Sashe 85
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
chest ɗinsa hannunsa ɗaya a waist ɗinta, idanunsa ya ware sosai cikin mutuwar jiki ya kasa cewa komai yadda take sauke numfashi haka shi ma yake ganin babu mai ƙauri a cikinsu ya sanya ya ƙara riƙeta sosai a jikinsa yana riƙe kansa da ƙoƙarin ganin ya dawo cikin nutsuwarsa. A hankali ya zame daga inda take yana matsawa ta yi baya zata kifa sbd ta gama tunanin tana jikinsa ta gama sakin jiki bakiɗaya, cikin sauri ta riƙe kanta da kyau tana jan breathing ɗinta da saukewa a hankali, har lokacin jikinta kuma bai gama daidaituwa ba rawa yake still. Idanunta ta buɗe da son nuna masa ko a jikinta ta ce "Ka fita daga cikin bedroom ɗina" Ta faɗa ba tare daya kalli direction ɗinsa ba, shi kuma ya zubawa yatsun ƙafarta idanu yana karantar yanayin da kike ciki, a hargitse ta ƙara cewa "Khalil get out of my room,i Said" gently ya ɗaga kai ya kalleta da rikitattun idanunsa wanda sukai laushi calmly ya ce "Bayan kasancewata Christa mene hujjarki?" Wani irin murmushi ta yi ta ce "Waya faɗa maka sbd kai ba musulmi bane ya sa naƙi amincewa? Da ace ina sonka da na ja ra'ayinka kan musuluncin ai" Ta gyara tsaiwa ta ce "Ba zan taɓa son ka, ba zan taɓa son yaron cikina ba, ba zan taɓa auren under age irinka ba, kayi mini ƙanƙantar da ba zan iya cewa kai mijina bane, infact i don't love you, wani gwanini da kai a gabana" Tunda ta fara maganar yake kallonta da wani irin yanayi wanda ba zaka iya tantance shi akan fuskarsa ba, ya nufeta da niyyar riƙe hannunta ta yi saurin matsawa ta ce "Ya zama last time da zaka ƙara gigin riƙe wani sashi na jikina, addina da naka akwai tazara mai yawan gaske" Rai ɓace kamar Mahaukaci! ya ce "Wanne irin addini ne wannan for God sake? Komai ba kyau" ta fizge hannunta, kau! Ta ɗauke shi da mari ta ce "Mahaukaci, addinina ya fi ƙarfin cin mutuncinka sai a yanka wuyan wanda duk zai aibata Musulunci" idanun Abraham sukai jawur ya ce "Shi addinin ya haramta auren macen data girmeka kenan? Shekaruna 18 mene abun yarinta a jikina? Me ya sa ki ka raina ni? Kawai saboda ni yaro ne, saboda kin girmeni da shekaru goma sha biyar?" "Kai yaro ne" "Zan wadataki da komai JEE, don kin rai ne ni a lokacin dana rasa iyayena bashi ke nuna ba zan iya zaman aure dake ba, ina soyayyar da kika nuna mini ina yaro? Okay fine, i have a solution! Your father doesn't like me kawai muyi auren Choci ko kuma wallahi mu haifi ƴa ƴan banza kuma shegu, ko kuma na wulaƙanta addinin Musuluncin naku" Yana faɗin hakan ya fice daga cikin bedroom ɗin. Zubewa tayi saman gado tana riƙe kanta wanda yake juyawa mata, tama rasa wanne irin tunani za ta yi da matakin da zata ɗauka, Abraham na neman zame mata ƙarfe ƙafa. A hankali ta lumshe idanunta da sauri ta buɗe jin tsigar jikinta na tashi har yanzu while bakinta na mata wani iri, Abraham ya bar mata wani irin moment da memory mai wahalar mantawa a zuciya, ya yi abinda babu wani namiji daya isa ya yi shi ya kafa tarihi a rayuwar Majeederh. Shuɗaɗɗan abinda ke damunta shekara da shekaru wanda tayi maganinsa ya dawo mata sabo fil. Gabaɗaya ta hargitse tare da yin luf saman gado ta rungume pillow addu'a take Allah ya kawo mata ko tsoho ne wanda ya girmi Abbu ta aura ku ta samu sauƙin maganganun jama'a ta kaucewa rashin kunyar ɗan cikin nata.. Uncle Isma'il ne zaune a parlourn baƙinsa ya dubi Pasto David kana ganinsa kaka cikakken Christa gaba da baya. Uncle Isma'il ya yi murmushi ya ce "Sir Please ga ruwa nan" Grandpa ya yi murmushi ya ce "My pleasure sir" Uncle Isma'il ya gyara zama cikin nutsuwa da harshen turanci ya ce "Kafin na ce komai zan su nasan waye kai, kuma na yi maka some of questions akan Abraham" Grandpa ya jinjina kai yana yaba nutsuwar Uncle Isma'il kafin ya ce "David sunana, shugaban church, business man with experience, sai wani secret aikina, kuma Abraham's Grandfather" Uncle Isma'il ya watsa hannu ya ce "That's good and i like it, amma Sir daman can Abraham Christa ne?" Kallo Uncle Isma'il kawai Grandpa ke yi kafin ya ce "Maybe, Abraham gaba da baya Christa ne kamar yadda ka ganni ɗin nan, muna ganin kima da matar tabar addininmu kamar yadda kuke ganin naku, muna ƙarfafa al'adunmu mun san muhimmancin hakan sosai, sai dai Abraham rayuwarsa ta samu bambanci da tamu kasancewar a nan Naija aka haife shi tun yana da 3yrs baya ƙaunar zama cikin gidan iyayensa, akwai wasu Neighbor ɗin su da suke Musulmi kullum yana gidan, yana da masifar wayo na ci da taurin kai, idan su kai alwala haka shi ma zai yi, ko sallah sukai haka shi ma zai. Bayan mahaifinsa ya fahimci hakan ya fara dukansa san bai gwadawa Abraham tausayi ba, ya tashi cikin mugunta yau zai dake shi ya fasa masa jiki haka zai wayi gari babu shi ya koma gidan Musulman nan, daga bisa ni ya kulle shi a wani ɗakin duhu babu abinci ya gana masa azaba sbd kawai ya daina zuwan gidan mutanen, kai har farcen ƙafa dana hannu Denial ya cire Abraham yana ɗan ƙaraminsa, shi yasa zuciyarsa ta ƙeƙa shi bashi da tsoro ko kaɗan, watarana kawai aka wayi gari babu shi neman duniya, shi kuma Denial ya yi tafiyarsa tunda daman ba a ƙasar yake ba, bai damu da ɗan ba ya ce watarana dole zai dawo gare shi idan har yana raye shi kuma daya haifi musulmi gwara ya kashe ɗan da hannunsa ya wuta" Wani irin tashin hankali ya bayyana akan fuskar Uncle Isma'il, da wani irin Expression yake bin Grandpa da kallo kafin ya ce "To mahaifiyarsa fa?" Ya ce "Ta mutu tun yana ƙarami ai, amma bai san da hakan bai kuma taɓa tambayar wani abu daya danganci mahaifiyarsa, Abraham bai taɓa zama da mace na minti ɗaya da sunan kulawa da bashi tarbiyya ba, mace ɗaya ta fara ƙoƙarin saita shi da ganin ya dawo hanya ita ce wacce yake kira da Mami, ur daughter Malamar nan" Uncle Isma'il ya ce "To ya akai ya dawo gare ku bayan ya ɓata? Tunda mun zauna da shi shekaru 2" Grandpa ya ƙara yin murmushi ya ce "His father, shi zuba private Investigators everywhere domin hankalinsa ya dawo kan shi, cikin sa a kuma aka same shi daga nan ya ɗauke shi zuwa wata ƙasar" Mamaki fal ya cika Uncle Isma'il sbd yasan cikin dare aka nemi Abraham aka rasa. "Waye mahaifin nasa? Yanzu yana ina? Me yasa kuma basa tare" Grandpa ya ce "You can ask him by yourself" Uncle Isma'il ya jinjina kansa kana ya yi murmushi ya ce "Yanzu ga abinda jikan naka yake ƙoƙarin rikituwa, kana ganin zai iya musulunta" Grandpa ya jima yana kallon Uncle Isma'il kafin ya ce "Har abada, ku gaggauta yiwa yarinyarku aure, idan kuma zaku bashi aurenta haka to, kai ko zaku bashi mahaifinsa ba zai taɓa yarda y auri musulma ba kuma ba wacce ta girme masa ai tayi tsofa da yawa gsky" Ran Uncle Isma'il ya fara ɓaci sosai kafin ya ce "Kai kake ganin tsofanta, bamu zamu gaggauta mata aure ba ku ne zaku jawa naku ɗan kunne akan ya fita harkar yarinyarmu ko kuma duk abinda ya same shi shikenan, ko hukuma ta rabamu da shi" Miƙewa Grandpa ya yi da sanda a hannu irin tsofaffin attajiran nan masu arziƙin gaske ba muna kuɗi ba ya ce "Hukuma? Waya faɗa maka Abraham na tsoran hukuma bayan shi ne hukumar kansa? Abraham babu wanda ya taɓa zama ya ce masa wannan abinda kake ba daidai bane ga wanda ya kamata ka yi, Abraham ko yini guda ya yi bai kai abinci bakinsa ba babu wanda zai ce masa ɗauki abinci kaci, irin wannan wanda bai san bambancin fari da baƙi be kake tunanin zai fahimci wani ya daina kula muku ƴa?" Grandpa ya girgiza kai kawai kafin ya ce "Sbd karamcinta ya sa nace kuyi nesa da ita daga idanunsa, Abraham ne yaro ne mai naci da taurin kai, tun yana ƙarami idan yana son abu kansa yake bugawa a ƙasa ba zau taɓa bari ba sai an bashi, Have a good day!" Yana faɗin haka ya fice daga cikin Parlourn ya nufi compound da sauri driver ya buɗe masa bayan mota ya shiga. Anti dake shirya Lunch ta kalli Uncle Isma'il ta ce "Ya akai kai jarumin namiji?" Ya nemi waje ya zauna tare da rufe idanu ya yi shiru. Ganin yanayinsa ya sa ta nemi ruwa mai sanyi a cup ta miƙa masa tana zama kusa da shi, bai musa ba ya amshi ruwa ya sha sosai yana sauke numfashi. Ganin bai ce komai ba itama Anti ta yi shiru da bakinta, har ya je sallar Asr ya dawo ya zauna cikin iyalansa idanunsa akan Jawaad ya kasa cewa komai, tunani fal ya sa yana sanya Jawaad matsayin Abraham taya zan iya sanwaltar da rayuwar ɗan shi ya bawa duniya ajjiyar shi? Ba dole ya kan gare ba. "Abba" Jawaad ya kira sunan Uncle Isma'il ganin kallon da yake masa kafin ya ce "Abba ruwa zan baka?" Ya girgiza kai kawai ya ce "Allah ya yi maka albarka Jawaad" Ya ce "Amin Abba" Sona ta ce "Jawaad kaɗai Abba?" Ya haɗe rai ya ce "Sona dake da Jawaad waye babba?" A hankali ta ce "Shi ne" Ya ce "To ya zama last day da zan ji bakin ki ya ce Jawaad ki bi bakin Majaufiarki na Fulanin Gombe ki ce Hamma, ko ki ce Brother da turanci ko Yaya da Hausa" A hankali ta ce "Am sorry Abba" Ya ce "Bashi haƙuri" Ta kalli Jawaad ta ce "Am sorry Yaya" Jawaad ya yi murmushi ya ce "No bad my dear" Bayan sun kammala cin abinci Uncle Isma'il ya zayyane wa Anti yadda sukai da Grandpa. Anti ta yi shiru zuciyarta fal tausayin rayuwar Abraham ta ce "No wonder sweetheart, ka duba Abraham sosai wallahi kallo ɗaya nayi