← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 93

Sashe 50

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*BOOK 1 PAGE 31*
MIJIN MALAMA
LITTAFIN KUÆŠI NE WANDA YAKE SO YA YI MAGANA 08119237616

Ina godiya bisa ta'aziyyar da akai mini ta babban rashin da na yi na wan mahaifina Alhaji Musa Zakari sheka ( Dagacin sheka) Na gode sosai Allah yabar zumunci marubuta da yawa wasu ma ban san su ba, sun nuna mini kara ƙwarai makaranta ina alfahari daku kune silar kai ni inda nake kune kuke goya mini baya ta hanyar siyan littafaina, ina fatan ba zaku gajiya ba🙏🏿🙏🏿32
Janta ya yi har tsakiyar main parlour yana zuwa ya saki hannunta yana binta da wani irin kallo kafin ya ce "Baki da hankali?" Ta buɗe idanu wanda sukai jajir ta ce "Me na yi?" Da idanu ya dubi shigar dake jikinta da kuma kallon fuskarta dake buɗe, itama tayi saurin kallon kanta tana ɗan marairaice fuska zuciyarta duk babu daɗi ta kasa cewa komai sbd yadda ƙirjinta ke ɗagawa ga zafin da idanunta suke mata duk ta sushe su. Ya gyara tsaiwa yana harɗe hannu a ƙirji shi ma nasa idanun sun yi ja sbd abubuwan da suke masa yawo a zuciya can ƙasa ya ce "Kuma da gaske fita zaki haka? Tsirara?"
“.... Tsirara!?” Ta faɗa da sauri cike da tsoro, Alpha ya haɗe fuska ya ce "Mene marabar dambe da faɗa?" Majeederh ta yi shiru domin ita sam tunaninta baya nan wajan, zuciyarta ta Kaɗaita da maganganun Abbu, lura da yanayinta ya sa Alpha bai ƙara magana ba ya bi ta gefenta ya shige ya zauna saman kujera yana harɗe ƙafafuwan. Majeederh ta shige part ɗinta not too long ta dawo sanye da rolling na vail a kanta, ta nemi waje saman kujera ta zauna, shiru ya biyo baya can ta ce "Ina yini?"
"Lafiya" Ya bata amsa a taƙaice. Majeederh ta yi ƙasa da kanta cikin sanyin murya ta ce "Ance an maka ƙarin girma congratulations" Alpha ya ce "Uhm" Yana ɗan kaɗa ƙafa kafin babu wasa idanunsa ya kira sunanta ya ce "Majeederh!" Ta yi shiru.
"Zabiya?" Ta kwaɓe fuska tunda bata son sunan ya ɗan shafa kai daman He just wants to tease her. Ta miƙe zata bar parlourn ya ce
"No, please" Ta zauna kamar zatai kuka ta ce "Tun ina ƙarama kake ce mini Zabiya Yaya, ni ban so idan kai ma da Aljanar nake maka kama to"
"Stop it Majeederh!" Ya furta a tsawa ce, domin ji ya yi kamar ta caka masa nashi a ƙahon zuciya, ya girgiza kai ya ce "Sorry"
Ta yi shiru speaking calmly ya ce "Sannu da dawowa ƙasa Nigeria, yanzu sai me?" Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta ce "Sai abin da Abbu ya ce" Alpha ya watsa hannu ya ce "Kina sane da problem ɗinki, komai zaki ki fara tuna aure first" Kunya ta kama Majeederh sai yanzu take dana sanin sanar masa da matsalarta, kuma yanzu da baya ai ba ɗaya bane tuni Ubangiji ya ye mata "Kina ji?" Ta ce "Aiki zan nema" Da wani irin sauri ya ce "Aiki?" Ta ɗaga kai ya ce "Shi ma Abbu ne?" Tayi shiru cike da tausayawa ya ce "Am sorry, zan masa magana ya fara bari kiyi aure" Wani irin abu ne mai ɗaci ya tsayawa Majeederh a maƙoshi ta runtse Idanunta tuni ta ji rauninta na son bayyana muryarta na rawa amma ta dake domin tayi al'ƙawarin ko hawan jini zai sameta, ko zuciyarta ce zata buga ta mutu nan take ta daina yin kuka ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Idan ya amince nayi auren wa zai aureni?" Alpha ya zura mata manyan idanunsa ya ce "Kamarya? kina nufin tsayin shekarun da ki kai a Egypt baki saurayi ba?" A hankali Majeederh ta girgiza kai ta ce "Even friend ban ba, shekaruna ashirin da takwas 28 ban taɓa yin saurayi ba idan ka ɗauke Imran shi ma ya guje ni ba tare da sanin dalili ba, baƙin jini ne dani Yaya na zama mujiya a idanun mazan duniya, hatta soyayyar ƙuruciya ban san ya take ba, ban san daɗin soyayya da wahalar cikinta ba, ko saurayin da zai zo ya yaudareni ban taɓa yi ba, balle wanda zai ji muradin aurena a zuciyarsa....,"
Ta yi shiru sbd numfashinta dake fisga kaɗan kaɗan kafin ta ce "Duk son da maza suke wa farar mace, duguwa mai kyan fuska nawa ya tashi a banza, mummunar mace wada ta fini farin jini, to idan ban yi aiki ba me zan Yaya? Shi ma Abbu fahimtar hakan ce ta sanya ya zaɓa mini wannan rayuwar kuma ina farin ciki da ita" Duk rashin imanin Alpha kasancewar shi Soja, wanda yaga masifu da yawa ya kashe rayuka da yawa amma a yanzu a gaban Majeederh sai dai zuciyarsa ta karye ya miƙe tsaye ya shiga kaiwa da komowa yana bugawa hannayensa waje guda kafin cikin sauri ya tsaya a gaban Majeederh ya ce "Majee ki minin wani al'ƙawari, do me a favor please" Ta kasa kallonsa ya kai hannu zai riƙe nata tayi saurin janye nata tana ɗan yi murmushi ta ce "Na maka"
Ya ja baya ganin bata son ya taɓa jikinta, numfashinsa na sauka ya ce "Kiyi accepting duk wani abu dana yanke miki muddin ba cutarwa bane, ki yarda ba zan cuceki ba Majee" Ta ce "Me zakai?" Ya bata amsa ya ce "Zaki ji, ki amince first" Ta jinjina kanta bai ƙara cewa komai ba, ya fice daga part ɗin ya shige part ɗin Abbu ita kuma ta nufi Kitchen ta fara haɗa dinner harta gama ta shige part ɗinta ba taga fitowar Alpha ba....
Chapter 50 · 0% Book details