← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 93

Sashe 6

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tajju na gama karantawa ko gyara bedroom ɗin bai ba ya zari key ɗin mota tare ficewa daga cikin gidan, tana ina zai fara? Ina zai ga Malama Majeederh har ya bata wannan saƙon? A fili ya ce "Allah na tuba, ban san me ya mantar dani ba" haka yaci gaba da driving.
Tun safe Majeederh take tafiya fuska rufe babyn ya yi shiru a jikinta, kamar mahaukaciya haka ta zama bata gane komai bata bambance komai, kiran sallar Magriba ya yi daidai da tsayuwarta a gefen wani shago a lokacin kuma babyn ya kama kukan yunwa, ta samu waje ta zauna ta shiga kallon fuskar jaririn ko Allah zai sanya ta gane dawa yake kama, amma abin mamaki komai nata ne, kamarsa ɗaya sak da ita idanunsa ne kawai da bai fiya buɗewa ba yasa bata gama gane ƙwayar tawa ba, ganin kukansa zai sanya hankalin jama'a ya dawo kanta ya sa ta zura shi cikin hijabi bata san me zatai masa ya daina kuka ba can ta tuna abincinsa yana jikinta ta ɗaga rigar asibitin dake jikinta tare da sanya masa nono a baki, babu ruwa ko kaɗan zai azabar zafi, haka ya dinga jan fata jin baya shan komai ya cika ya dinga tsala ihu. Sai a lokacin ta fashe da kuka take rungume shi ta ce.
"Asstagafirullah Ya Allah, ba san komai, na yarda da ƙaddara, Allah ka kawo mini ɗauki albarkacin Annabin rahama" a hankali ta dinga tattaro yawun bakinta tana bawa jaririn yana sha, tun tana bashi har yawun ya ƙafe bai kuma daina kuka ba. Ta miƙe riƙe da shi tare da ƙara sawa wajan shagon tayi sallama can ƙasa kafin tayi magana ta ji saukar muryar Abbu a kunnenta ta juya da sauri ta kalli T.v dake shagon, fuskar mahaifinta tar a t.v yana yi wa ƴan jarida bayani ya ce.
"Me kuke son sani?" Ɗan jaridar ya ce "Shin da gaske ne ƴarka Malama Majeederh Abdul'aziz Khan kan ta haihu? bayan duniya ta san bata da aure? Ko dai tayi aure a ɓoye ne, ko kuma zargin da ake a kanta ya tabbata?" Abbu ya yi dariya sosai yana kallon Ɗan jaridan ya ce.
"Ina da Æ´a Majeederh, amma tawa yarinyar ta zama gawa tun tuni bata raye, ban kuma san yarinyar dake amfani da sunana da kuma sunan familyna ba, zan yi amfani da wannan damar wajan yi mata Allah ya isa har abada, zan kuma shaidawa duniya duk inda suka samu yarinyar nan mai amfani da sunana su jefe ta ko kuma suyi mata bulala akan laifin aikata zina, su kuma É—auki mataki akan amfani da rigar Muslunci tana aikata alfasha"
ÆŠan jaridar ya kalli Abbu sosai, da alama ya firgita da maganganun shi ya ce. "Kenan Malama Majeederh ba Æ´arka ba ce wacce muke tunani?"
Cikin tsawa Abbu ya ce
"Yara biyar ne kaf duniya, tawa Majeederh ta zama gawa tun da jimawa bana son wata tambaya bayan wannan" a firgice Majeederh ta dafe ƙirjinta da yake wani bugawa jajirin ya nemi suɓucewa ta shiga kokawa da numfashinta, wani abu mai nauyi ya tsaya mata a ƙirji Idanunta suka tsaya ƙam akan fuskar mahaifinta tunani take ko dai da gaske bashi ya haifeta ba? Mai shagon ya girgiza kai ya ce.
"Kai duniya, kai duniya wai yanzu aikata zina ya zama ruwan dare? Matan aure su aikata zina, ƴan mata su aikata zina, zawarawa su aikata zina, mijin aure ya nemi matar wani, matar aure ta nemi mijin wani? ga Fyaɗe daya ya waita, ga matsalar tsadar abin duniya, ga rashin nefa ga rashin ruwan sha, albashi wannan sai a shige wata ba a biya, wani lokacin ma a rage albashin, ga yawan aibata Musulunci yanzu Fisabilillahi a kaf garin nan waye bai san Malama Majeederh Abdul'aziz Khan babbar malamar musulunci ba ce? waye bai san irin tallafin da take bawa Muslunci ba, waye bai san wa'azin da ta kewa masu aikata alfasha ba, sai gashi ana zaton wuta maƙera sai gata a masaƙa, shi ya sa ake cewa kayi amfani da faɗar Malam kada kayi amfani da abin da yake aikatawa, wallahi ko ki aka bani dama sai na jefe wannan shaiɗaniyyar" Lawan ya girgiza kai ya ce "A'a Bala, amma dai Allah ya kyauta!" Bala ya ce "Amin, shi ya sa taƙi aure tana ta zuba alfasha, kasan daman duk wani mai aikata zina aure bai dame shi ba, kuma ko ya yi aure ba zai daina yin abinda ya saba ba"
Malama Majeederh bata tsaya neman ruwan ba, ta juya da sauri tare da barin wajan a lokacin ji take kamar ta shiga duniya, kamar ta zama ƙaruwar da suke danganta ta da ita, ji take kamar ta zama sanadin lalata sunan mahaifinta dana familyn da yake nesa ta da shi gudun kada ya ɓaci, zuciyarta ta ƙe ƙashe duk damuwarta ta tsaya, lokaci zuwa lokaci take jan numfashi ta sauke sbd abinda ya tsaya mata a saitin zuciya da maƙo shinta. Tayi tafiya mai nisa sosai kafin ta samu wani waje kusa da wata bola ta zauna ta rungume yaron wanda ya yi shiru, jikinsa ya ɗauki zafi. Ji take kamar ta rataye kanta, ga jinin haihuwa daya gaba ɓata mata jiki a haka barci ya ɗauketa.
Tsaye suke gabaÉ—aya a parlour Hajia ta girgiza kai ta ce "Me kayi haka Zaki? Me ka aikatawa kan ka haka Aliyu?"
Almustapha ya kalli news paper ɗin ya ƙara ware idanunsa akan photon Bar Aliyu Sufyan Alhassan da kuma photon Malama Majeederh Abdul'aziz Khan dake zaune fuskarta rufe da liƙab. Almustapha ya shiga karanta headline ɗin jaridar. "Bar Aliyu Sufyan Alhassan shi ne ya aikata zina da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, tare da saninta domin su wulaƙanta matar Aliyu wato Latifa Omar kasancewarta aminiyar Jeederh" ya karanta a fili cikin zafin nama da faɗa Almustapha ya ce "Wanne shirme da hauka ne haka Aliyu? Zina? Ɗan shege?" Aliyu ya kalli yayan nasa ya ce..
"Ba shege bane" "To uban mene? Aurenta kayi?" Aliyu ya ce "Ko É—aya, ina son ta am ready to marry her, É—a kuma ba shege ba ne" Almustapha ya É—auke Aliyu da mari ya ce
"Mahaukaci, to kayi gaggawar zuwa gidan jaridar nan ka ƙaryata rubutun su, ina da tabbacin kuma matarka Latifa Omar ce tayi wannan aikin ai a gidan jaridar take aiki"
"Tayi dubun su, ba zai sauya mini ra'ayi ba"
Cewar Aliyu. Almustapha ya ƙara ɗaga hannu zai mari Aliyu,cikin sauri Aliyu ya riƙe hannu ya ce
"Kasan Allah ka ƙara marina zan karya hannunka,ka bar ganin kai yaya na ne, idan kun shirya korata kamar yadda Mahaifin Majeederh ya koreta fine I'll leave the house" abu kamar wasa dambe ya sarƙe tsakanin wa da ƙani cikin ɓacin rai Hajia ta zabgawa Aliyu mari ta ƙara zabga masa mari ta ce "Ka nutsu Zaki, ka nutsu" Aliyu ya fashe da kuka ya rungume Mahaifiyarshi ya ce
"What should I do Hajia? Dame zan ji ne? Wallahi idan kuka matsa mini zan iya aikata komai, Hajia I love Majeederh don Allah ki nemo mini ita, hajia hajia....,"
Da Hajia da Almustapha su kayi kan Bar Aliyu Sufyan Alhassan wanda ya faɗi a ƙasa sumamme...

Government House
Labarai ake ta ko'ina gabaɗaya kuma akan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ne, Human rights sun shiga maganar, ƙungiyar mata ta shiga maganar, shugaban ƴan hisba. Ya sauke ɓoyayyiyan numfashin tare da juyawa kaɗan ya kalli tulin jaridun da aka wallafa, gefe guda kuma yana mamakin gidan Jaridar Hausa lastest News, domin sun fi ko wanne gidan jarida ɗaukan zafi da kuma aibata Malama Majeederh. Sama sama yake kallon photon ta, bai taɓa ganinta ba amma muryarta kullum tana yi masa amsa kuwwa a kunne. "Ham...mad" Hammad ya yi sauri ya rusuna ya ce
"Your excellency" "Waye me wannan Shirman?" Hammad ya ƙara yin ƙasa ya ce "Wata ƴar Jarida ce, Latifa Omar"
Abu-turab ya ce.
"A dakatar da gidan jaridar" with so much respect Hammad ya ce
"With pleasure Your excellency" ya jinjina kai kawai, Hammad ya juya cikin sauri. Kai tsaye akai sanarwar da yawun Gwamna tare da bada umarnin rufe gidan Jaridar. Abu-turab ya kasa komawa gida, tun safiyar yake jiran ya ji ance an samu Malama Majeederh Abdul'aziz Khan amma shiru har biyar na yamma ya yi. Tajju ne ke driving hannunsa riƙe da Envelope yana ta yawo amma bai samu Majeederh ba, gashi har an kwana wani daren na shirin yi kamar ance masa ya juya idanunsa ya sauka akanta tana nan zaune bakin bolar ta ƙanƙame jaririn kamar za a kwace mata shi, ta fita hayyacinta duk jini ya ɓata jikinta, cikin sauri Tajju ya gangara gefen titi tare da yin parking yana Hammadala a ransa ya fito,bai san mene a envelope ɗin ba amma yasan dole yana da alaƙa da wannan jaririn babu ko tabbata musamman yanzu daya tuna wata rana. Yazo daidai tsakiyar titin yana ƙoƙarin tsallakawa wata ƙatuwar tifa tayi awon gaba da shi....

#Bar Aliyu Sufyan Alhassan
#Dr Jamal
#Abu-turab

Na'ima Sulaiman Shu'aibu
08119237616
Not editing*🌈 MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta

*_Please kuyi following Acct ɗina a arewabooks🫰🏿_*
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

*AN SAMU MISTAKE, WANNAN SHI NE FULL PAGE NA 4 KUYI SHARING, A GOGE WANCAN🙏🏿*
Chapter 6 · 0% Book details