← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 93

Sashe 67

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ƙirjinta dinga ɗagawa da gaske Little ɗinta Christa ne? Wani ya sauya masa addini ko daman can shi ne ba musulmi bane? Ta ce "Full name?" "Abraham Denial David" Ta runtse Idanunta tare da yin jikin kujera ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ta dinga maimaitawa hankali tashe. "I hate my father" Bata kula da maganar Father ɗin ba ta ce "Your mother where's?" Ya kwaɓe fuska yana ɗan ɗage mata gira bai ce komai ba. "Ka yarda kai Bad boy ne?" Ya jinjina kai ya ce "Yhhhh" "Kai Mahaukaci ne?" Nan ma ya ce "Eh" Ta dinga kallonsa cike da tausayawa kana ta miƙe tsaye shi ma ya miƙe Ta ce "Jeka gida" Ya marairaice mata ya ce "Jee zan bika, I will sleep with you today, Mami, I miss you so much" Ta kalle shi bata ce komai ba har ta nufi wajan motar ta, yana ta mamaki Maminsa tayi kuɗi ko me? Ganin zata shiga mota ya ce "Kawo key ɗin, I'll drop you" Frm head to toe ta kalle shi tana harɗe hannu a ƙirji ta ce "Wani ɗan kwanini da kai ina ka iya driving?" Kasancewar da Hausa tayi maganar sai bai fahimta ya kalleta da kasalallun idanunsa yana riƙe da murfin motar ya ce "Me?" Da Turanci ta ce "Idan zaka iya Hausa ka iya Little ban iya surutu da turanci dama dai larabci ne" ba tare daya fahimta ya ce "Ohk" A hankali ya zuba hannunsa a aljihu yana kame fuska ya ce "Let me drive you and drop you off at home" Ta ce "Wai kai yaushe kaga ɗan ƙaramin yaro yana driving? Kawai ka zubar dani lallai yaron nan" Ta faɗa cikin turanci sbd bata son wani surutun kuma. Wani irin Expression Abraham ke kallon Mamin tasa, a ransa yana ƙara maimaita kalmar yaro Ta ce "Kabari ka ƙara girma da wayo ka san halin kanka zuwa matakin aure" Calmly ya ce "Ohk" Yana tsaye harta fice daga cikin makamatar yamma lis, ya dinga kallon ƙofar kana ya cire hannunsa ɗaya daga aljihu ya dinga hargitse sumar shi. Gang team ɗin suka dinga dariya Taj yadda riƙe ciki ya ce "Gaskiya Mamin nan taka ta rainka da yawa, wai kai ne yaro?" John ya ce "Da kana kula babies wata rana ta ganka da wata a kwance manne kamar chewing gum ai ba zata ce maka yaro ba" Joshua ya ce "Wai kabari ka ƙara wayo sai ka yi driving nata, Goodness!" Abraham kallon su kawai yake. Taj ya ce "Amma seriously i like ur mother classes one Educated women, amma mene wannan a fuskarta? Naso ganinta" John ya ce "Amma dai ƴar rainin hankali ce wai kai ne yaro?" Gadan-gadan Abraham ya yi kan John tare da shaƙe masa wuya kamar wanda ke ƙoƙarin kashe shi "Am sorry Bad boy, sorry" Sai dai Numfashin John ya fara sama kana ya sake shi yana pointing nasa da hannu ya ce "Ko Grandpa ba zan ƙyalle ba akan Malumana Mamina, Jeena balle kai" Yana faɗin hakan ya shige motarsa ya mance kalmar yaro ya nufi gida wajan Grandpa cike da farin ciki yaga Mamainsa..... Wani irin kwara amai Aliyu yake kamar kayan cikinsa zai fita lokaci ɗaya ya fita hayyacinsa, Latifa ta dinga masa sannu ko kulata bai ba, da ƙyar ya wanke bakinsa a sink yana mai da numfashi ya fita parlourn daya zage ya gyara shi, zubewa ya yi saman kujera yana ƙaro gudun A.c Latifa ta ce "Wai lafiya? Mene ya saka amai?" Ya yi mata banza daga ƙarshe ya miƙe zai bar parlourn ta ce "Please Aliyu what's going on? Muje hospital" Ya kalleta kawai ta ce "Please Sweetheart" Ya girgiza kai ya ce "Kyankyaso cikin abincina Latifa? Kyankyaso dai na cikin toilet ki haɗe kika dafa abinci da shi, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya dafe kansa yama rasa me zai ce Ta ce "Kayi haƙuri ban san yaushe ya shiga ba" Da ƙarfi ya ce "Haƙuri haƙuri, I'm tired of your behavior, I feel sorry for you" Yana faɗin hakan ya fice daga gidan bakiɗaya he need to see a doctor ji yake kamar komai na cikinsa zai zube. Cikin dare Latifa na bacci ta ji an jawota ta yi saurin buɗe idanu tare da kunna switch haske ya bayyana, Suka haɗa idanu da Aliyu ta ce "Lafiya?" Da mamaki ya ce "Are you exlty questioning me?" Ta yi shiru ya ce "Ke ba matata ba ce?" Ta haɗe fuska ta ce "Yanzu mene?" Ya miƙe tare da jingina da frame ɗin gadon ya ce "Why are you answering my questions with a question?" Ta ce "Naga ai dare lokacin da ko wanne mai rai yake hutawa yana bacci gajiya, 1/24 idanun Mutum biyu" Ya jinjina kai ya ce "Ko?" Ta ce "Wallahi fa, mu kwanta mu yi bacci" A hankali ya ce "To" Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye yana jin mararsa kamar zata cire saboda azabar ciwo haka ya raya dare ido biyu tar sai asuba ya yi wanka tare da nufar masallaci a hankali suka haɗu da Abbu suka gaisa... Misalin 9:00 na safe Majeederh na bacci sbd jiya ba tayi baccin kirki ba tunanin yadda zata sauya Little kawai take ya dawo musulmi kamar ita da sauran jama'a, gefe guda kuma maganganun Uncle Bello da ya zo har gida ya yi mata ta tas akan taƙi tana yawo ta gaggauta fito da miji suka taro sukai mata tsaye a zuciya wanda ya hanata bacci sai asuba. tashin da Aaliyah ke mata a gigice ne ya sanya ta buɗe idanu Aaliyah ta ce "Anti Jeederh ki tashi" Ta kalli Aaliyah alamar "Lafiya?" A ruɗe hankali tashe ta ce "Wallahi Wani ne ya zo yana ta kwalla kira wai Mami, Malumana, hadda Jee" Majeederh tar ta buɗe idanu ta ce "Tun yaushe?" Ta ce "Tun Ɗazo fa, am sure Abbu bai ji ba da tuni ya fito" Jikin Majeederh duk rawa yake gashi kayan bacci ne jikinta ta ɗako hijabi ta saka ta ce "Shi da waye?" Ta ce "Shi kaɗai" Ta yi gaba bata saka Liƙab ba, gabaɗaya shap ɗin jikinta juyawa yake sbd ɗan saurin da take, Aaliyah ta rufa mata baya, tana zuwa compound idanunta ya sauka akan shi daga shi sai armless white colour sa gajeren wando gargasa duk kwance a fatar jikinsa gashin kansa a hargitse sai surar jikinsa da ƙarfafan maza ta bayyana, daga nan idanunta ya sauka akan wasu dalla dallan mahaukan matoci a ƙofar gate ɗin su daga waje, kafin ta yi magana taga ya kama katanga ya diro cikin gidan nasu tana ƙoƙarin juyawa tana girgiza masa kai amma ina tuni yayo kanta idanunsa cikin nata yanzu zuwa ya rungumeta sai gabaɗaya ta shige jikinsa duk girmanta hadda empty space daidai nan Abbu da Mami suka fito compound ɗin...
Chapter 67 · 0% Book details