← Book details Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 113

Sashe 3

Sakon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Koda aka idar da Magrib gyara zama yayi dan yaji ta’aleem wanda dama shi haka yake sai bayan yay isha’i yake komawa gida, yana zaune inda yake wani yaro dan matashi haka dabazai wuce 22yrs ba yay kamadashi kaman yay kaki yatofar yazo kusadashi ahankali ya zauna tareda daura hannunshi kan nashi warmly yace “Abee” dagoda fuskanshi yayi yadaura akan fuskan yaron asanyaye yace “Ya school”? Murmushi yaron yamai yace “fine Abee yanzun nan nadawo nashigo masallaci dannai salla bari naje gida nai wanka naci abinci Abee I am hungry” gyadamai kai Abee yayi hakan yasa yatashi tareda wucewa yafita daga masallaci mahaifin nashi nabinshi da kallo ganin yanda gajiya ya nuna afuskanshi karara.

Sai bayan sallan isha’i sannan suka fito daga masallacin dashi da kannenshi biyun maza Hamza da Ibro sai Abdallah, magana yayi da Ibro dazai wuce gidanshi dan yanada mata gidanshi babu nisa da nasu shima a estate din yake zaune da matanshi da yaranshi Mata guda biyu hakan yasa shida Hamza da Abdallah dakemai hira sukai cikin gida ko kadan baida magana amsanshi baya wuce uhnnn u’u, suna shigowa falo akan lumtsetsen one sitter kujera yazauna dake facing wanda Hajiyanasu ke zaune akai 2 sitter, idanunta kyam akanshi tace “an dawo daga masallacin”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya” murmushi tayi tace “to Madallah kowa yaci abinci jeka dinning kaci naka kaima” dan yatsine fuska yayi tareda girgiza mata kai kaman wanda akace yay wani mugun abu ahankali yace “coffee kawai zansha Hajiya ankaimin daki”? Tabe baki tayi tace “ai tuni diyar nan taka mai rawan kai takaimaka daki” tashi yayi yace “to saida safen ku” tashi shima Abdallah yayi yace “Inna nima nagaji bacci zan gobe inada 6 nasafe, good night” binsu Hajiya tayi da kallo saikuma tai shiru murmushi Hamza dake kallon Hajiya yayi yazo kusada ita zama yayi yatasata agaba kuri yana kallo hararanshi tace “me kake kallona kaikuma”? Murmushi yamata yace “Hajiya kinga kiragema kanki wannan damuwan ko dazu saida Anty Binta tamiki fadan nan, kirage damuwan nan kan Yayanmu ba yaro bane he can take care of himself, kowa yasan Yaya baida yawan cin abinci idan yaji yunwa dakanshi zaisa akaimishi” baki tabude zatai magana daidai akai sallama tareda shigowa falon wani magidancin mutum ne wanda akalla zaiyi sa’an Abee washe baki tayi tace “surukina oyoyo Mustafa” murmushi yayi yataho da sauri har gabanta yaje ya tsugunna yace “ina yini Hajiya mun sameku lpy” murmushi tayi tace “Alhamdulillah dan nan yakuma zaman jidda? Ya fama da abincin larabawa mara magi sai uban kanunfari su masoro da sauransu”? Murmushi yayi yace “Alhamdulillah Hajiya” gaidashi Hamza yayi daidai nan su Anty Binta da kanneta duk suka fito gaidashi sukayi Ya amsa tashi Anty Binta tayi zata kawomai kayan kwalama yace “ina Imran Wife”? juyowa tayi takalleshi tace “yana dakinshi” tashi yayi dasauri harzai wuce Hajiya tace “Mustafa” dawowa yayi dasauri gabanta yace “na’am gani Hajiya” dan ijiyan zuciya tasauke baki tabude zatai magana saiga hawaye Hamza dake kusada ita yace “kinfara ko Hajiya”? Dan murmushi Mustafa yayi taredakai hannunshi yakama na Hajiya anatse yace “zan mishi magana Hajiya Dan Allah kidena kuka” bakin zaninta takama dasauri takai kan idanunta ta share tass sanan takalli Mustafa tace “Mustafa dole na koka Imrana shine yarona na farko wannan wani kalan kaddaran rayuwane, shine uban duka yaran nan nawa, ganida yara mata, yanzu nan nan Rahama uwar Aneesarh tadawo gida da yara biyu mata mijinta yarasu, idan wani abu yafaru shi za’a nema shine me tsaya musu, bama wanan ba at least wayannan su kannenshi uwa daya ta haifesu yaranshi daya haifa fa iyye? Yaran cikinshi fa Kausar da Abdallah? Yazaci su basu damu kullum suna ganin ubansu haka bane? Nasan yawahala arayuwan nan na………” “Hajiya!” Mustafa yakira Hajiya ahankali dayasa ta kalleshi murmushi yamata yace “in sha Allah zanyi magana dashi yau bari naje” tashi yayi ahankali yay sama sukuma duka yaran har Anty Binta sukazo suka zagaye mahaifiyar tasu kowa yay zugummm kunsan ance yara mata dabanne akwaisu da tausayi da jinkan mahaifiyarsu duk lallashinta suka cigaba da yi kowa na bata baki.
Chapter 3 · 0% Book details