← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 113

Sashe 30

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Zaune yake gaban desktop nashi yana wani aiki dagashi sai singlet dawani dan gajeren wando wayanshi ne yay kara hakan yasa yadauka ganin Hajiya ne yasa yakai wayan kunnenshi yana mamakin meyafaru take kiranshi.
“Ka sameni adakina Imrana” ta katse wayan, ijiye wayan yayi yatashi tareda daukan jallabiya yasaka sannan yasa slippers yafito batare daya kalli kofan dakin Lujain dayake iyajin maganan Anty Binta aciki ba tana mata fira wucewa yayi yasauka kasa Hamza da Abdallah yagani a falo suna buga video game suna ganinshi duk suka natsu dakin Hajiya yawuce da sallama yabude kofan yashiga Hajiya na zaune bakin gadonta tana kallonshi hakan yasa yakarasa ciki yazauna kan lallausan carpet na tsakar dakin ahankali yace “gani Hajiya” karasa jan charbi datakeyi tayi ta ijiye sannan takalleshi tace “Imrana” dan dago kanshi yayi yakalleta yace “na’am Hajiya” ahankali tace “I promise not to meddle with affairs naka dana matarka but I think akwai somethings that I can overlook a matsayina na babba” Hajiya tadanyi shiru saikuma tace “banson damuwa yama Yar karaman yarinyar nan yawa Imran, kaiba kulata kake ba kannenka ma haka, Binta ne kawai ke kula da yarinyan nan agidan nan nikuma baran iyaba dan kafafuna ba barina zasuyi ina hawa saman nan ina saukowa kullum ba” Hajiya takarayin shiru sannan tace “inaso gobe kafin katafi aiki ka dauki yarinyar nan ka kaita makaranta mai kyau kasata, islamiyya kuma zaka sata wanda su Kausar ke zuwa asabar da lahadi, amman dai gobe yarinyar nan tafara makaranta kaga karatu nata wuce ta, tunda bawai wani abu take agidan ba banda zaman kadaici da kuka dan haka ka kaita kasata a makaranta mai kyau kaji ko Imrana” gyadama Hajiya kai yayi yace “to” Hajiya tabishi da kallo tace “tashi katafi to Allah bamu alkhairi” ahankali yace “Ameen” yatashi yafita daga dakin tareda maida mata da kofan yarufe, sama yakoma daidai lokacin Anty Binta tafito tareda Lujain din da hijab ke jikinta black dayawani kalan haskata, ganinshi yasa tasauke kanta akasa tashige bayan Anty Binta ahankali tana wasa da yatsunta, Anty Binta ma sauke kanta kasa tayi ganin yanda yake kallonsu da wannan idanun nashi dabaka jurewa, kallonsu yayi ba yabo ba fallasa yace “where to”? Ahankali Binta tace “dakina zamu ta kwana awajen Ya Imran wai bata iya kwana ita kada…….” wani mugun kallo yama Anty Binta yace “bacemin daga nan” dawani kalan sauri Anty Binta tawuce tayi hanyar dakinta, wani kalan kuka Lujain taji yazomata batare data kalleshi ba tajuya ahankali takoma cikin dakinta ko tsayawa kulle kofan ma batayiba da gudu tafada gado sai kuka, yadade awajen tsaye sannan yakarasa gaban dakin nata batare daya kallo ciki ba yasa hannu yajawo kofan yarufe yawuce dakinshi.EPISODE 2️⃣3️⃣

Wanka yashiga yafito ya shirya cikin wasu milk pajamas masu bala’in kyau yazauna kan gado, drawer jikin gadon yajawo yadauko wani babban english novel na UK mai suna the soulless love, wani akwati yabude na glasses yabude yaciro wani white glass yasaka sannan ya jingina da gadon tareda kashe wutan dakin yakunna wutan side lamp kadai ya jingina da gado tareda jan bargo ya lullube kafanshi yabude book din yafara karantawa yanajin kukanta sama sama dan daga nan dakinshi yakanji abinda ke faruwa acikin dakinta, almost 2hrs yayi yana karanta book din sannan ya maida yarufe ya ijiye saman drawer ya kwanta ahankali yanaso yay bacci amman baya iyawa kuma bayaso yanashan magungunan shi, dan lumshe idanu yayi yabudesu jin ko’ina tsit that means tayi bacci kenan, wayanshi yadauka ahankali yabude wani locked folder hotunane aciki na wata black beauty mata maidan jiki kaman yanayin girman Anty Binta, kaganta kamanninta da Kausar daya sak kaman tayi kakin Kausar ta tofar, lumshe idanunshi yayi ahankali yabudesu yasake daurawa akanta yatsanshi yakai kan fuskanta yana shafawa murya chan ciki yace “I’ve missed you Muna, why did you have to go and leave me alone at this stage of life” shiru yayi tareda lumshe idanunshi again yaja wayan yakaishi kirjinshi ya rungume tsamtsam.
Chapter 30 · 0% Book details