Sashe 20
Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Yau Friday tun ranan Monday bayan an daura auren nan dasuna shigowa gidan Abee yawuce dakinshi dagudu rabon kowa dayaganshi ko masallaci baya fita, Ya kulle dakinshi baya karban abinci yanda za’a kawo abinci a ijiye gaban dakin haka zaa dawo adauka, shigowa gidan Musty yayi afalo ya zauna yana kallon yanda Hajiya dakowa yay jugum ahankali yace “har yanzu bai fitoba Hajiya”? Wani kalan ijiyan zuciya Hajiya ta sauke tace “ai inhar ciwon nan yatashi saikuma yanda tayu, har yanzu likitan nashi”? Ahankali Musty yace “gashinan zuwa Ibraheem yadaukoshi daga airport” shiru dakin yasakeyi babu wanda keda walwala Kausar da Abdallah yakalla sun bashi tausayi yauma basuje makaranta ba, jin karan gate yasa Musty yaleka yace “Alhamdulillah gasunan” Dr na shigowa falon baima tsaya gaidasu ba yace “give me his room key” ciro key Hajiya tayi daga Yar purse na hannunta yawuce sama kowa na zaune akasa, kusan 30min yayi aciki sannan yasauko kowa tashi tsaye yayi yana jiran abinda zaice dan murmushi Dr yayi yace “ku kwantar da hankalinku he is fine” ajiyan zuciya kowa yayi, Mustafa dake kallonshi yace “Dr maisa yake kulle kanshi yaki fitowa duk yanda Imran yakaiga son bautan Allah jam’i baya wuceshi zakaga hatta masallacin baya fita yaje, yaranshi dayakeso baya yarda yagansu baya ganin kowa, why is it like that”? Ahankali Dr yace “kasan patient nawa aka rasa to PTSD post traumatic stress disorder? I applaud Imran bakaramin jarumi bane mai kwazoba he’s fighting it with all of his strength, PTSD nakama mutum ne Idan mutum yay experiencing a shocking event, mutuwan matarshi, yanda akai hanging nata sun harbeta a goshi, aka kashe yaranshi in cold blood shine abinda yasa PTSD yakamashi, symptoms nashi shine magrine, da mutum ya tsani kanshi yayita bama kanshi laifi akan abinda yafaru, mutum yay isolating kanshi daga mutane kaman yanda yake yanzu dasauransu irinsu rashin yawanyin magana, gashinan gashinan ne, for 13yrs I’ve been managing him da little medication su Anti depression dakuma psychotherapy, yana zuwa har office dina he talks to me I talk him out of all the guilt the experience dakomi dayake feeling, for a long time now kusan shekara daya kenan baitasomai ba sai ranan Monday din nan shima sabida wannan dan he’s traumatized sabida kazafin da akamai aka kuma yada aduniya yanar gizo, saikuma this sudden Marraige, Auren nan dan gani yake he’s betraying his late wife, yanzu dai I assure you komi yazo karahe, Hajiya inason kije kiyi magana dashi but before then dukku zazzauna inason magana daku gabaki daya” zama dukansu sukayi shima Doctor yazauna yace “all abinda patient na PTSD ke bukata is love and support from close family nasu and friend, ku nunamai kuna sonshi he means a lot to you, sannan kununamai ku bama kusan yana ciwo ba koyanada wani ciwoba duk randa yabude kofan nan dakanshi yafito kuyi mu’amala dashi kaman bakumasan yashiga daki ya kulle kanshi na kusan kwana biyarba baci basha kungane”? Dasauri kowa yace “eh” Dr yace “sannan karkumai kuka, don’t show him pity rather show them love, idan yaga kuna nunamai pity kunamai kuka zaiyi worsen condition nashine dan he will feel yana causing muku pain, karku nunamai kowani abu instaed ma zai iya idan yafito kuce mai babu kaza kaza kaza agida, Abee inada assignment kaza kaza kungane engage him in something life moves on” yakalli Hajiya yace “idan kinje dakin nan ba danki mai lafiya ke magana ba, ba Imran dinki zakigani ba, this one is Imran mara lafiya, PTSD mess with brain Hajiya, so no matter mezaiyi don’t show weakness kokuma kiyi kuka agabanshi, as his mother handle him kaman jariri tell me kinasonshi he’s your everything, sannan idan kin shiga dakin daidai da hasken screen na wayanki kada kisake ki kunna bayason haske bayason hayaniya bayason kuka at this time cus all of that nakara tunamai da traumatic experience na lokacin memory nadawo mishi fresh, idan tadade adakin ku aikamata da abinci kar wanda yashiga dakin abakin kofa zaku ajiye kutafi, babu abinci acikinshi sannan he’s dehydrated, ga weakness kungane” atare duk sukace to, Hajiya share hawayen fuskanta tayi tass sannan tawuce sama, Dr yabi kowa na dakin dasukai jugum da kallo yace “he is fine nan da 24hrs that’s idan yamakai kenan ya warware” yay maganan yana bama Ibraheem prescription sheet yace “he needs this drugs now kuje kusayo” tashi Musty yayi yakarbi takardan a hannun Ibro yace “bari naje nasayo kai Ibro drop Dr at home tunda ba mota a hannunshi” suka fita tare.EPISODE 1️⃣5️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI