← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 93

Sashe 82

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

love ɗina tana wani wajen ke kuma Allah ya ƙaddara zan zauna dake matsayin mata, ina baki ci sha, suttura ina saka miki kuɗi a bank duk wata, Maysoon ina jin zafi a zuciyata ina jin raɗaɗi ki taimaka mini na samu abinda nake so ta hanyar addu'a, yadda nake son ta ko mulkin nan dake tunkaro ni bana so haka, mene matsalarki?" Kuka take sosai ta ce "Are you going to insulate me? Kana faɗa mini ƙarara baka so na, dole akai maka, me ya sa ba zaka duba irin son da nake maka ba Yallaɓai? Ni bani da matsala kaso ko wacce kawai kulawarka nake nema lokacin ka nake buƙata, hatta wannan cikin na jikina Ubangiji ne kawai ya ƙaddara samuwar shi, yaushe rabon daka raɓeni?" A hankali ya ce "Sorry Maysoon" Kuka take ta ce "Please ko sau ɗaya ne" Ya ce "Am not in the mood, ki je" Za ta yi magana ya daka mata tsawa tare da hankaɗeta ta faɗi ƙasa saman ƙaton cikinta, wata ƙara ta saki tana runtse Idanunta Abuturab ko ta kanta bai bi ma ya nufi part ɗinsa, ƙarar data kuma yi ya ya jawo hankalin Mama da mai aikinta suka shigo parlourn a guje jinin dake malala a ƙasan Maysoon ya sanya Mama rikice Maysoon tuni ta fara kokawa da ranta, Mama ta fara kuka sbd tausayi cikin ikon Allah kuma suka fara jin kukan jariri da sauri Mama ta ɗaga Maysoon ta matsar da babyn Salati Maysoon take tana kiran sunan Abuturab tare da yin wata jijjiga idanunta na rufewa, Abuturab Mama ta shiga ƙwalawa kira yana ji ya yi shiru ganin numfashin Maysoon na tafiya baya dawowa yasa Mama fara kalmar shahada,idan ta kira sunan Maysoon sai ta faɗi kalmar shahada cak numfashinta ya tsaya jikinta ya saki idanunta ya yi sama rai ya yi halinsa Maysoon died.
Chapter 82 · 0% Book details