Sashe 63
Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MIJIN MALAMA it's a paid book, pay before you read...... For me information via WhatsApp number 08119237616Ya gara zama ya ce "Allah ya na gani na ga ji da ganinki a cikin gidan nan ba aure, gorin dangi ya Isheni ba zan jure ba, ba kuma zan lamunta ba, shekaru 31 kina haɗa kafaɗu da mahaifiyarki? Gabaɗaya ke ɗaya ya rage a dangi ƙannen bayanki suna gidan mijinki" Da tashin hankali kawai take bin Abbu da idanu ta kasa koda jan numfashi domin a ƙirji komai ya tsaya mata, zufa na yanko mata all over herself, kullum tana jin ciwo a zuciyarta, bata da burin daya shige tayi aure amma kuma bata da ikon aurar da kanta ai? Ciwon dake damunta kullum ƙara yawa yake This pain was different, it was draining and excruciating painful, and soon it stopped abruptly. Abbu ya ce "Kina ji na?" Ta ɗaga masa kai a hankali ya ce "Good, Tun kafin na nuna mini The other side of me ki shiga hankalinki, ko mazan auren ki ka rasa? Kawai kin tsaya zaɓe da ruwan Idanu" Majeederh dai bata ce komai ba, domin sama sama take jin maganganun mahaifin nata rai ɓace ya ce "Get out, ki fari na sake miki maganar fito da mijin aure" A sanyaye ta ce "Kayi haƙuri Abbu" Zata miƙe ya ce "Sit down" Ya kalleta sosai sosai cikin magana ta fahimta tsakanin uba da ƴar shi ya ce "Mene matsalarki?" Ta yi ƙasa da kanta, tsayin shekaru 31 bai taɓa zaunar da ita ya ce meke damunta ba, sai yanzu da komai ya ƙare mata “When all is gone†to yanzu ta ce me? Bayan faɗar bata da wani amfani, it's too late to cry. Cikin tsawa Abbu ya ce "Ina magana kina ji na?" Ta girgiza kai ta ce "Lokaci ne bai ba Abbu, ka yi haƙuri" Abbu ya ce "Eclty, ni ne kike cewa lokaci ne bai yi ba? To buɗe kunnenki da kyau ki ji" Ya gyara zama ya ce "Wallahi wallahi ki fita daga idanuna, dana matsa miki a shekarun baya ki yi karatu ai saboda rufin asiri mu ne nothing more, yanzu i have what i want, kin rufa mini asiri yanzu kema ki rufawa kanki kiyi aure hankalina zai fi kwanciya, Hawwa'u am telling you as your father lokacin da zan ƙara miki maganar aure zaki sha mamakina wallahi Allah" Yana faɗin hakan ya miƙe tare da shigewa bedroom ɗinsa ya barta zaune kamar gunki. "Majeederh!" Zuciyarta ta kirata, ta yi saurin ware idanunta tana dafe ƙirjinta. Zuciyar tata ta ƙare cewa "Nutsu Majeederh, think about that, wai kina da saurayin ne ma?" Waya taɓa cewa yana son ki? Balle ya yi tunanin sanyaki a gidansa matsayin matar aure ta sunna?" A razane Majeederh ta girgiza kanta, cike da tashin hankali tana sauraren abinda zuciyarta ke faɗa mata, ta yi shiru jin ta ce "To kenan yanzu ya zaki? Shelar kan ki za ki yi ko yaya? Kinga dai bakya son ɓacin ran Abbu ya zame miki dole neman mijin aure.....," Da sauri ɗaya zuciyar ta buge ɗayar ta ce "Ji banza, ke dai ƙwaƙwalwarki bata aiki kamar mai shan miyar kuka, banda awon igiya ce ke kamar Malama Majeederh ce zata yi shelar kanta? Kuma shi Abbun bai san ƙaddara bane? Waye ya jefata wannan halin tun farko? Ba son zuciyarta bane da neman abin duniya? Do what is right not what's easy, yadda ya dama zaka zai shanye abinsa, tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa akan doka! Dole abu ya yi haƙuri domin shi ne silar faruwar komai shi ne ya haddasa mata jinkirin auren, by the way Ubangiji hakan jarabta mu, kuma shi aure lokaci ko ita Majeederh ce zata aurar da kanta? A wannan zamanin bafa ita kaɗai ce take da wannan matsalar ta rashin aure ba, jarrabawa ce! Kuma zurfin cikin ki ya yi yawa Majeederh You have to do something, do something Majeederh! Biyyar da kikewa Abbu is too much....," Kamar zautacciyya haka Majeederh ke sauraren shirar zuciyoyin nata guda biyu, da mai faɗin gaskiya da mai kushewa tana ɗora ta a tubalin da zai kai ta halaka. Kyakkyawar zuciyar ta ce "Oh! Kina nufin ta wulaƙanta mahaifinta kenan? Daman haka ya dace ɗan halak ya yi wa iyayensa? Ba Abbu da yake mahaifinta ba, ko Mami idan ta yi magana dole Majeederh ta yi mata biyayya, mai haƙuri shi ke da riba a wannan rayuwar, na tabbar Ubangiji ba zai taɓa barin Malama Majeederh ta haka ba, dole akwai wani rabo da tanada mata albarkacin biyayyar da takewa Mahaifinta, rabonta yana ta wani ɓangaren" Majeederh ta yi zuru domin tafi gasgata maganar kyakkyawar zuciyar, muguwar zuciyarta ta ce "Hoo ƙaaasa! Yau ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa, waya hanata auren tun fil azal, lokacin yana wagairawun bai ajjiya ko sisi ba, a matsayinsa na uba wanda zai fita ya nema ya ciyar da iyalansa amma ya jingina ƴar cikinsa mai tsafta da kamala matsayin jarinsa, ya sadaukarwa duniya ita idanunsa ya rufe, kuɗi kawai yake so arziƙi yake nema ta ko'ina sbd yanzu ta tara masa ya shiga jerin masu kuɗin Kano shi ne zai ce ta fito da mijin auren? Ya ja mata ƙaddara sai su amsheta da hannu bibbiyu, rayuwar Majeederh ta shiga cikin lack of parents careless, Takaicin Uba zai iya kai ruhinta zuwa kushewa, yanzu daya tilasta mata kawo mijin aure idan zuciyarta ta buga fa? Kawai ki share mahaifinki ki ci-gaba da sabgar gabanki ya je ya ci kansa, Allah kaɗai ya san yadda zai da shi" Da hannu bibbiyu Majeederh ta toshe kunnuwanta, sosai maganganun da zuciyoyinta suke, suke mata amsa kuwwa a kunne! Jikinta har ɓari yake yana wata jijjiga. Kyakkyawar zuciyar ta ce "Amma ke baki da lissafi, da kina da shi ba kya ce haka ba, komai yana da sanadi Ubangiji ya ƙaddarawa Majeederh Jinkirin aure, amma Abbu shi ne sila, idan mutum ya kauce hanya addu'a ake masa idan da rabo ya dawo, abu ɗaya Majeederh za ta yi ta ci-gaba da addu'a, sadaƙa da yawaita azkar, kuma shi Imran ƙilan ƙaddararta da tashi daban shi ya sa a lissafin ƙaddararta babu auren shi, abu guda ɗaya ne ke ɓata mini rai da Majeederh yadda take yin shiru shirun nan, yaran cikinta na rainata ta ci uban kowa ta tattaka kowa, ta kuma cigaba da kare mutumcin kanta..." Ceceku ce aka shiga yi tsakanin zuciyoyi biyun! Kowa yana son Majeederh ta ɗauki shawararsa, ta saka hannu ta rufe kunnenta tare da sakin wani irin gigitacciyar ƙara ta zume wajan a sume.... Misalin 12 na rana, ta shiga buɗe Idanunta wanda sukai mata nauyi, a hankali ta saka hannu ta dafe gefen kanta dage barazanar tarwatsewa. "Sannu Hawwa'u" Muryar Anty ta sauka a kunnuwanta. Ta ya motsa fuska a hankali ta miƙe zaune tana jingina da jikin frame ɗin gadon bedroom ɗinta, cikin son nuna ta ji sauƙi ta ce "Ina yini? Yanzu kika zo" "I haven't been here long" Anti ta bata amsa cikin ƙasa da murya sai kuma ta ce "Meke faruwa dake har haka?". Majeederh couldn't speak sai da Anti ta ce "Kina da ilimi, kuɗi, hankali, kyau, amma duk da haka da sauranki baki gama cika mace ba". Anti ta yi shiru can ta kuma cewa "I'm starting to get tired of seeing you in this situation,It is good that now you are married and you are in your husband's house, Majeederh duk wani ɗaukaka da da iliminki a banza yake, macen da bata san komai ba wacce take gidan mijinta sai anfi ganinta da girma da daraja, sai anfi martabata fiye da komai, Abbank Uncle Isma'il shi ne ya turo ni ya ce na faɗa miki ya gaji idan ya haɗu dake ba zaki ji da daɗi ba, You're a darling ke abar so, kina da kyau" Murmushi kawai Majeederh ta yi wanda ya fi kuka ciwo ta kalli Anti ta ce "Mene amfanin kyau? Wallahi ban taɓa fariya sbd ina da kyau ba, ina tausayawa duk wata mace mai kyau" "Kyau abin so ne Majeederh" Majeederh ta runtse Idanunta ta ce "Bai ƙare ni da komai ba, wallahi da na san inda ake sauya fata daga fara zuwa baƙa da tuni na yi, na gaji da duniyar nan Anti" Ta faɗa tana riƙe ƙirjinta hawaye ma ya gagara fito mata. Anti ta ce "Kin gaji da duniya ga shi duniya na son ki, Majeederh mazan aure kika rasa ne?" Kanta a ƙasa ta kasa cewa komai Mami dake zaune looking so worries ta ce "Ta yani tambayarta Maryama, ni dai ba ruwana dole na ja baya idan ina matsa Majeederh za ta yi zaton dan bani na haifeta bane wallahi,to me ma zan ce? Nan nan wata Neighbor ɗinmu ta zo ta mini ta tas kamar uwata, zagi kala-kala tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin tashin hankali irin na ranar ba" Ta yi jim! Sai kuma ta ce "To akan me" "Uhm, ta tsuniyar gizo ai bata shige na ƙogi, cewa ta yi wai bata yarda da Majeederh ba, gani take gantali kawai take a duniya shi ya sa bata damu da aure ba" Anti ta ce "To fa, ita wa kenan? Ina cewa akwai zabga zabgan ƴan mata a gidan wata ma ta yi Arba'in kamar uwata wallahi, amma ita ba taga na gabanta ba sai munafurci a ɗaure a ƙugu? Mutane basa kashe wutar dake ci a gabansu sai na wani? Baka da gadon mutum yana da gadon maganarka, to da izinin Ubangiji ba zamu ga wannan mummunan ranar ba, wani hanin ga Allah baiwa ne" Mami ta ce "A to, munafurci ne kawai irin na mutane wallahi Maryama, nan ta zo ta wata yaƙunanniyyar atamfarta duk gansa kuka, ai kana ganin wannan matar kaga zubin munafukai Inyami take kowa?" Anti dai bata ce komai ba. Ta juya kan Majeederh ta ce "Ki tausayawa kan ki, ki tausayawa mana dan Allah Majeederh, zaɓen miji yanzu ba naki bane, duk wanda ya fito da niyyar aurenki kawai ki amince masa As long as you trust his morals, his behavior, his mind and his religion" Kallon Anti kawai Majeederh take domin bai ɗaki shiyasa inda yake masa yayyu, wai ba