Sashe 92
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
jikin ko wanne mai rai akwai zuciya ita take saƙa masa komai, to at this point ba zaka taɓa hana mutane abinda sukai niyyar faɗa ba, haka halin ɗan adam yake, baka da gadonsa yana da gadon maganarka, wani ma bai sanka ba bai san ya kake gudanar da rayuwarka baz bai san komai game da kai ba, ji kaiwa zai yi mutane suna magana ya ara ya yafa ya ɗora nashi akai, sbd kawai baya ƙaunarka ko yana baƙin ciki da abinda kake ko yadda yake gudanar da rayuwarka, wani kuma haka halinsa yake da haɗa ƙanzon kurege haka mutum yake, The world is big, the challenges in it are many, the people in it each have their own character" Latifa tayi shiru tana goge hawayen idanunta ta ce "Human nature is difficult to deal with, whether you do well or not, you will never stop a person from saying what he intends, kinga kenan babu yadda za mu yi, let them says lokacin su ne watarana za su daina, Mami banga aibun auren yaron daka raina ba, tunda bakai ka haife shi ba, ba kuma na nufin rainon yaran da ba kai ka haifa ba illa ne ko haramun ne, amma da Abbu ya bawa Abraham dama nasan dole zai musulunta" Cak Majeederh ta miƙe jiri na ɗaukarta. Washegari gari ta yiwa asibiti tsinke ta nufi wajan Dr Jamal ya gudata ya shaida mata kawai stress ne na gari ya bata magani. Bayan ta koma gida ta samu Abbu da Mami a parlour Mami ta ce "Me Dr ya ce? Akan zazzaɓin?" Majeederh ta ce "Wai stress ne" Mami ta ce "Oh Allah ya ƙara sauƙi" Abbu daman tuni ya zame hannunsa daga kan Majeederh ko gaisuwarta baya amsawa Family ta daina shiga kowa iyaye yake mata akan yana da aure gorin aure ake mata babu ji babu gani, ji take kamar ta mutu ta huta da sauri kuma take Asstagafirullah. Shiru tayi haka kurum tunanin Abraham ya faɗo mata gani take tafi kowa laifi, mai yasa idanunta ya rufe a lokacin ta kasa fahimtar da gaske ba ita ta haife shi ba? Me ya sa take sake masa har yake taɓa jikinta? Bayan tasan ya haramta a gareta, kenan ita ce wacce ta bashi da dama har ya ji ya fara sha'awarta. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, na shiga uku, Allah na tuba Ubangiji ka yafe mini, ban taɓa tunani hakan ba" Tun daga ranar take neman yafitar Ubangiji da yardar shi, tana jin kamar ta ci amanar addinin musulunci ne, Tunanin Alpha ya faɗo mata haka nan taji tana son saka shi cikin addu'a, shi ma ya riƙe hannunta amma gwara shi yayanta ne, Sai Ajlaal kuma bashi da kunya dama daga gani yafi ƙarfinta ko wanne a riƙe hannunta mistake ne bada gangan ba Abraham kai ta sakewa yanzu kuma tayi ladama kullum cikin neman yafiyar Ubangiji take tana hora kanta da raya dare tana sallah da azumi..... After a year da ta ƙara zuwa wajan Dr Jamal nan ma ya shaida mata lafiya take. Lokacin tana da shekaru 34 ta jingine komai a gefe, ta ƙaddara Abraham baya ƙasar ba labarinsa babu na Gang team. Lokacin data shiga shekaru 35 farkon shekarar sai ta ji kamar gilamar abu a cikinta ta ɗauka kawai irin abin nan ne da ake kira macijin ciki. Nan ma ta ƙara zuwa wajan Dr Jamal ya dubeta yana murmushi ya ce "Wai mai Malama Majeederh ke tunani ne? Gashi dai har scanning da X-ray duk nayi amma ba komai lafiya lou kike" Ta ɗan yatsuna fuska ta cikin liƙab ta ce "Kawai ban san yin ciwo" Ya jinjina kai ya ce "You're right, ni kam na tambayeki mana" Ta jinjina masa kai ya ce "Me muhimmancin saka liƙab da hijabi ga mace ne?" Ta kalle shi ta ɗauke kai ya ce "Wlh masu saka liƙab da hijabi na mugun birgeni, na taɓa ganin wata ina sonta amma tayi mini kwarjini" Sai a lokacin Majeederh ta ce "A duk sanda kaga mace ka ji sha'awa to ba kai ne mai laifi ba ita ce zata ɗauki zunubi, ita ta baka damar ganin abinda zai sanya ka ji sha'awarta, to me liƙab sirri ne, hijabi mai taraba ne ga ko wacce mace, abu uku zuwa huɗu yake fara jan hankalin namiji ga ƴa mace, na farko da namiji yaga mace idanunta yake fara kalla, a wannan kallon wani zai iya samun matsala, daga nan sai baki, daga nan sai wuya, abu na gana kuma murya, daga nan kuma bayan mace namiji yake gani, to idan zaka saka hijabi ka saka liƙab ka rufe jikinka babu wani ɗa namiji da zai sha'awarka balle ita macen ta ɗauki zunubi, liƙab da hijabi alama ne da tarbiyyr mutum, masu sakawa a fassara mu su da Allah, idan ka duba larabawa za kaga ko wacce da liƙab ɗinta, me ya sa ƴan izala suke sawa matansu suna sakawa? Ka yi tunanin su ɗin suna da kishi kuma sun san amfaninsa" Zai yi magana ta miƙe ta ce "Thank you Dr Jamal" kwanci tashi Majeederh ta ji cikinta ya fara girma tsoro ya kamata har aka ɗauki wata biyar Mami kallonta kawai take. Tana zaune kamar daga sama taga Uncle Isma'il da Uncle Bello "Saka hijabi hospital zamu" Bata ce komai ba ta miƙe suna zuwa asibiti a gabansu akai mata komai da komai Dr ya ce "Lafiya lou take, gaskiya ko da wata cutar mu dai bamu gani ba, ga photon komai na cikinta ai kuna gani" Uncle Bello ya sauke numfashi Uncle I ya ce "Mu je wani hospital ɗin" suna zuwa wani the same abinda aka faɗa musu shi ne suka sake ji, Uncle Isma'il ya saka akai mata medical check up nan ma the results is good dole suka dawo gida. Latifa ta dinga bawa Aliyu labarin halin da ake ciki akan Majeederh shiru kawai yake mata ta ce "Don Allah don Annabi ba danni ba ka duba girnan Allah dana mahaifiyarka Hajia ka amince da auran Malama Majeederh" A hankali yana miƙewa tsaye ya ce "Accepted" ta kurma ihu ta rungume shi. Lokacin data jewa Majeederh da maganar fata fata sukai ta ɗauke mata huta. Tafiya tayi tafiya har Majeederh tayi wata tara cikin shekarar data shiga na 35 haka kurum ta ji hankalinta yaƙi kwanciya, musamman da cikinta ya yi wani irin mahaukacin girma ƙafarta ya kumbura sosai ta buɗe tai wata ƙiba, hijabi ta saka ta ɗauki waya da jaka ta fito, Mami na zaune a a parlour tare da Raihana da Ruma da Aaliyah hadda Sahar data zo ta fito da ƙyar, tunda ta fito Mami ke kallonta ta ce "Wai kinga ganki kuwa? Anya likita ba ƙarya ya yi miki ba? Ji bi ciki kamar wacce akaiwa ajjiya? Majeederh ta ce "Mami ko jiya sai da Uncle Isma'il ya tisani a gaba wajan likita asibiti biyar muka je Mami ki tambaya ki ji" Ta ce "To Likitocin me suke cewa?" Kanta a ƙasa ta ce "Cewa suke lafiya ta lau, ba su ga komai ba" Ta jinjina kai ta ce "Allah ya kyauta" Ta ce "Zani wajan Dr Jamal na kirasa yanzu ya ce yana cikin asibiti kawai zuwa zan" Mami ta ce "To Allah ya kiyaye" Raihana dai kallon Majeederh take tun daga sama har ƙasa tana tuntsirewa da dariya, da ƙyar Majeederh ta ja ƙafarta zuwa waje ta nufi gidan Latifa ta sameta zaune ta ce "Plx ki yi dropping nawa hospital Latifa i can't drive myself" Ta ce "Ok, amma yau kin fi bani tsoro akan kullum wannan kamar wata mai cikin tagwaye?" Ta miƙe ta ɗauki key ta mayafi ta ce "Sweetheart ya fita zan masa yawa idan mun je" Mota suka shiga Latifa na driving Majeederh a gefe idanunta rufe ta cure waje guda sbd wani irin sanyi da aka tashi da shi yau ga wani masifaffan hazo na tashin hankali, tunda suke tafiya kuma bata ce komai ba rawar sanyi take Latifa ta ɗaga Glasses ɗin motar ta kashe komai na sanyi, amma duk da haka sanyin shiga jikin Majeederh yake tun kuma data shiga motar kanta ke sunkuye, Latifa na lura da damuwar da Majeederh ke ciki, kuma ta yau tafi da ko yaushe, ta ƙara sauri domin su yi su ƙarasa Aminu Kano hospital ɗin amma ina daidai by pass na first bank go-slow ya riƙe su...... _*(A page 1 za a ga ci-gaba daga nan)*_