← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 93

Sashe 38

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MIJIN MALAMA
08119237616
Uhm get ready...... Yanzu zamu fara🥹26
Majeederh ta sake kallon Aliyu, she saw that he had changed from the way she knew him, duk da ba wani mugun sani ta yi masa ba, ta ɗauke kai ganin yadda ya kafeta da idanunsa da suka janye, a hankali ta juya idanunta cike da hawaye ganin Khan's family maza da mata yara da manya suna ɗaga mata hannu. Jikinta na ƙyarma da ɓari na rashin sabon tafiya ita ɗaya ta ƙarasa kujera ta zauna tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, wani rauni ya mamaye dukkan zuciyarta fargaba da tsoran abin da zata tarar a ƙasar daba tata ba ya wanzu a zuciyar Majeederh Abdul'aziz Khan. Ya za ta yi a garin da babu uwa ba uba? Garin da ba wa ba ƙani? Garin da babu idon sanin? Garin da babu mai kwaɓarta? Ya za ta yi idan abu ya faru da ita wa kuma zata tunkara? Rashin sanin wanda zai bata amsar tambayoyinta ya sanya ta ƙara tura kanta wani mahaukacin kuka na kwace mata ta yi saurin rufe bakinta. "Assalamu alaiki" Wata murya ta sauka cikin kunnenta a hankali ta goge hawayen idanunta tas ta ɗago kanta bayan ta gyara zaman liƙab ɗin fuskarta. A hankali ya daidaita tsaiwar shi ya ƙara cewa "Assalamu alaiki" Su take ta amsa amma harshenta ya yi mata nauyi ta ɗaga kanta suka haɗa idanu, yana tsaye ya rungume hannu ɗaya a ƙirjin fuskarsa maƙale da face mars, ya ƙara zuba mata idanu ganin yadda take ta sauke ajjiyar zuciya ya ce "Ki duba number seat ɗin ki" Sai a lokacin ta duba taga a number 35 take zaune number ta kuma 34 ne, ta langwaɓar da kai alamar ban haƙuri kana ta tashi a hankali ta zaune a number dake window. Ya nemi waje ya zauna yana danna airplane mode a wayarsa tare da ware jarida ya shiga dubawa, yadda Majeederh ke sauke numfashi a wahale ya sanya ya juya ya kalleta tare da cewa "Are you okay?" Ta jinjina kanta.
"Are you sure?" Ta ƙara jinjina kanta ya bita da kallo kafin ya ce "Okey"
Sanarwar aka fara kowa ya shirya jirgi zai ta shi, a hankali ta jawo ballet ta É—aura a jikinta.
Jirgi ya fara juyawa a ƙasa tsayin wasu daƙiƙo zuwa mintuna, Majeederh ta rufe Idanunta tare da ƙanƙame jikinta waje guda, lokacin da jirgin ya yi katantanwa zai tashi ji tayi kanta yana sarawa amai na shirin zubo mata. A taushashe ya ce
"Sorry" tana cikin wannan yanayin jirgin Emirates Airplane ya ɗaga da ɗarorun ɗalibai. Ta sauke ajjiyar zuciya ya ɗauki ruwa ya miƙa mata ta girgiza kai, har lokacin bai ji maganarta ba.
"Please bear with the interruptions, is this your first time on a plane?"
"Uhm" ta furta a yanayin da ba zai iya haddace muryarta ba.
"I see, sorry" Ya mai da hankali zuwa ga jaridar dake hannunsa deep down na zuciyarsa he was thinking ko dai bata jin magana, kurma ko bebiyya? Only God knows... Majeederh ta rufe Idanu yayinda da dukkan wani farin cikinta ta barshi a jihar Kano, ƙasar Nijeriya.
Aliyu ya zame idanunsa daga kan jirgin su Majeed wanda ya gama shigewa cikin gajimare, ji ya yi kamar da zuciyarsa ta tafi tare da nutsuwarsa ya sauke numfashi yana ƙoƙarin buɗe murfin motar shi ya ji an ce. "Hi"
Ya tsaya ta buÉ—e motar ya juya idanunsa ya sauka akan Alpha wanda baya jin zai iya mance yanayin daya gansu shi da Majeederh. Bai ce masa komai, Alpha ya gyara zama ce ya ce
"Alpha Bello khan my name, Captain, It is the highest rang in Tactical troops organization"

"Good" Aliyu haydar ya ce murya kuma can ƙasa, Alpha ya gyara tsaiwa ya ce "Sunanka Aliyu Sufyan Alhassan, ɗan Jarida a matakin farko na fara aiki, Kayi karatu a Al'ƙalam University, daga nan ka shige Cairo ka ɗora da karatu, a gida anso ka karanci ɓangaren politics Democracy, kai kuma ka ce Law ka ke so, mahaifinka Alhaji Sufyan Alhassan shi ne Commissioner for education, ku biyu iyayenku suka haifa, yayanka Almustapha shi ne Manager a Bua campaign, mahaifiyarku tana ji daku sosai shi ya sa bata jure dukkan ɓacin ranku, wannan dalilin ya sa bata takura ku akan maganar aure duk da akwai ƴan mata a familynku amma kuna jin kun girmi ajin su" Alpha ya yi murmushin gefen baki ya zuba hannu a aljihu ya ce.
"Idan har a kwana ɗaya zan iya sanin waye kai, to karantar zuciyarka ba zaiwa Alpha wahala ba, bayan kasanceweta soja ina aiki a hukamar fikira ta jiha ka kiyaye, kada ka fara abin da ba zaka iya ba, kada ka sanya zuciyarki cikin ramin da zata kasa fitowa, kada ka yi ƙullin da zaka saka cikin kejin kaza, kasan kaza uwar tune-tune ce, stay away from her, Ina nufin Majeederh Abdul'aziz Khan she's my sister"
Bar Aliyu Sufyan Alhassan dake jingine da jikin lafiyayyiyar motarshi ya ɗan miƙe hannunsa mai ɗauke carnoner ya ɗaga ya shafa kansa ya ce "Anzo wajan"
Ya dubi idanun Alpha dake kwance cikin nasa idanun kai tsaye ya gane me launin idanun yake nufi domin a yawan karatun English Novels da yake da literature daya karanta yasa fahimtar hakan bai masa wahala ba "Uhm"
Sai kuma ya ce "Me ya sa zaka nuna maitarka a fili? Kada ka manta nan fa ba filin yaƙi bane ko dajin sambisa Captain Alpha Bello khan, a tsare rayukan jama'a kafi ƙarfi, amma ba zaka nunawa Babba lauya fahimtar waye mutum ba, by the way, who are you talking about? Stay away name? Please open your heart ƙilan na fahimta sosai"

"Ka janye jiki daga gare ta, baku dace ba?" Cewar Alpha. Cike da rainin hankali irin na Lauyoyi Aliyu ya ce "Wai wa kake magana? stop bitting around the bush, just go to the point" Ya faÉ—a da muryar marasa lafiya.
"Na hango soyayyar Majeederh a cikin ƙwayar idanunka, shi ne nake maka gargaɗi kada ka sanya son abin da ba naka ba, ku dan muhimmancin rayuwarka ga wanda suka damu da kai" Alpha Said, ya na buɗe ido.
Aliyu ya ware idanunsa ya ce "Soyayya? Ni ɗin? Kuma wai da sister naka? Goodness, to an faɗa maka halin Lauyoyi da Sojoji ɗaya ne? A cikin gari muke fa ba wai barrack ba, balle ka ce zakai kishi akan kilaki, and ka yi kuskuren fahimta zatonka ya saɓa lissafinka"
Aliyu ya taka a hankali har gaban Captain Alpha ya ce "Yes Am in love, amma da ƙawar Hawwy ba ita kanta ba, bani da tabbaci da zuciyata, ban yi kuma al'ƙawari ba, domin shi kayana ne, zuciyata ba sansanin sojoji bane wanda a koda yaushe za a cillaku duk garin da aka so, zuciyata ba rigar sawa ba ce, balle a cire sanda aka so a kuma saka sanda aka so, Shi kuma so a makaho ne, baya ji baya gani baya kuma fahimta balle a gargaɗe shi, shi ne kamar dukiya ne wanda maganar mai shi kawai take ji, Ni bana soyayya domin So tsuntsune yana iya tashi daga kan wata ya koma kan wata, abun da zuciyar Barrister Aliyu Sufyan Alhassan ta sani shi ne _“KAUNA”_ irin ta har abada, ƙauna wacce zan iya mutuwa akan ta, ban san sacrifice a cikin Ƙauna ba, Cikakken namiji shi ne mai faɗa domin cimma nasara, nasara bata tabbata sai da tarin ƙalubale, ƙalubale a rayuwa shi ke nuna yarda da ƙaddara, yadda da ƙaddara ke nuna yarda da Allah Ubangiji maɗaukakin sarki" Ya yi shiru yana sauke numfashi kafin ya daki kafaɗar Captain Alpha ya ce "My friend, fight for your love"

"And you too Barrister Aliyu Sufyan Alhassan, kada ka manta ko a kasancewata Cousin zan iya yi maka illa"
Alpha ya sake faɗa a siga ta ya zama dole ka bar abinda zuciyarka ke so. Murmushi kawai Aliyu ya yi domin ƙoƙarin magana kawai yake yana faɗin hakan ya shiga mota, daidai nan Latifa ta ƙarasu ta ce

"Meke faruwa, kai da.....,"
Sauran maganar ta maƙale ganin Captain Alpha tsaye jikinsa sai ɓari yake shi kaɗai ta yi saurin nufar Aliyu ta ce "Yaushe ka zo?" “.... Not too long”
"Tafiya za ka yi?" Latifa ta sake tambaya ba tare daya kalleta ba ya ce
"In sha Allah" Ta ce "Ok then, Bye zan ki raka na ji jikin" Ya ware idanu akan Lafita ya ce "Ok love"
Ya yiwa motar key tare da yin reverse ya bar wajan da gudu.
Da sauri Alpha ya shiga ta sa motar har lokacin jikinsa ɓari yake yana jin Anti na kira amma ya yi banza. Gabaɗaya Khan's family suna can kan Aaliyyah dake ta faman kukan tafiyar Majeederh da ƙyar suka lallaɓata tare da shiga napep su kai gida.

New life
Airplane ɗin Emirates ya sauka a filin sauka da tashin jirgi na Cairo International Airport, kasancewar tsakanin Nigeria da Egypt tafiyar 5 hours 25 minutes ce. Ya sanya su ka yi saukar dare, weather garin ta bambanta data ƙasa Nigeria, Ruwan sama: 1 Laimar iska: 30 Iska 18km/h tun a step ɗin farko na jirgin ƙofofin fatar jikinta suka buɗe suka shiga amsar saƙon sauyin yanayin da suka samu. A hankali Majeederh ta ɗaga kanta sama tana ganin sararin samaniya sama ɗaya ce kaf duniya, amma ta bambanta da saman data gani a taushashe ta ce “Majeederh a Misira”

Misira/ Egypt
Kasar Misra,ko Masar tana kudu maso gabashin Afrika, kuma tana kudu maso yammacin Asiya, ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewarta a kan mararraba ta kusa da nahiyar Turai. Sannan kuma tana matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar Bahar maliya. Harshen ƙasar Larabci ne, Shugaban ƙasar Abdul-Fatah El-sisi ya wadata ƙasar shi da komai, kuɗin ƙasar kuma Fam ne, ita ce ƙasar da tafi ko wacce yawan Al'umma a cikin ƙasashen Larabawa, ga babban birninta Al'ƙahira har ila yau gata a ƙarshen kogin Nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya.
Chapter 38 · 0% Book details