← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 93

Sashe 72

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da ya ji. Ya ɗago jiki a sanyaye sbd shi bai ba san yaushe ne ya shiga dukan mutumin ba, kallonta ya yi ya ce "Sorry Mami" A fusace ta ce "Sorry for yourself Khalil" Ta kalli mutumin ta ce "Don Allah ka yi haƙuri, yaro ne ina mai baka haƙuri" Ta juya ta kalli Abraham da ransa ya yi masifar ɓaci jin ta ce wai shi yaro ne? Ta ce "Say sorry to him, ka bashi haƙuri" Ya ɗauke kai tare da yin shiru. Tun da aka fara faɗan yana zaune cikin mota, sanye da wata dakakkiyar shadda gezner sai ɗaukan idanu take, komai na jikinsa da mugun kuɗi aka siye shi. Uncle Isma'il dake ɗaya side ɗin ya ce "Majeederh's disappointed me, na kasa yarda ita ce cikin tsakiyar mutanen nan" Abbu ya runtse idanunsa,wai ƴar cikinsa ce a nan wajan? Idanunsa ya sauka akan rigar Abraham dake jikinta, a hankali ya dinga binta da kallo, frm head to toe ganin jini kwance a bayanta ya sanya Abbu fara tari yana girgiza kai, Uncle Isma'il ya ce. "Take heart Abdul'aziz, Ka bi komai a sannu dan Allah, Please!" Shi kansa Uncle Isma'il idan ransa ya yi dubu to ya ɓaci, he can't believe cewa Majeederh yake gani, akan idanunsu ta saka hannu ta jawo hannun Abraham har zuwa cikin mota. Shi kowa Abbu tari ne ya sarƙe shi idanunsa ya yi jajur sosai, da ƙyar yana jan numfashi ya amshi bottle water ɗin da Uncle Isma'il ke bashi ya shiga ja yana komai ya fice masa a rai. Misalin 5 na yamma wata ƙatuwar mota, Mercedes-Benz EQS Black colour ta yi parking a compound na gidan Uncle Isma'il, Driver ya ce "We're here, Sir" Abraham dake bayan mota, ya shiga buɗe idanunsa da suke always sleeping sbd ƙwayoyin da yake sha, tar ya buɗe ganinsa akan harabar gidan, har ranshi ya ɗauka gidan zai ninka tunaninsa sai ya ga ko kwatan na Grandpa bai kama ba, balle kuma nasa gidan da bai fiya zana cikinsa ba. Sanye yake da Brown ɗin Armani suit, wacce ta kama jikinsa sosai dark black skin ɗin ta fito sai sheƙi take, hannunsa maƙale da agogon wrist na Patek Philippe, ga wani takalmi Half Cover Leather Shoe, komai na jikinsa designer ne. Fitowa ya yi daga cikin motar yana rufe idanu tare da zuba hannu a aljihu, a hankali yake bin komai na harabar gidan Uncle Isma'il, yana tsaye Uncle Isma'il ɗin ya fito cikin nagartacciyyar shigarsa tun daga nesa yake kallon Abraham har ya ƙarasu ya ce "Oh har ka iso?" Abraham ya nufi wajan Uncle I zai rungumesa alamar gaisuwa Uncle Isma'il ya miƙa masa hannu alamar musabaha bai musa ba ya amsa a hankali ya furta "Good day Sir" Uncle Isma'il ya ce "Come in, bismillah" Suka shiga har Parlourn baƙi. Uncle I ya gyara zama cikin turanci ya ce "Sunana Isma'il mahaifi ne ga Majeederh uwar riƙon ka, Ban yi wahalar gane ka ba, a wancan lokaci Little ake ce maka, sbd yadda kake baƙi ƙyakƙyawan mai ɗaukan hankali, ga saurin fushi da zafin zuciya,na lura har yanzu akwai ta kuma" Abraham dai kallon Uncle Isma'il yake bai ce komai ba. "Kana da shekaru 3 a duniya Majeederh ta tsince ka, ta raineka da hannunta, ta ciyar da kai da albashinta tana hana cikinta ta baka, bata faɗa amma akan ka tana yi kamar wacce akaiwa asiri da jininka, a haka har kayi shekaru biyar bi ma'ana kayi 2 years a wajanta, Tayi kuka sosai lokacin daka sake ɓata a hannunta sai gashi yanzu ka bayyana a bayyanar da ban ji daɗi ba, ka bayyana a wani addinin da ba namu ba" Uncle Isma'il ya gyara zama ya ce "Tambayoyi nake son yi maka, ina fatan zaka bani amsa?" Abraham ya jinjina kansa alamar yana jinsa. "What's your real name? And who are you? Meme aikinka? Matakin karatu? Ina familynka suke, Father, mother, e.t.c" Abraham ya sauke numfashi a ɓoye ya daɗe yana kallon Uncle Isma'il kafin a hankali ya ce "Abraham Daniel David, that's my name, Who is me?" Ya yi shiru for a second kana ya ce "Bani da uba, but i have a mother" Uncle Isma'il ya ce "Mene sunan mahaifiyar taka?" Abraham ya ɗauke shi fa duk ya gaji da tambayoyin nan, kawai don Uncle ɗinsa ne ya ce "Ohk, Jee Malumana, i can't I can't pronounce the name" Ya faɗa yana ɗan yatsuna fuska. Uncle Isma'il ya ce "Ok, Ina son faɗa maka abinda baka sani ba, Majeederh uwar riƙo ce ba uwar asali ba, ina nufin akwai aure tsakaninka da ita ba kamar yadda ba zaka taɓa auren wacce ta tsuguna ta haifeka ba, yadda kake zuwa kana rungumeta itama tana biye maka is prohibited in Islam. Ka saka a ranka duk sanda ka fara feelings na Majeederh to zaka iya aurenta, kasan Developing feelings towards opposite sex shike kawo So ka ji kana son mutum ko kasancewa da shi ko aurensa zama na dindin wani kuma sha'awa ce kawai take jan mutum ga abinda yake gani, kasan mata komai nasu mai kyau ne Zasu iya attacking opposite sex ɗin su, su ja ra'ayin namiji ya kwaɗaitu da su, Abraham I am telling you this as your Uncle, not as my guest" Tunda Uncle Isma'il ya fara maganar Abraham ke sauraren shi cike da fahimta, nan take ya ji komai na zuciyarsa na sauyawa. Uncle I ya ce "Think, U can marry Majeederh, but u can't marry your real mother, maybe a duk sanda kke rungumeta kana jin wani abu a ranka baka saki jikinka ka fahimci mene ba sbd tunanin Majeederh is ur mother amma yaudarar kanka kawai kake, itama Majeederh takai matakin da zata iya haifar ɗa kamar ka shi ya sa ta manta cewa abin da take kuskure ne, ina fatan ka fahimta za ku ka yi nesa da jikinta" Abraham was speckless da ƙyar ya jinjina kai tare da miƙewa suka fito waje anan ya ci karo da Sona kamar ta san shi ta ce "Uncle" Ya ɗan yi murmushi domin yana ana bashi girma ya ce "Sorry gashi bana yawo da kuɗi?" Sona ta ce "Ba komai, kai ne mijin Anti Jeederh?" Bai gane ba sbd da Hausa ta faɗa ya yi al'ƙawarin zai dawo mata da gift... Majeederh ta share hawayenta kwana biyu duk ta zama raguwa mai saurin kuka ta kalli Latifa ta ce "I'm tried Latifa na ga ji da rayuwar nan, tun ina son aure har ya fita akai na, yanzu wa nake da shi wa zai aureni da za a ce mini na kawo miji nan da 2weeks wlh bana da kowa" Katifa ta yi murmushi ta ce "Kina da wanda zai aureki mana Majeederh" Majeederh ta ce "Wallahi babu, ko zance ban taɓa yi ba" Latifa ta ce "C'mon ni na amince Mijina Aliyu ya aureki ko gobe ne...
Chapter 72 · 0% Book details