← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 93

Sashe 55

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa bata amsa tayi saboda tashin hankali, ganin kowa ya yi shiru ya sa ta ce "Finally, ni ma na zama matar aure Allah na gode maka bisa wannan tarin Ni'imar da kayi mini, na ƙara yadda wani jinkirin alheri ni Anti, gashi yanzu Ubangiji ya bani nagartaccen miji" Majeederh ta yi murmushi tana goge hawayen farin ciki, duk wani zafi da ƙunci ya kau a ranta, tabon dake cinta a zuciya ya hanata sukuni gabaɗaya ta neme shi ta rasa. Aurenta da Yayanta Alpha ya zama abu na farko wanda ba zata taɓa iya mantawa fashi ba. Anti ta juya ta kalli Aaliyyah da Sona ta ce "We need privacy, ku je waje yanzu zan fito" Aaliyyah ta yi waje, Sona ma ta bi bayanta. Anti ta kalli Majeederh tana murmushi wanda bai kai zuciya ba ta ce "To Amarya" Kunyar Anti ta kamata, ta ɗan yi ƙasa da kanta a hankali Anti kamar kazar da ƙwai ya fashewa ta ce "Ki je ki yi sallah, wanka,cin abinci we need to talk ok" Majeederh ta miƙe tsaye da sauri ta dafe gefen kanta "Sorry kan ne dai?" Anti ta tambaya tana riƙe kan nata, jijiyoyin kan duk sun fito sai har bawa suke idanunta jajir, ta ƙara yin murmushin ƙarfin hali ta ce "Abbu ma zai farin ciki ko Anti? Zai yi farin ciki yaga aurena, ni kuma zan aurar da Aaliyyerh" Gabaɗaya Anti tunanin dake sarrafa ƙwaƙwalwarta ne ya tsaya da aiki ta tsaya ta dinga kallon Majeederh da ƙyar ta iya cewa "Ki je ina jiranki Majeederh" Ta nufi bathroom da ƙyar ta yi wanka tare da sallolin dake kanta, Anti ta kawo mata wata atamfa Valisco milk da yafin blue a jiki, ɗinkin duguwar riga Ashap. Majeederh ta dinga kallon kayan domin bata saba saka irin su ba, tina cewa ko wacce amarya irin kayan da take sakawa kenan sai bata ce komai ba, ta shirya tsaf tayi wani irin masifaffen kyau, kamar irin Fulanin Usul ɗin nan ko na Daji ko kuma irin Half-caste ɗin nan jinsan larabawa da yankin Niger na Agadas ko Sudawa. Idanunta zuru-zuru tayi muguwar rama kamar kuɗin guzuri, fuskarta kamar tafin hannu. "Anti na kira number Yaya a kashe fa? Zan yi masa godiya da aurena da ya yi" Anti ta kasa bata amsa ta juya da sauri tare da ficewa daga bathroom ɗin ta nufi part ɗin Uncle Isma'il lokacin yana zaune saman kujera yana waya, tana zuwa ta rushewa Uncle Isma'il da kuka tsabar firgici ya saki wayar hannun sa tare da miƙewa jikinsa na rawa ya ce "Subuhanallah! Ƴar Aljanna ke dawa?" Anti ta dinga kuka jikinta har rawa yake kai kace Uncle Isma'il ne ya rasu, ko kuma an aiko mata da mutuwar mahaifinta daga Gombe. Cikin kuka ta ce "Mun shiga Uku Yallaɓai, mun shiga uku Abban Jawaad" Uncle Isma'il ya ce "Ba mu shiga uku ba da izinin Allah, Ubangiji na tare damu" Ya saka hannu ya ɗagota yana riƙe fuskarta ya ce "Majeederh ko?" Ta kasa magana sai kuka Uncle Isma'il ya rasa yadda zai rarrashi matar tasa ya kamo ya rungume ya ce "Haba bansan fulani da raguwar zuciya ba, haba jinin Gwambawa haba ƴar Bafullatanar matata uwar ƴaƴana kukanki azaba ne a zuciyata" Ya yi murmushi cikin dauriya ya ce "Akanki bulala nawa na shanye? Gwambawa sun gana mini azaba a haka na shanye shaɗin na aureki, mene ya kawo haka? Kinga juriya ce da yadda da Allah da ƙarfin addu'a, ki zama jaruma kamar yadda na zama jarumi a soyayyarki ki yi haƙuri don Allah uwar Jawaad da Sona, garkuwar Du'a haba matar Isma'il amarya kuma uwar gida, idan baki jure ba ina zaki samu ƙarfin qiwwar rarrashin Majeederh" Ya goge hawayen da suke bin idanunta tana shassheƙa ta ce "Na rasa yadda zan yi babu kalaman ban haƙuri ga Majeederh, wannan yaron ya cucemu he disappointed us" Uncle Isma'il ya ce "Da wannan salon yaudarar taki da kika sace zuciyar Isma'ila da shi zaki rarrasheta, komai na rayuwa yin Allah ne ba namu ba, bama da ikon hana komai ko faruwar shi take heart please" Miƙewa tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta nufi part ɗin da Majeederh take ciki. A zaune ta sameta idanunta rufe ƙirjinta na ɗagawa kamar wacce asthma ɗin ta take shirin tashi, kafin ta ƙarasa ta nufi wajan freezer ruwa ta ɗauka mai sanyi ta tsiyaya a kofi ta ce "Drink" "Azumi nake" Majeederh ta bata amsa, Anti ta ce "Ai kowa zaki karya azumin me?" Ta yi ƙasa da kai ta ce "Nuna godiya ga Ubangiji" cewarta. Anti ta nemi waje ta zauna tana bin bedroom ɗin da kallo a hankali ta ce "Hawwa'u!" "Na'am Anti" Ta amsa gabanta na faɗuwa haka kurum. Anti ta ce "Mece ƙaddara?" Da mamaki Majeederh ta kalli Anti sai kuma ta ce "Jarrabawa ce da Ubangiji yake jarabtar bawansa domin gwada imaninsa, shi ya sa aka ce yarda da ƙaddara shi ne cikin imanin ko wanne musulmi" Anti ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Allahamdulillah" Wajan ya yi shiru can dai Anti ta ƙara kiran sunan Majeederh a wannan karam kasa amsawa tayi ta ce "Hawwa'u mace da ciki da ciki ta mutu, miji ya rasu ya bar matarsa da yaransa, uwa ta rasu tabar miji da yaranta, iyaye sun rasu sun bar yara, Gabaɗaya hakan tsarin waye? TSARIN ALLAH, Ubangiji ke da ikon ƙaddara kuma shi ne wanda masarrafar rayuwarmu ke hannunsa, ya haliccemu domin bauta masa dayin biyya da iyaye duk mutumin da ya cika haka bazai taɓa tuzarta ba, ƙaddara shuɗaɗɗiyya ce, ba za'a taɓa hana zuciya ƙuntata ba, domin baka da ikon yin haka amma akwai mataki na kare kai, Majeederh ki yarda Allah ke tsara duk abinda zai faru, Mu so wanda ya ke son mu shi ne soyayya, mu so Mutum ya so me shi ne dacewa a soyayya, mun so abu babu damuwa maybe abin ya dace aso shi saboda nagartar da yake da ita, rasa abinda zuciyar mu ke so, bashi yake nufin rasa rayuwarmu ba, watakila rabonmu na ta wani wajan yana jiranmu, idan soyayya na gudunm ƙauna ta har abada tana can wata duniya idanu rufe tana nemanmu, faɗuwa a soyayya nuni na cewa hakan ba alheri bane a ranmu, ba laifi bane don munyi kuka idan an yaudaremu, babbar asara ce ka komawa wanda ya guje ka ko ya yaudareka, hakan na alƙinta mana mun rasa wani abu a baya inma mu rayuwa inma mutum mu rayu da sanin Ubangiji ke zana komai cikin tsaftaccen allon lauhil mahfuz, yi kuka Majeederh akan farin ciki kada ki yi kuka akan baƙin ciki...." Anti ta yi shiru kana a hankali cikin rauni tausayi da fargaba ta ce "Ba a ɗaura aurenki da Alpha ba, domin ya gudu bisa ra'ayinsa na ƙin auren wanda Ubangiji ne kaɗai ya san dalili" Da wani irin Expression Majeederh take kallon Anti, kallon da sai da hantar cikinta ta motsa, gabanta ta faɗi domin bata taɓa ganin rikiɗewar idanu lokaci ɗaya irin na Majeederh ba, ƙarar tsayawar abu a wuyan Majeederh yasa Anti taɓata ta ce "Majeederh ki yi haƙuri ki yi haƙuri, ban san yaushe ne hakan ta faru ba, ban san mene ya sauyawa Alpha ra'ayi ba, amma nasan yana son ki ina ganin hakan acikin idanunsa, rabonki yana wani tsagin rabo mai girma rabon da zai bawa kowa mamaki,ki yi haƙuri da rayuwa Majeederh" Maimakon kuka sai taga Majeederh ta saki Murmushi, murmushi mai kyau wanda bata taɓa ganin irinsa a fuskarta ba, irin wanda dashi gwara kayi kuka irin sa yafi kuka ciwo a zuciya hakan na nufin Mutum yana cikin halin da kuka ya yi masa kaɗan. Ta miƙe tsaye ta ce "Zani gida" "Majeederh are you okay?" Ta ce "In sha Allah" A hankali ta ce "Kiyi haƙuri ki miƙa lamuranki ga Ubangiji please" Ta ƙara yin murmushi ta ce "Ba komai, bani hijabi da liƙab ɗin Sona" Ba zata iya tsayar da ita ba, akan Idanunta ta saka hijabin da liƙab ɗin tare da amsar kuɗin napep wajan Anti ganin haka yasa Anti ƙwalawa Aaliyyah kira ta ce "Maza jeki ku tafi akwai matsala" Jefa ƙafafuwanta kawai take without knowing ina take takawa, da gudu kuma Aaliyyah ta cimmata ta tsare mai napep ta ce masa Lodge Road..... Misalin 8 na dare wani irin ciwon kai ya kama Majeederh har bata iya gani sosai ga jiri da ƙyar ta miƙe ta nufi part ɗin Abbu da yake kiranta tana zuwa ta zube a ƙasa wajan ƙafafuwansa ta kasa cewa komai. Ya dubeta ya ce "Kin kyauta" Da sauri ta kalle shi tana son tambayar mai tayi sai kuma tayi sbd nauyin da harshenta ya yi mata wanda ya tilasta mata kame bakin. Ya gyara zama da kyau ya ce "Kin tuzartani cikin dangi Majeederh,kin kunyatani kin cin mutuncin shekaruna, akan namiji? Yanzu me gari ya waya? Kin barwa kanki abin gori kin bar mini nima koma babu komai tarihi zai kafo akan Alpha ya gudu saboda baya ƙaunar aurenki" Ya girgiza kai ya ce "Majeederh kin yarda ni mahaifin ne?" Da sauri ta ce "Wallahi Abbu ban taɓa kokwanto hakan ba" Ya miƙe tsaye tare da ɗakko Alkur'ani mai girma daman yana da alwala ya ɗora hannunsa akan Alqur'ani izzu sittin ya ce "Wallahi wallahi Allah Majeederh ni ne ubanki mahaifinki, wanda jinina ke yawo a jijiyoyinki, na rantse da Allah ni ne mahaifinki ni Alhaji Abdul'aziz Khan" Ta dinga girgiza kai babu hawaye ko ɗaya a Idanunta ta ce "Don Allah Abbu ka bari" Ya kalleta ya ce "Amma ni ina tunanin kamar an sauya mini ɗiyata, kamar ke ɗin ba Majeederh ta bace"A rikice ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, Ya Allah wallahi bana gane komai ko fahimta" Ya zauna ya ce "Kin kasa bani abinda nake so nake buri Majeederh, na rasa yadda zan yi dake kin kasa rufa mini asiri, Hawwa'u aure fa ba dole bane tunda zaki iya riƙe kanki, kuma ni na san jinkiri ne kawai kika mijinki nan zuwa ki taimaka mini, ni mahaifinki ne" Majeederh ta ce "Ka yafe mini, ba sake cewa ina son kowa ba shi na don Yayana ne ai kaga ma bai aurenin ba shikenan
Chapter 55 · 0% Book details