← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 113

Sashe 108

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wani kalan tarwatsewa glass na kofan yayi ya watse saida mutanen reception din duka suka mike tsaye kowa ya firgita hannun Abee yahau jini dasauri Zuzu da ta bala’in firgita da yanda taga Abee dan kaman ciwonshi yatashi tace “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un, Ya Imran please take it easy, babu abinda yasami Lujain In sha Allah, muga hannunka, you are bleeding” dasauri su Baffa Hadi sukazo wajen ganin abinda Abee yayi yace “dan Allah kabi ahankali Imrana za’a ganta” daidai lokacin idanun Abee suka sauka kan Olusay tareda wata Yar Babban mace da zatai tsaran Zuzu da Anty Binta suna saukowa daga stairs da sauri sauri kaman suna neman abu sai waige waige suke shiru Abee yayi yakafe Olusay da idanu yana kokarin tuna inda ya sanshi kafin kanshi yahararomai Mandawari, jikinshi har rawa yake yayi ciki yana taka glasses din ko ajikinshi Zuzu tace “be careful Ya Imran” Olusay ko kadan baima lurada Abee ba kawai ganin Abee yayi yasha gabanshi, kwayan idanun Abee dayagani saida gabanshi yafadi hakan yasa yasauke kanshi kasa yama kasa magana, cikin wata kalan kakkausan murya Abee yace “where is your friend”? Faduwa sosai gaban Olusay yayi da kyar ya iya daddagewa yadago kanshi yakalli Abee yace “Mandawari shi muke nema muma, yau kwanan mu 3 a asibitin nan baida lafiya, yacemana dazu sai zauko yadan sha iska tunda yau za’a sallamemu we are just waiting for his doctor, nikuma na zauna da Mom dinshi adaki, he just sent me this text abinda yafito damu kenan a burkice neman shi, now that I see you nagane kan message nashi” yay maganan yana ciro wayanshi daga aljihun gaban riganshi yamikama Abee, karban wayan Abee yayi dasauri duk yanda yaso yakaranta messege din yakasa sabida yanda idanunshi ke ganin duhu duhu, baki baki, dasauri Zuzu takarbi wayan daga hannun Abee ganin yakasa karantawa tace “bari nakaranta maka Ya Imran” takalli wayan da karfi tace “Mom, Olusay, I’ve gotten abinda nakeso, my woman is with me now, baraku kara gani na ba har abada! Kugayama wannan tsohon daya aure mini girlfriend cewa I have my Lujai…….” Abee baima karasa jin karshen messege dinba yawani kamo gaban rigan Olusay yabalain shakeshi yace “where is my wife! Ina yakaimin matata!” Gabaki dayan asibitin saida ya amsa ihun Abee, Olusay ko numfashi yakasa sabida yanda Abee yarikeshi saima wani kakari dayafara kaman zai mutu dasauri daga Zuzu harsu Baffa da mahaifiyar Mandawari tace “sakeshi dan Allah, Innalillahi, yau wani kalan fitina Muhammad keso yasani, dan Allah bawan Allah kasakeshi” dasauri Baffa yarike hannun Abee yace “cikashi Imrana, dan Allah kacikashi abi abin nan ahankali, kar zuciya ta dibeka kayi kisan kai” Zuzu tace “Ya Imrana wlh zai mutu please kasakeshi” yanda jijiyoyin goshin Abee suka fito idanunshi sunyi jajir saika tsorata kaman ma baya hayyacinshi, wani kalan kukkullewa da jujjuyawa idanunshi suka farayi sai kawai jikinshi yafara wani kalan rawa kaman wanda ke having attack na farfadiya sai kawai yasakeshi yay baya zai fadi da gudu su Baffa suka tareshi suka kwantar dashi akasa , Zuzu tace “Innalillahi Ya Imran, Ya Imran can you hear me”? Tai maganan tana tattaba fuskanshi ganin yanda duka jikin Abee kewani kalan rawa kaman ansamai wani abu idanunshi sun kakkafe, wani kalan ihu Zuzu tayi. “I need a bed, nurses doctors, I am loosing him” daga su Olusay har su Baffa saida suka firgita da ganin abinda Abee keyi kaman zai mutu, ita kanta Zuzu kuka tafara sosai tana jijjiga shi mutane suka taru akansu yan reception din ana kallo kafin likitoci da nurses suzo aka daga Abee dahar lokacin jikinshi ke wani kalan rawa ya sassankare aka sashi akan gado aka wuce dashi su Baffa suka shiga kiran Baba, Zuzu kasa komi tayi tana kallon yanda Dr kebama Abee taimakon Gaggawa ana kokarin ceto rayuwanshi dan wani kalan critical cardiac arrest zuciyanshi yashiga tafito tana kiran number Ya Mustafa.

Before good 30min saiga Musty a asibitin tareda Ibro da Hamza da Abdul da Harun, ba’a sanarda Hajiya ba, shima Baba gashi a asibitin hankali tashe da manyan kaya dan daga kasuwa yazo, idan kaga Musty zaka dauka yazare ne, su Abdul tsayawa sukayi dasu Baba da Olusay shikuma Musty yawuce ER din da Abee keciki, security dake gaban dakin yana cemai you can’t enter the room wani kalan tureshi Musty yayi yashiga cikin dakin dasauri ya tsaya chak yana kallon yanda aka yaga gaban rigan Abee anasa defibrillator ana kokarin getting zuciyanshi to beat yana wani kalan ajiyan zuciya, ganin Abee yaki responding yasa yay wajen gadon zai tabashi aka hanashi Dr yace “you can die don’t touch him” cikin ihu Musty yana kallon fuskan Abee yace “Imran are you a coward? Zaka mutu ne batare daka nemi matarka with your unborn baby ba? Is this how you love Lujain?Imran wake up wake up my friend! Please wake uppp” daidai nan ana kara shocking zuciyanshi dasauri Doctor yace “he’s back” dawani kalan sauri Musty yatashi yana murmushi sosai yana kallon yanda Abee ke nishi ahankali that is very weak yagoge dan gajeren hawayen daya zubomai yajuya yafita daga dakin dasauri, Ibro da Hamza ne suka fara tareshi, murmushi yamusu yace “Alhamdulillah he’s breathing” yakarasa dasauri yamikama Baba hannu yana gaidashi, Baba yace “yaron da mahaifiyar Mandawarin sunce basusan inda yaje ba” cikin wani kalan zuciya Musty yace “koma ina yaje zasu fito dashi, suna ina”? Musty ya tambayi su Ibro, hakan yasa Musty yace “muje Baba suna office din kanwata” wucewa dukansu sukayi zuwa office din Zuzu, zaune sukaga mahaifiyar Mandawari sai goge hawayen takeyi da gyalen dake jikinta gwanin ban tausayi mijinta na tsaye kusada ita sai Olusay Abdul na interrogating nasu, anatse Mom din Mandawari tace “dan girman Allah nasan babu ta yanda zan baku hakuri kuhakura amman dan girman Allah kuyakuri kada kuyi arresting Olusay wlh baisan inda yake ba, Olusay shine yakirani dayake ni a Yola nake aure yasanar dani halin da Mandawari keciki akan yanda yakeson matan wani, gasunan ku tambayesu abinda yakawoni garin nan kenan gidan tuni nasashi a kasuwa anma saya wlh, ciwon dayakeyi yasa bamu tafi ba muka kawoshi asibiti amman da tafiya zamuyi sabida yama bar anguwan yakoma rayuwanshi nada ya manta da ita, ni bansan wannan wace kalan kaddara bane, Mandawari wannan wani fitina kake neman saka kanka ciki kadauke mata mai karamin ciki ni Rukayya ina zansa rayuwata naji dadi”? Kaga Mom din Mandawari zaka iya kuka kuma zakasan ba karya sukeba, magana Musty yama Abdul whispering hakan yasa Abdul yace “I need all papers na property shi, I need all his contacts, his friends, clubs da duk wasu wajejen dayafi zuwa, we will track him dukma inda yashiga zai fito, kukuma zamu saku on house arrest my team will be watching you for 24hrs agida, kutashi mutafi.EPISODE 1️⃣0️⃣1️⃣
Chapter 108 · 0% Book details