← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 113

Sashe 44

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

12 daidai Abee yagama aikin dayakeyi tass yakashe computer sannan yajuyo ahankali yadaura idanunshi akanta gabaki daya atakure take tana gyangyadi kanta na lilo awahale. “Kee!” Wani kalan mugun firgita tayi tabude idanunta dasauri tareda mikewa tsaye tana kallon Abee awani kalan tsorace, mikewa tsaye yayi ahankali tareda zuba hannayenshi acikin aljihun wandon dake jikinshi yafara tafiya yana tahowa inda take, batasan mesaba wani kalan faduwa gabanta yashigayi yawani kalan cika mata idanu yamata mugun kwarjini kasa jure kallon dayake mata tayi dawani kalan sauri tasauke kanta kasa, karasowa yayi gabanta ya tsaya chak hannunshi zube a aljihu yana wani kalan kallonta, tunda take bata tabaganin mutumin dayamata rumfa kaman yanda Abee yamata ba ganin yanda ya tsaya daf da ita ko Baba baya mata rumfa haka, hakanan jikawai tayi kafafunta sun kasa daukanta, dukewa tayi awajen dasauri tana wasa da yatsunta, kallonta yayi cikin kakkausar murya yace “stand up!” Babu musu ta mike tsaye kirjinta nawani kalan bugawa babu kakkautawa bata tabajin kalan faduwan gaba datakeji ayanzu ba wani kalan zati da kwarjini Abee yakedashi da ita kanta bazata iya bayani ba, ganin yanda takasa dago idanunta takalleshi yasa strictly yace “look into my eyes!” Dago idanunta tayi tadaura akan nashi kasa cikakkun 3secs tayi ganin kalan kallon dayake mata zata sauke idanubta kasa azafafe yace “don’t you dare!” kafeta yayi da idanu yana tura hannunshi cikin aljihu yaciro wayan Mandawari tareda nunamata wani kalan ijiyan zuciya tasauke saida yaji saukan numfashin akan fuskanshi gashi ya tsareta da idanu bayako kyaftawa daburcewa tayi daburcewan dabata tabayiba tunda tazo duniya kawai fashewa tayi da kuka, yatsanshi yakai kan lips nashi hakan yasa tawani kalan hadiye kukan tass, anatse yace “kuka nace kimini”? Girgixamai kai tayi tanawani kalan sauke ijiyan zuciya gwanin ban tausayi, ganin yanda take numfashi kaman zata shide yasa ya sassauta murya ahankali Yace “what did I say?” Adaburce tace “kace wayan waye wannan?” Tsareta da idanu yayi alamun yana jiran amsa, lips dinta har rawa suke kaman an jonamata electric shock tace “Maa…….Man…….d…..wari yab……b……bani” tafada dukta burkice, wani irin kallo dayamata yasa taji cikinta ya murda batasan lokacin datace “a school din nan yakawomini” wani irin kallo Abee yamata yace “ina jinki” kuka ne a muryanta sosai amman yahanata yi in that crying tone tace “ina aji security guy yazo yace Yayana nakirana I thought kaine naje naga shine, he asked me yanda akai auren mu, saiya bani wayan yace zai kirani and he’s inviting me to his welcoming party, da……daz….zu ma yaaaaa…..kir……rani” Abee jiyayi kaman ta watsamai garwashin wuta azuciyanshi, nunata yayi da yatsa yace “listen here girl babu abinda zanyi dake, I don’t consider you my wife one bit, ko anjima aka kama yaron nan I will be sending you back to your father’s house batare dana bari kin kara koda kwana daya agidan nan ba, but listen here dagayau don’t ever bring wani abu that belongs to wani namiji into my house kinajina” gyadamai kai tayi dasauri tana tagwayen ijiyan zuciya idanunta na mugun kyalli sabida yanda suka cikada hawaye, cikin zazzafan murya Abee yace “nine nace you can live anyhow and talk to duk wanda kikaga dama and that same me yau na janye! Inhar kina gidan nan kina zama karkashina karki kara kula wani, idan kika kara koda kallon that small boy saina baki mamaki kinajina” gyadamaikai tayi dasauri tace “eh naji” cikin fushi sosai Abee yace “just sit and be praying akamo mutumin nan so that you will get out of my life forever nagaji dake! I am tired of you! Pray akamoshi sabida narabu dake only then you can do duk abinda kikaga dama and talk to duk wanda kikaga dama Imran doesn’t care! Understood” gyadamai kai tayi dasauri, hakan yasa yawuce fuuuuu yafada bathroom nashi, wanka yayi yafito sanye da kayan dayashiga dasu bayin yana fitowa yabude kofa yashiga dakin closet nashi yadan jima aciki sannan yafito dawasu pj dark blue ajikinshi yana wani kalan kamshi hannunshi rikeda wani babban bargo batare daya kalleta ba yace “jeki kwanta akan gado” dan dago kanta tayi takalleshi ganin yay kan dogon couch din wajen yana shirin kwanciya yasa ta tashi ahankali tai kan gadon har wani tsoron hawa gadon take, gadon fes fes bedsheet din fari kal amike kaman ba’a kwana akai, kaman wacce bata bata ganin gado ba tahaukai ta kwanta gadon nawani kalan kamshin turarenshi, bargo taja ta lullube sabida yanda dakin keda sanyi, kashe wutan dakin akayi hakan yasa ahankali tasauke ijiyan zuciya tareda lumshe ido.Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

EPISODE 3️⃣8️⃣

Hakanan jitayi baccin yaki zuwan mata tarasa sukuni bakaramin damuwa ne aranta ba, yace zai saketa dazaran gaskiya ya bayyana amman kuma yahanata magana da saurayinta mai sonta wanda zai aureta dazaran sun rabu, duka maganganunshi dawomata suke, wani kalan kukane yazo mata taushe bakinta tayi da bargon data lulluba dashi tadinga kuka, tarasa farincikin ta rana daya kawai sabida wani mugun shairi dawani mutum yahada mata, dudda Babanta baida kudi Babanta atampopi yake saidawa akasuwa gidansu babu Ac kaman wannan, gidansu is not mansion kaman wannan, babu motoci agidansu kaman irin manyan motocin gidan nan but she has always been a happy person, kometakeso takeci, Baba nadadewa kafin ya yanka musu kaji but Gwaggo koda yaushe tana cikin yanka mata kaji tana soyamata, dudda lokacin Mandawari baitaba kulata ba ko amsa messages nata still she’s always happy, she’s always at each she sleeps peacefully clinging to Gwaggo so tight, but rana daya she lost everything she lost her sweet life, kunya da tsoron fita take, zaman aure take dabama tagane kan Auren ba, zama take a inda batasan kowaba, Mandawari da sunan shine kullum acikin sallolinta biyar finally Allah yahadata dashi he loves her so much har yana bata iPhone IPhone dabata taba rikewa a hannu ba, but Mandawari yabata yay yay inviting nata but she couldn’t show up duk sabida wannan kaddararren auren duk dan sabida wannan shairin da aka mata, Allah kadai yasan yanda Mandawarinta yake fushi da ita yanzu ina zatasa kanta taji dadi, babu abinda kemata dadi aduniya, cikinta ne taji yadaurenata kanta na sarawa, lallashin kanta tasomayi juye juye tadingayi akan gadon tarasa abinda kemata dadi aduniya, daga baya tashi zaune tayi gashi wutan dakin akashe abinda yakara kara mata damuwa kenan, yaye bargon tayi ahankali tasauke kafafunta sama dudda dakin ba duhu mikewa tayi ahankali tana shafa bango kaman mayya tana kokarin locating bayin dataga yashiga dazu, jin ta taba kofa yasa ahankali ta murda kofan tabude wani kalan farin bayine tsaftaccen gaske ita har tsoron shigama tafara dan karta mai datti da bayin ganin yanda hasken bayin ke shigowa cikin dakin yasa tadan juya atsorace takalli kujeran dayake kai ya lullube fuskanshi kadaine ke waje dasauri tashige cikin bayin tareda maida kofan ahankali tarufe, tana kalle kalle, wanke fuskanta tayi da ruwan sanyi takalli fuskan nata a madubi idanubta sunyi jajir sun kumbura sabida kuka, bayin tabida kallo ganin bataga towel ba wani drawer mai bala’in kyau datagani takai hannunta har rawa yake tabude towels tagani kusan guda 10 farare tass anmusu wani kalan rolling ninki sotake tadauka tadaura amman yanda taga an gyarasu awajen yasa tsoro ma yahanata tabawa, bayin tashiga kallo tana kallon sabulan wankanshi kadai kusan 13, different shower gel na maza, da scrubs dakuma set na bubble bath, abubuwan dayake dashi ko ita batadasu bayin sai kanshi yake bude kofan tayi ahankali tafito ta maida tarufe tana daddafa bango tawuce takoma gadon ta kwanta ahankali tacigaba da rolling still takasa bacci sai wajajen 2:30 bacci yay awon gaba da ita.

Tashi Abee yayi ahankali ya zauna dan all this while ba bacci yakeba yan addu’a yayi 3 dot as usual yatashi yawuce bayi alwala yayi yafito yahau kan dadduma yafara salla har zuwa 4:00 yanakan dadduma sannan yatashi bayi yashiga wanka yayi yafito da pj dinajikinshi yawuce closet nashi shiryawa yayi cikin wani jallabiya fara kal da hula sai kamshi yake zubawa yafito ko kallon gadon baiyiba dan yasan ba salla takeba yabude kofa yafito tada mutanen gidan yayi suka wuce masallaci.
Chapter 44 · 0% Book details