi yaje babu ita, Zuzu tace “to ina zata Yaya? Bamata da karfin dazataje wani waje”? Daidai su Hadi sun karaso wajen hannu yamikama Abee da kyar Abee ya iya basu hannu duk ya rude sai kalle kalle yake, Hadi yace “lafiya kuwa Imrana”? Zuzu ne tace “Lujain batada lafiya yanzun nan sukazo yabarta a reception yaje yasayo magani baiganta ba ance tafito nan shine muke dubawa amman bamu ganta ba” dasauri Baffa Hadi yace “har yanzu Lujain bata daina shirmen nan ba, Allah kyauta nima nazo duba wani abokin aikina ne da aka kwantar dashi anan jiya ciwon sugar, bari mutayaku nemanta mu rarrabu tukunna” Abee yakasa magana sabida yanda gabanshi ke faduwa he’s feeling so uneasy, to kodai tagudu wajen Gwaggo ne datacemai yakaita, but no barata iya guduwa tabarshi ba, duk girman asibitin nan kaf suka duba dan Zuzu harsa security tayi suka shiga tayasu gabaki daya babu Lujain, ahankali Abee yace “ko zaka tayani kiran Gwaggo ka tambaya” dasauri Hadi yace “to bari nakira Gwaggo naji ko ta tafi gida ne, amman indai nan taje saina saba mata” jiri jiri Abee yaji yanaji hakan yasa ahankali yadafa bango saikuma ya tsugunna tareda runtse idanunshi trying to be strong sabida yanda zuciyanshi ke tsinkewa, dasauri Zuzu tadafashi tace “Yaya don’t worry Lujain is fine babu abinda yafaru kaji” cikin muryan da baya fita sosai ahankali Abee yace “something happened I can feel it Zuzu in my heart, my wife is not safe” yay maganan yana kallon Baffa Hadi dake waya da Gwaggo, ganin yakatse wayan yasa Abee ya mike tsaye ahankali yana kallonshi, har addu’a yakema acemai tana wajen Gwaggon, anatse Baffa Hadi yace “wlh bataje gida ba” daidainan wayan Abee yay kara alamun sako dasauri yaciro wayan hannunshi har rawa yake, wani unknown number ne yamai messege.
“You will never see her again!”.
Wani kalan faduwa wayan yayi daga hannun Abee zuwa kasa Abee yay baya baya baya yana tafiya da baya baya, dasauri Zuzu tabishi tace “Yaya, Ya Imran menene”? Baffa Hadi dasauri yaduka yadauki wayan yakaranta sakon yana nunama kaninshi Abee nakaiwa jikin glass door na reception din wani kalan mahaukacin duba daya yama kofan, kofan yawani kalan tarwatse kararara!!!.EPISODE 1️⃣0️⃣0️⃣
Chapter 107 · 0% Book details