Sashe 3
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*2.......*
A raunace tana ƙoƙarin danne jaririn ta rarrafa zata riƙe mahaifinta, Abbu ya yi saurin ja baya yana nunata da hannu idanunsa sun yi jawur ya ce "Ɗan shege a cikin gidans? A tsakiyar parlourna Majeederh? Kina ta rayuwa da cikin shege a jikinki kina ce mana ciwo ne, ashe ni mahaifinki ki ka yaudara! Ki ka munafurta?"
Ya dafe ƙirjinsa abinka da farin mutum nan da nan fuskarshi tayi jajir.
"Allah ya isa, Allah ya isa tsakanina dake...,"
"Na shiga uku,Abbu" cewar Majeederh wacce ko motsi bata iyawa ga jikinta gabaɗaya jinin haihuwa ya wanke shi. Aaliyyah kuka take sosai ta durƙoshe gaban Abbau ta ce.
"Don Allah Abbu kada ka tsinewa Anti Jeederh, kada ka aibata ta ka ɗauki ƙaddara wacce zata iya faɗawa kan kowa, idan ka tsine mata da wanne zata ji, Abbu ka...," Tsawa ya dakawa Aaliyyah ya ce "Aaliyyah da wanne suna ki ke amsawa a makaranta?"
Cikin tsoro ta ce "Aaliyyah Abdul'aziz Khan!" Abbu ya nuna Malama Majeederh da hannu ya ce "To daga rana mai kamar ta yau na haramtawa Majeederh amsa sunanta tare da nawa, na zareta daga cikin yarana, na haramta mata dukkan amfani da wani abu daya shafi sunana ni Abdul'aziz ko sunan familyna Khan" Tun da ya fara magana Malama Majeederh ta kafe mahaifinta da idanu zuciyarta ta fara daina aiki, Idanunta ya sauya tare da jirkicewa zufa ke yanko mata ta ko'ina jikinta ɓari yake, da sauri Ruma ta janye jaririn tare da sanya reza ta yanke masa cibiya,ganin Mabiya wato mahaifa bata faɗo ba ya sa ta nemi abu ta ƙulle jikin cinyar Majeederh.
Ruma ta saka hannu zata ɗauki jaririn domin ganin me Jeederh ta haifa Abbu ya ce "Ruma idan hannunki ya ƙara taɓa wannan shegen la'anannan yaron zan miki Allah ya isa kamar yadda na yiwa uwarsa"
"Kayi haƙuri Abbu" cewar Ruma. Mami duk abin da ake tana tsaye a gefe ta kasa cewa komai, idan ta kalli Malama Majeederh sai ta dawo da idanunta kan Jaririn.
Aaliyyah ta zube ta ce "Abbu me ya sa hakan? Zaka bawa Anti Jeederh tikiti shiga duniya da hannunka,bayan komai ta aikata kana da kamasho akai ba ita É—aya ba, mene ya sanya zaka hofintar da MACE MUTUM kamar Anti Jeederh,ita É—in haske ce, farin ciki ce ta ji da iya jarrabawar da take ciki ta rashin aure da kallon da jama'ar gari suke mata, kayi bincike Abbu, kada ka yi ladama a lokacin da bata da amfani"
Hannu ya sanya ya ɗauke Aaliyyah da mari yana huci ya ce "Ba zan taɓa ladama akan na rabu da wannan shaiɗaniyyar yarinyar ba, wacce ta cuceni ta cuci tarbiyyar dana bata, babu abin da zan iya cewa Majeederh sai Allah ya isa, ban yafe ba, ban yafe har na koma ga mahalaccina ba zan yafe mata ba" ya juya ya kalli sauran yaranshi da matarshi ya ce
"Ni Abdul'aziz Khan na yanke dukkan mu'amalar dake tsakanina da ƴata Majeederh Abdul'aziz Khan, ko da wasa ta ƙara ambaton sunana a matsayin ni ne mahaifinta wallahi sai na tsine mata, domin ni a wajena bata da maraba da gawa! Duniya ce ki je zaki gani"
Ba fatan gaskiya Majeederh take ba, ba kuma neman afuwar Abbu take ba, domin shi ɗin kaifi guda ne, amma tasan zai yi ladama a lokacin da bata da amfani kamar yadda Aaliyyah ta ce. Burin Jeederh shi ne Allah ya bayyana mata uban Jaririn nan, ko itama zata samu damar tsine masa, tayi masa Allah ya isa kamar yadda Mahaifin daya kawota duniya ya yi mata, ta yi masa mummunan fata a rayuwarshi ta yi masa addu'ar ɗaukewar dukkan wani jin daɗi walwala na tsayin rayuwa, damuwa da ƙunci su mamaye farin cikinsa, duhu ya maye gurbin hasken daya haska duniyarshi.
"Tashi ki ɗauki shegen danƙi ki bar mini gida" Aaliyyah kamar zata haukace ta ce "Mami ki sanya baki don Allah, Abbu ina Anti Jeederh zata nufa? shin tana da gidan da ya fi wannan ne?" Sai a lokacin Ruma ta ce "Aaliyyah kada ki sanya na fara zargin kema kin munafurci Abbu" Aaliyyah ta juya ta kalli Ruma ta ce "Me kike nufi?" Ruma ta ce "Ina nufin abin da kunnuwanki suka je yi miki, kin jima da sanin Majeederh nada cikin shege ki ka ɓoye"
Wani irin mugun kallo Aaliyyah ta watsawa Ruma ta ce "Ki ji tsoron Allah, kuma akwai ƙiyama, Mami do something"
"Something?" Mami repeated. "Don Allah" Aaliyyah ta sake furtawa Idanunta ya kumbura sosai, tausayin Malama Majeederh ya kamata tasan tunda Majeederh ta kasa cewa komai hakan na nufin abubuwa da yawa.
Mami ta kalli Majeederh ta ce "Ki duba Majeederh babu alamar dana sani a idanunta, ni kai na da nake uwarta ta yaudareni, sai yanzu nake mamakin abin da ya hanata aure ashe mu muke hauka ita ta jima da sanin kan É—a namiji shi ya sa babu littafin aure a cikin littafan da take wallafawa, kin ja mana abin faÉ—a"
Da sauri Abbu ya ce
"Ta jawa kanta dai, domin ban haɗa komai da ita ba, ta je hakƙin Addinin Musulunci ma kaɗai ya ishe ta, kafin na buɗe idanu ki fice daga gidan nan"
Zuciyarta tayi nauyi bata da hanyar kare kanta, fatan ta Ubangiji data yarda da shi,kuma take bautawa ya bayyana gaskiya ya wanketa a wajan Mahaifinta ko da ba zai amsheta matsayin Ƴa ba. Ta juya ta kalli Jaririn ko Jaririya domin bata san me ta haifa ba, amma tasan samuwar babyn na nufin wani abu! Only God knows.
Da hannu biyu ta ɗauki jaririn ta miƙe da ƙyar jiri na ɗaukarta, ga wani ciwo da cikinta ke mata har yanzu mahaifa bata faɗo ba. Kanta a ƙasa cikin wata murya mai tsananin rauni wacce ko fita ba tayi sosai sbd yadda numfashinta yake riƙewa ta ce.
"Me ya sa zaka mai dani Gawa bayan da rai a tare da gangan jikina? Bayan da numfashi a ƙirjina? Me ya sa zaka bawa duniya ni Abbu wallahi bana da laifi ban san samuwar cikin ba, ban san waye da wannan alhakin ba, ban san waye yake da sanya hannu wajan ruguza rayuwata ba, ban san waye ya zama silar rabani da Mahaifina, dangina, haɗi da farin cikina ba, zan tafi Abbu ina roƙan ka yafe mini a duk sanda gaskiya ta bayyana ko da ƙasa ta rufe mini Idanu, zan raini kyautar ALLAH, zan raini Raba Gardama shi ne hujjar da zata iya fiddani daga zargi, Allah ya haɗa fuskokinmu da alheri"
Aaliyyah ta cire hijabin jikinta ta sakawa Majeederh domin rigar barci ce kawai a jikinta, kuka take sosai tana faɗin. "Kiyi haƙuri Anti Jeederh bana da ikon taimakonki na kasa aikata komai kiyi...,"
Kuka ya ci ƙarfinta ta juya da gudu ta shige ɗaki ba zata iya ganin tafiyar yayarta ta ba.
Gently Malama Majeederh ta kalli Mami, ta juya ta kalli Ruma, da kuma Raihana wacce bata ce komai ba har yanzu. Ta jima tana kallon Mahaifinta kafin ta nufi hanyar barin parlourn jiri na ɗaukarta, tana jan ƙafa wacce ko takalmi babu ta buɗe gate tare da ficewa daga cikin gidan, kamar yadda take barin gidansu haka numfashinta ke barin ƙirjinta, ganinta na janye wa, jinta na raguwa, jaririn hannunta na neman ƙwacewa zuwa ƙasa.
Tafiya take jini na bin cinyoyinta, tafin ƙafarta na taka kan titi, tun tana jurewa har ƙafarta ta fara rawa jikinta ya saki ta ƙanƙame jaririn a ƙirjinta, slowly slowly ta fara ganin duhu a Idanunta tayi baya luuu! Zata faɗi a kayi saurin tare ta, ta faɗa jikin mutum ba numfashi a ƙirjinta.